Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dakatar da Jose Mourinho daga jagorantar Chelsea wasa daya, ta kuma ci shi tarar fam 40,000.
Hukumar ta ce Mourinho ya amince da tuhumar da aka yi masa tun farko ta rashin da'a da kuma yin munanan kalamai ga alkalin wasa Jon Moss.
FA ta tuhumi Mourinho da nuna halin rashin da'a a wasan da West Ham ta ci Chelsea 2-1 a gasar Premier wanda aka kore shi daga karawar a ranar 24 ga watan Oktoba.
Da wannan hukuncin Mourinho zai biya tara kudi fam 40,000, sannan ba zai jagoranci kungiyar ba a fafatawar da za ta yi da Stoke City a gasar Premier wasan mako na 12.
Sai dai kuma Mourinho ya bayyana hukuncin da aka yanke masa da abin kunya ya kuma daukaka kara.
Title :
An dakatar da Mourinho an kuma ci shi tara
Description : Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dakatar da Jose Mourinho daga jagorantar Chelsea wasa daya, ta kuma ci shi tarar fam 40,000. Hukumar ta c...
Rating :
5