Masu bincike game da hare-haren ta’addanci da aka kai birnin Paris na Faransa, sun gano wata jigidar bama-bamai da ba a tarwatsa ba a kwandon shara a wata unguwa da ake kira Montrouge da ke wajen birnin.
Wannan na zuwa sama da kwanaki 10 bayan munanan hare haren da aka kai a birnin inda aka kashe mutane 130.
Masu binciken sun ce jigidar ta yi kama da ta maharani na Paris.
Hare haren Paris dai sun razana kasashen Turai, inda yanzu haka Belgium ta tsaurara matakan tsaro bayan samun labarin ana shirin kaddamar da hari a kasar irin na Paris.
Title :
An gano wata jigidar bama-bamai a Paris
Description : Masu bincike game da hare-haren ta’addanci da aka kai birnin Paris na Faransa, sun gano wata jigidar bama-bamai da ba a tarwatsa ba a kwando...
Rating :
5