Ya kyalkyale da dariya yace “ kema fa kina da abin dariya gaki dai kamar ba zaki yi ba “, ya zauna a kujerar dake nesa kadan dani ya dora da cewa “nayi mamaki ma2ka dana duba kaf makarantar nan ban hango tauraruwar dake haska wannan makarantar ba ke kinga yadda duk makarantar tayi duhu kuwa??
akwai bukatar ki fita ko don ki haskata“.
Na dauke kaina daga lttfan da nake dubawa nace “kai!! ina yin abuna a nitse kazo zaka rikitani wai kai wane irin mtm ne??
Kai baka rabo da NACI??
Baki, musulmi kuma bahaushe. Ya bani amsa irin wannan a karo na biyu sannan ya dora da cewa “ina da naci musamman idan ina so na isar da wani sako aka kasa fahimtata.
Na tabe baki nace “sako?? wanne irin sako kake so ka isar??“
Ya danyi shiru jimawa kadan ya mike alamar wasa ta fita daga fuskarsa yanayi na fadar magana da gaske ya shigeta ya taka a hankali izuwa gaba yace “ Akwai wata kalma da ake kira SO wacce a baya ban santa ba, ban fahimceta ba hasalima ban yarda da ita ba.
Abinda na dauka shine ba zata iya tasiri akaina ba sai gashi lkc guda na fahimci ashe SO gsky ne domin tamkar kwayar virus yake wajen saurin fadada, yana da ma2kar gudu a cikin jini hakan kesawa yayi saurin bin sassan jiki kwatankwacin yadda yabi jinina ya hana min duk wani sukuni....“
Nayi saurin jan wani dan karamin tsaki nace “ To ni ina ruwana?? “
Ya juyo izuwa gareni yace “abinda kika kasa fahimta shine na kamu da sonki duk da cewa ban sanki ba bansan daga inda kike ba hasalima ko sunanki ban sani ba, wannan na daga cikin aikin SO ba ruwansa da kyau, muni, asali ko kuma banbancin akida.
INA SONKI!!! kalmar da bana shayin fadarta a ko‘ina domin na tbbtr shine abinda ke ckn zuciyata.
Nayi saurin dago kaina idanuwana suka zaro tamkar zasu fado, Kana sona??
Tambayar dana fara yi masa kenan na dora da cewa “ Ban taba tsammanin jin wannan kalmar daga bakinka domin wadanda suka fika komai ma ba wanda ya taba 2nkarata da wannan maganar...“
hakan na nuna miki irin son da nake miki kuma yana tbbtr miki ni masoyi ne gaske bana yaudara ba.
ya fada kyakykyawar fuskarsa na kaina.
Na ajiye littafan dake hannuna na mike da dubeshi tare bata hade rai wanda ban taba yin irinsa ba nace “ kaga leader kake kowa?? wasanka yana yin yawa yakamata kasani akwai wasan da kakanni kawai ake yiwa irinsa....
Ya katseni da cewa “Wlh ba wasa nake ba idanuna kadai sun isa su tbbtr miki da haka, amsa kawai nake jira daga kyakykyawan bakinki wanda ta yiwu shine danbar fara sabuwar rayuwata“.
Amsa kake jira?? na tambaya ina kllnsa nace “ kana tsammanin amsata zata zo a yadda kake so ne?? to kayi kuskure, babu wata maganar soyayya tsakanina dakai kayi gaggawar janye wannan maganar ko don tsira da mu2ncinka a idona.
ya gyara zamansa izuwa kallo na sosai yace “ Bazan taba janye kudirina ba sai dai idan har zaki fada min shin wani mummunan hali gareni da za‘a ki sona sbd dashi??
Na girgiza kai nace “ba wani mummunan hali amma koba komai banbancin class... kuma ma kawai bana ra‘ayin soyayya yanzu.“
amma.............
Nayi saurin katse maganar tashi da tsawa nace “Bana sonka!! nace bana yi!! karka kara zuwar min da zan2ka irin wadannan sbd nafi karfin jinsu bare na yarda dasu.“
Fuskarsa ta sauya ma2ka ckn yanayin da ban taba zaton akwai ranar dazai zama haka ba a yadda nake ganinshi, yace “ Naji na amince kuma na hakura amma zanso kiyi abinda idan na tafi bazan zargeki ba sai dai na zargi kaina.“
Kamar yaya?? na tambaya ina kllnshi.
Yace “ kiyi min duk irin jarabawar da kika gadama a duniyar nan da kowacce nau‘in tambaya kîka gadama idan har na fadi to shikenan na hakura kuma bazan taba zarginki ba sai dai na zargi kaina.“
Idan kuma ka amsa fa??
Nayi saurin tambayarsa.
Yace “sai ki dauki kaddara ki yarda muyi soyayya.
Na bishi da kallo na koma inda nake a baya na zauna nace “ ba tambaya daya zanyi maka ba sai dai guda uku kuma cikin kwanaki uku a jere idan ka fadi a daya ko kayi tsallaken rana daya shikenan dole ka rabu dani.“
Na amince.
Ya fada ba tare da jinkiri ba....
Na bishi da kallo ckn mamakin yadda bai tsorata da komai ba saima wani karfin gwiwa da yake da ita, ya tsareni da ido jiran irin tambayar da zanyi masa kawai yake.
Allah ya sani yana ma2kar birgeni sbd ya hadu sai dai kawai ji da kai da takamata ta hanani na amince da ainihin abinda ke zuciyata, wacce tambaya ma yakamata nayi masa?????
Tambayar dake ta yawo a zuciyata kenan ckn salo na nazari.
Zuwa can na dago kai nace “tambayar yau me sauki ce ina so ka canki sunana wanda mahaifina ya rada min, sau daya kawai zaka fada idan ka fada ba dai-dai ba ka fadi.“
Yabi ni da kallo tare da gyara zama yace “ Sunanki?? Haba ranki ya dade ta ina kika taba ganin an fadi sunan mtm daga ganinsa??? SUNAYE na daga abubuwan da suka fi komai yawa a duniya don haka amsa wannan tambayar is impossible a ko‘ina, a zatona zakiyi min tambayane wadda kwakwalwa zatai aiki wajen gano amsa amma ba canke-canke ba.
Na danyi gun2n murmushi nace “daga farawa harka fara karaya?? wannan itace mafi sauki daga wadanda nayi maka tanadi, koka manta kai kace duk irin tambayar da nake so??“.
ya kauda kai daga kallo na a hankali ya dan jima baice komai ba zuwa can yace “bari kwakwalwa tayi aiki“.
Ya mike daga inda yake zaune ya fara takawa a hankali yana kaiwa da komowa hade da kallona a wasu lokutan, yanayin na nuni da zuzzurfan nazarin daya shiga, ni kuwa har wani murmushi nake yi idan na kalli halwar daya shiga, yau dai zan rabu da kaya.
Abinda naketa darsawa kenan domin ina da yakini 100% bazai iya amsawa ba.
y‘an min2na kalilan ya kwashe ya juyo gareni yace “A mafi yawan lkt suna nayin tasiri a kamar mu2m da yanayinsa, idan har an sami haka a kanki to ina da tbbcn sunanki ba me guda daya bane irin sunan nan me guda biyu ko ince tagwaye kamar “fatima-bintu, zainab-abu, halimatus-sadiya! sai dai duk bakiyi kama da wadannan sunayen ba.
Ya dan taka da kafarsa dake sanye da wani kyakykyawan farin takalmi ya juyo gareni ya kalleni na dan lkc yace
“AISHA HUMAIRA!!!!!!!“
Ya fada tare da sake mai-maitawa da fadin “yes nafi yarda sunanki Aisha humaira....“ ya zarce da kllna don jin abinda zan fada.
Ni kuwa 2ni idanuna sun kwalalo waje sbd AL‘JABI, ya akai kasan sunana??
tambayar dana jefa masa kenan, fuskarsa tadan fara saki yace “ kina nufin Na fada dai-dai kenan??“
Bansan sanda na gyada kai alamar eh ba, ya kawo gwauron numfashi hade da murmushi ya koma ya zauna tare da cewa “Step one done saura na gaba, ita dama SOYAYYA hadin Allah ce idan yaso koke baki da ikon hanawa kuma ina da yakini da karfin gwiwar yin nasara sbd ina ji a jikina akwai alkhairi a tarayyarmu.“
Ya mike tare da ja da baya fuskarsa cike da yalwataccen murmushi yace “Nima sunan nawa me tagwayene UMAR FARUK!! sai an jima farar tauraruwa me farin haske.
Ya juya ya fice.
Na daki tebirin dake gabana kamar na fashe da kuka, gsky ya birgeni amma naji haushin yadda yayi kaca-kaca da tambayata mafi tsauri irin wannan domin ba canka kawai yayi ba hankalinsa ne yayi aiki a wurin.
wai wannan anya kuwa mu2m ne???
dakyar na karasa abinda nazo yi na tafi class.
°ranar sai ya zamana duk na zama wata iri 2nanin irin zazzafar tambayar da zanyiwa faruk kawai nake wacce zata gagareshi amsawa, koda ace zan yarda da soyayyar faruk amma bana so ya kureni, sai dai duk tambayar data fado min sai naga kamar kwaf daya zaiyi mata°
Washe gari 2nda na shiga makarantar bamu hadu dashi ba har aka tashi na fito daga class na hangi driver na sai dai dole na jira mufida wacce bata fito ba har yanzu, na karasa jikin motar na bude bayanta na zauna ba tare dana rufe kofar ba saima kafafuna dana ziro waje, salon sallamar dashi kadai keyi tasa nasan ya iso, na dauke kai kawai.
Ya dubeni sosai yace “sorry for the late, Allah ya taimakeni baki tafi ba da shikenan na fado ina fatan dai baki manta tambayar da kika tanado min ba??
Na kalleshi nace “bana so saina kayar dakai ta karfin tsiya ka hakura kawai zaifi maka sauki daga jin tambayar da miliyoyin mutane suka gaza amsata masu ji da basirar, hikima da hazakar da tafi taka..Mai-makon kalaman yaudarar da nake amfani dasu suyi tasiri akansa saima ya kyalkyale da dariya ya dan taka kadan izuwa jikin kofar motar dana bude ya dafashi da daddadar muryarsa me ratsa zuciya yace “Humaira kenan kada kiyi tsammanin kautar da 2nanina akan abinda nake so kuma nake da yakinin zan sameshi, na kasance ina da baiwar yin abubuwan da miliyoyin mutane suka kasa, wannan kamar a jinina ne don haka karki damu kiyi min kawai ni abinda na dauka shine abinnan da muke yi kamar istahara ne a gareni indai tarayyarmu dake alherice to zan amsa tambayoyinki koda sun kai 100, idan kuma babu alheri a ckn soyayyarmu to bazan taba iyawa ba.“
Nabishi da kallo kawai nace:
*“ Akwai wata halitta a doron kasa wacce yanayinta ke caccanjawa.
Idan tana karama tana tafiyane da kafa hudu, idan ta girma kuma sai ta koma tafiya da kafa biyu, yayin da kuma ta tsufa sai ta koma tafiya da kafa uku, wacce halitta ce wannan???*
Yayi saurin sakin kofar daya rike yabini da wani irin kallon da ni kaina sai dana tausaya masa, yaja da baya kadan lkc guda ya fara kaiwa da kawowa a wajen hankalinsa in yayi dubu ya tashi, na saki yalwataccen murmushi nace “kaga faruk ba iya amsawa zakai ba ka.......“
Ya daga min hannu yace “ karki katseni “.
Na daga ido tare da tabe baki a raina nace ‘ayi dai mugani‘.“
Ya dan dakata kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya shafi gashin kansa yace “DANKARI!!“
Na kyalkyale da dariya kawai na dauke kai na fara latsa wayar dake hannuna sbd a yadda nake ji a jikina na gama dashi, sai dai ta ciki na ciki don kuwa kirjina dif-dif kawai yake don bansan yadda zamu karke dashi ba. tsawon lkc muka shafe amma babu alamun ya karaya da amsa tambayar saima dada kaimi da yake wajen 2nani da nazari, jim kadan yadan yi nuni da hannun tare da gyada kai ya saki murmushi kyansa ya kara fitowa, ya tako a hankali izuwa inda yake tsaye 2n dazu yace:
“ idan har 2nanina da nazarina sun bani dai-dai-dai to ina da tbbcin ba kowacce halitta bace wannan face MUTUM wato bil‘adama.dalili kuwa mu2m sanda yana yaro da kafa hudu yake tafiya shine RARRAFE, gwiwoyi biyu hannaye biyu.
Yayin kuma daya girma ya iya tafiya sai ya koma tafiya da kafa biyu kamar yadda ni dake muke tafiya yanzu.
Lokacin kuma da mutum ya tsufa sai ya zamana kafa biyu ba zata iya daukarsa ba sai ya kara da sanda a matsayin kafa ta uku.“ Bansan sanda wani irin murmushi ya kwace min ba wanda shine ya nuna ainihin abinda ke zuciyata nake dannewa, yadda yake zano abubuwan tamkar me karantawa a littafi ya birgeni ma2ka.
Shima yayi murmushi tare da cewa “ zan iya cewa wannan murmushin tayani murnar cin nasara a karo na biyu ne??“
Na gyada kai tare da cewa “kwarai kuwa da alama gaf kake da cina da yaki faruk akan haka dole na jinjina maka domin kaine mu2m na farko daka fara neman ka kureni, murmushin da kaga nayi na tayaka murna ne da kuma tausaya maka domin ka kai matakin da dole kayo kasa domin gobe koda kai aljanine baka isa ka amsa tambayar da zanyi maka ba.“
Ya dago kansa ya fashe da dariya yace “kina birgeni sarauniya sbd komai naki me tsari ne kuma da karfin gwiwa hakan na daga ckn abinda yasa muka dace da juna, idan wai kina tsorata nine to sai ince miki kima hutar da kanki don kuwa ma2kar ina tuna cewa soyayyarki nake nema to zanyi abinda aljani ma bazai iya yi ba.
Na gyara zamana dai-dai sanda na hangi mufida tare da kokarin shigo da kafata ckn motar nace “can dai da yawarka“.
Yayi dariya ya gyara doguwar jakar dake rataye a kafadarsa wadda ta hadu da dressing din jikinsa tayi masa kyau yaja da baya a hankali yace “Ki shiryawa fara sabuwar soyayya a gobe......“ Nayi saurin katseshi da cewa “ko kuma ka shiryawa bakin cikin faduwarka a gobe ba“. Ya dan dakata yace “ to shikenan zan iya cewa duk mu jira FINAL din don ganin yadda zata kaya, ya dora hannunsa a gefen goshinsa ckn alamu na sarawa tamkar soja yace “sai gobe farin ganina“...
Hmmm mumadai allah yakaimu GOBEn muji wannan wata tanbayace haka..zata hada ko zata raba..?!
GOOD MORNING..