Bayan kwanaki uku da dawowata ina kwance bisa doguwar kujera hannuna na rike da wani novel daya daga cikin abokan hirata a london me suna HAPPINESS DAY na prof. christiana wolein dan kasar holland, kyakykyawar fuskata nakan littafin wanda fararen idanuna ke kallo, hankalina, tunanina da duk wani nazarina ya tafi ga karanta daddadan lbrn da nake yi wanda nake matukar son karasashi ko don naji yadda karashen lbrn zai kasance.
Magribar da nake ganin ta doso yasa na kara kaimi, Momi ta fito daga sashinta rike da wani dan madai-daicin kaskon turare wanda wani daddadan kamshi ke tashi ta hanyar farin hayakin dake fita daga kaskon, ta fara zagaye faffadan falon domin kanshin ya isa ko‘ina kafin ta dawo ta ajiye shi a tsakiyar falon.
A dai-dai lkcnne dady na ya dawo, cikin fara‘a yayi sallama kasancewar ya ganni a falon, ya karasa ya aje jakarsa tare da zama. Kamar hadin baki nida momi muka amsa sallamar, na dago daga kwanciyar da nayi tare da aje novel din a gefena nace “Wellcome back my dady“.
Yauwa yar lele na da fatan dai komai normal ko? na gyada kai kawai, momi dake gefe ta bimu da kallo tare da jinjina kai tace “uhm.. gsky ina ganin kabilanci a gidannan, wato Alhaji yarka kawai ka sani ni ba mu2m bace??“ Daddy ya kyalkyale da dariya yace “kinji ki hajiya da wani zance gani kikai na tashi daga nan bance miki komai ba??“ Da sauri tace “zaka iya don ba karamin aikinka bane kace bama ka ganni ba 2nda ka shigo sai da nayi magana.“ Dady ya sake yin dariya yace “ A haba sai kace wani makaho? kawai dai........“ Y‘arka ce a ranka!! momi ta karasa masa zancen.
ya gyada kai yace “anji muje a hakan“. Momi tace “gashi kuma duk daran dadewa sai ka shigo falon nan ka tarar batanan koka manta macece dole ka aurar da ita??“ Dady yayi murmushi yace “kinga hajiya duk takaicinki kyayi ki gama ai ba akuya bace ita bare kice zan kaita kasuwa na siyar mun rabu kenan har abada.“
Duk muka fashe da dariya, dady ya kwantar da kansa jikin kujerar yace “ yauwa ni na tuna ma, humaira!!
Na dago kaina a nitse domin nasan indai dady ya kira sunana kai tsaye to maganar da yake son yimin me muhimmanci ce.
Yace “kasancewar kinyi kara2 me tsada a wuri me tsada kuma akan abu me tsadan gaske izuwa yanzu na sami request daga wurare daban-daban akan anaso ayi aiki dake, daga ciki akwai central ban.k da me gwamnan bankin da kansa ya rubuto min takarda akan cewa suna bukatar karin kwararru da suke da sani akan tattalin arziki, akwai FIRST BANK, GTI BANK, DIAMOND BANK da sauransu.
Ma‘aikatar kudi ta tarayya ma na bukatar kiyi aiki dasu, sannan jami‘o‘i kamar B.U.K, A.B.U da sauransu na bukatar kiyi musu aiki a matsayin lecturer, ke harda wasu hukumomi daga kasashen waje sai kin zaba kin darje.
A maimakon nayi farin ciki sai na hade rai, dady ya dubeni tare da gyara zama yace “Ah ya naga kin bata rai?? lafiya??“
Na dan kumburo baki nace “dady nifa bazanyi wani aiki a duk wuraren nan ba.“
dady yace “sai a ina?? ko a bankin duniya kike so kiyi aiki??“
Na girgiza kai nace “ A‘A ni bazanyi a ko‘ina ba.“
Kafin yace wani abu momi tace “ba zakiyi ba kina nufin duk kara2n da kikai ya tashi a banza kenan??“
Dady ya dubeta yace “haba hajiya kibita a hankali mana, ya juyo gareni yace “Yar lelena me yasa bakison kiyi aiki??“
Nace dady nifa banyi kara2 don na wahalar da kaina ba, nawa ne duka albashin da za‘a biyani? duka fa bai kai kudin da gyaran gashi na keci ba.
Yayan talakawa da matsiyata sune keyin kara2 don su sami aiki amma ba irina ba.“
Daddy ya kyalkyale da dariya kamar zai tuntsiro daga kan kujerar yace “gskyrki fa y‘ata.“
Momi tace “ Au wai kaima ka biye mata a hakan??“
Daddy yace “To karya tayi??, ya juyo gareni yace “ yanzu ke me kike so ayi??“.
Na tabe baki kamar ba zance komabi ba daga bisani nace “ daddy nifa a duniya ba abinda ban iya ba irin kwamfuta don haka ina son na samu certificate akanta.
Cikin sauri daddy yace “Tooo!!! a germany ko japan ko america zabi daya......
Na tabe baki nace “NO daddy duk basai ankai ga haka ba, anan kano nake so nayi.“
Daddy yabini da kallo yace “kina nufin a makarantar matsiyata??“ Dariya ta kwace min na girgiza kai nace “ a‘a akwai wata reshen AL-KHRAMY ta kasar saudiya da suka bude anan kano next week za‘a fara lecture, MUFIDA ma can zata fara zuwa kaga na sami abokiyar tafiya.“
Daddy ya gyara zamansa yace “kwarai naji lbrnta, to karki damu my daughter a ckn satin nan za‘a shirya miki komai next week dake za‘a budeta.“ Nayi murmushi nace “Thank you my dad“.
Daddy ya mike “bari in karasa ciki, ya juyo ga momi yace “a ina kika saka min jakar nan ta jiya??“ Har yanzu takaicine akan fuskarta tace “ tana nan cikin lokar dakinka“. daddy ya sabi jakarsa ya wuce. Ni kuwa wani farin ciki ya lullubeni, gsky daddy na sona ni kaina nasan haka.
Hararar da momi keyi min ce tasa ban takalo wata hira da ita ba na jawo novel dina tare da kwanciya bisa luntsimemiyar kujerar da nake kai na cgb da kara2n da nakeyi a baya.
******** ******* ******* ********
Sati daya dai-dai da faruwar haka na fara zuwa lecture a katafariyar makarantar AL-KHRAMY computer training school, 2n daga sanda na hangi makarantar a shigata ta farko naji a raina tayi min sbd tsarinta. fasalin gininta kawai abin kallo ne banda kuma zubin cikinta.
Tana da ma2kar fadi da girma da kuma wadatar dakunan kara2, akwai bangaren da aka ware musamman don hutawa a lkcn da ba‘a lacca wanda ya kunshi kujeru a jere daf da wasu kyawawan bishiyu da kuma filawowi dalilin da yasa iskar dake kadawa a wajen ta zama me kamshi, wajen dai ya dace da hutawa ga wanda ya debo gajiyar kara2.
Gefe guda akwai daki na musamman da aka ware aka cikashi da littattafai kala-kala da suka shafi darasin computer da mutum zai iya zuwa ya bincika wanda yake so, nesa kadan kuma akwai wurin cin abinci da aka ware musamman ga masu bukata.
Da yake makarantar mallakar larabawa ce an ware bangaren maza daban na mata daban.
Ga yadda ake kaffa da dalibai ake maidasu y‘an gata.
kamar yadda aka saba ranar juma‘a 12:00pm mun tashi zaune nake bisa wani dan dandamali ina jiran mufida ta fito mu tafi kaina na kasa na kurawa laptop din dake bisa cinyoyina ido ina tayi, sallamar da naji anyi ce tasani dakatawa kamar na dago kai na dubi wanda yayi sallamar sbd muryar tasa ta ratsani sosai amma sai girman kan ya motsa na cgb da abinda nakeyi ko sallamar ban amsa ba.
Kyakykyawan saurayin bai gajiya ba yace “ pls na gaji da tsayuwa in zauna??“
Na cilla idona tare dago fuskata nace “ka zauna mana idan ka gadama“.
Mai makon ya bata rai sai yayi murmushi yace “godiya nake.“
Ya zauna bisa dandamalin nesa kadan dani, kaina na kasa amma zuciyata na sake-sake, ji nake kamar na dago kalli mu2min daya fara birgeni karo na farko a rayuwata.
Jim kadan mufida ta fito ai kuwa tana kyalla ido taga wannan saurayin dake kusa dani sai ta bude baki tare da fadin “ Ah leader manyan gari kaine anan haka??“
Yayi murmushin daya kara masa kyau yace “nine wlh kinga su nazir nake jira basu fito ba dama tare kuke da wannan??“
yayi nuni dani.
Eh tare muke da ita wlh ni take jira......
Na rufe laptop dina tare da diban littattafaina dake ajiye a gefena na doka tsaki na wuce nabarsu anan.“
mufida tabini da kallo kawai ta juya tare da yin murmushi tace “sai gobe ko??“
Ya gyada kai kawai dai-dai lokacinne abokansa su uku suka karaso wanda ya riga kowa karasowar yace “kai wai ya akai harka 2nkari wccn yarinyar ta barka ka zauna kusa da ita??“
Ya bishi da kallo yace “kasanta ne??“
Kwarai kuwa shugaban y‘an girman kai, takama da gadara ta duniya kenan.“
duk sukai dariya, saurayin ya shafi gashin kansa yace “kai! nazir yarinyar fa ba karya wlh ta hadu“, wanda aka kira da nazir din yace “ ana fada maka matsalarta kana cewa ta hadu??“
ya harareshi yace “ mace idan batai takama da gadara ba waye zaiyi?? girman kan ne kawai matsala.... ya sake bin inda muka bari a mota da kallo.“
Ni kuwa 2nda muka tafi mufida nata bani lbrn saurayin wai mu2min kirki ne kaza-kaza nidai ban kulata ba, don kasa gane me take nufi da hakan....
Ammafah....koda baxance komaiba..senaga iya gudun grman kannata....
Yanxu ne aslin komai ze fara..sekucigaba dabina..
Ammafa bada guduba..
#ILAL LIQA'A..