'Yan bindiga sun kai hari a Otal din Radisson Blu Hotel da ke Bamako, babban birnin kasar Mali.
Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa da alama an kai harin ne domin yin garkuwa da mutane.
An ji karar harbe-harben manyan bindigogi masu sarrafa kansu a cikin otal din.
Wakilin BBC ya ce 'yan kasashen waje da ke aiki a Mali ne suka fi zama a otal din, mai dakuna 190.
Wani rahoto ya ce maharan sun yi garkuwa da wasu mutane.
Jami'an tsaro sun yi wa otal din, wanda ke tsakiyar birnin, kawanya.
A watan Agusta, wadansu 'yan bindiga da ake zargi masu kaifin ra'ayin addini ne sun kashe mutane 13, cikinsu har da ma'aikatan majalisar dinkin duniya guda biyar, lokacin da suka kai hari wani Otal a garin Sevare.
Amurka ta gargadi 'yan kasarta
Ofishin jakadancin Amurka da ke Bamako ya gargadi Amurkawa da su ci gaba da zama a gidajensu, sannan su bibiyi abubuwan da ke faruwa a birnin.
Kazalika, Amurka ta bukaci 'yan kasarta da su tuntubi iyalansu da ke birnin domin sanin halin da suke ciki.
bbchausa
Title :
An Kai Hari A Bamako
Description : 'Yan bindiga sun kai hari a Otal din Radisson Blu Hotel da ke Bamako, babban birnin kasar Mali. Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillan...
Rating :
5