MUM ta dade tana kallona cikin takaici jim kadan tace " Me tayi miki kika mareta??"
Na koma kan kujera na zauna nace " zuwa... tayi ta giftani ina kallo ta kare min ban gani ba kuma tambayarta tayi min shiru."
ta kada kai tace " lallai humaira rashin mutuncin naki yakai, kawai daga na kirata ta gifta ta gabanki shine abin duka??"
Na zunburo baki nace mum " kare min fa tayi kuma......."
Ta katse ni da cewa " ke dalla can rufa mana baki kice kawai wulakancinki ya motsa to kin daketa kinji dadi, idan kinfi karfinta ai akwai Allah."
Ta nufi inda hanne ke zaune har yanzu bata tashi ba sai kuka da take yi.
Na dan kara bata rai tare da gyara zama nace " ni mum wlh bakya yimin adalci a komai ba zaki taba goyon bayana ba kullum nice me laifi a wurinki akan wadannan banzayen."
Nakai karshen maganar da kauda kai.
Mum tace " anki a goya miki bayan wace gsky gareki?? Ke ko kunya baki ji ba don Allah?? ki rasa wacce zaki zage kwanjinki akanta sai yar aikin gdnku wadanda yakamata ace kin jasu a jikinki ki nuna musu kauna."
Na kalli hanne na zabga mata harara nace " wadannan shashashan matsiyatan zanja a jikina?? Allah ya kiyaye.
Mum tace " to tunda ba zaki kyalesu susha iska ba ba ruwanki dasu basu shiga rayuwarki ba kada ki kara shiga tasu idan kuma kika ku wlh zan basu dama idan kika dakesu su rama suyi miki dan banzan duka ai ba karfinsu kika fi ba. Taja hannunta suka wuce, nabi mum da kallon mamakin jin abinda ita kanta tasan bazai yiwu ba, nace " Su dakeni fa kika ce?? "
Ta juyo da sauri tace " Eh don ubanki ".
Nabita da kallo ganin abin ya dau zafi da yawa ta juya suka bar falon da nake a zaune.
Na gyara zama na hade rai nayi kicin-kicin kamar na fashe da kuka, wai ni ake zagi akan wannan banzar yar aikin? lallai zamanta yazo karshe a gidan nan bari dady ya dawo.
BAYAN AWA DAYA naji motsin dawowar dadyna na kakalo sabon fushi da takaici, dady yana shigowa yayi ido hudu dani cikin fushi, yayi saurin ajiye jakarsa tare da tunkaro inda nake zaune " my daughter ( daya daga cikin sunayen da yake kirana dasu ) menene ya faru haka? waye ya taba min ke?"
Nayi shiru na kara hade rai kawai na juyar da kaina.
Dady ya zauna gaf dani cikin kasa-kasa da murya yace " fada min mana waye ya taba ki? uhummm?"
Cikin shagwaba na mirgina kai nace " ba mum bace......."
Me kuma tayi miki??
Ya tambaya da sauri.
nace " wai..... zata sa yan aiki su rinka dukana "
dady har wani dan babban motsi yayi tare da mai-maita abinda na fada " su dakeki??".
na gyada kai.
Ya juya da sauri ya fara kwallawa mum kira.
Hajiya!!!!! Hajiya!!!!!
Da saurinta ta fito izuwa falon da faddady yace " Me yasa kika batawa humaira rai, wai ke hajiya me yasa kike haka ne don Allah.... to to yanzu me kike nufi yar aiki tafi yar da kika haifa da cikinki kenan??"
Mum ta tabe baki tace " au wai da akan wannan ne kake kwala min kira haka sai kace wani tashin hankali??"
Au kina nufin shi wannan ba komai bane kenan?? kinga hajiya ran kowa zai baci a gidan nan fa.
Mum tace " rainin nata ne yayi yawa nace zansa a dai daita mata zama.
Na tsandara ihu nace kaji ko dady??
Dady ya kara rudewa ya fara zabga bala'i ta inda ya shiga batanan yake shiga ba.
Zuwa can nace " dady kawai a kori yan aikin nan dukansu ".
dady ya juyo yace " kwantar da hankalinki, abinda za'ai kenan suna ina ne??"
Mum tace " Wai suwa za'a kora?? bazai yiwu ba sbd duk cikinku ba wadda kuka dauka kuma baku kuke biyansu ba nice don haka babu me korar minsu ina jin dadin aiki dasu......
Munji tafi kici gaba da harkokinki kada ranmu ya baci duka, Allah ya baka hakuri.
Ta juya ta nufi sashinta, dady ya juyo gareni ya fara rarrashina ni kuwa sai wani kara hade rai nake.
Kinga manta dasu kinji humaira na, ba wanda ya isa ya taba ki duk wanda ya kara bata miki rai wlh tamuce ni dashi.
Kada ki manta fa gobe iwar haka kina kasar birtaniya kin bar musu kucakar kasar tasu zaki fara rayuwa cikin turawa ba wanda zai takura miki inda iskar da zaki shaka ma ba irin wannan bace.
Jin hakan da nayi yasa nadan saki raina kadan, yace " to danyi murmushi mana "
Na saki rai sosai yace " Yauwa ko ke fa! gobe kiyi kokari ki tashi da wuri sbd jirginki na safe ne an gama duk wasu shirye-shirye kina zuwa direct zaku daga shuuuuu!!! sai london."
yakai maganar da murmushi.
Na dan tabe baki cikin shagwaba nace " dady nifa dakai zamu tafi idan muka je sai ka dawo."
Ya dubeni yace " to ke banda abinki ina naga lokacin binki har london kuma na dawo? kedai karki damu jirgin na musamman ne zaki samu duk abinda kike bukata kuma za'a kula daku sosai musamman ma ke yar lele.
Nayi murmushi kawai.
Daddy ya mike ya dau jakarsa bari na shiga ciki ko?
"To dady" Na fada idona na kasa ya wuce.
Na daga kaina na dubi katafaren agogon dake manne a jikin bango karfe 6:15pm sallar magaribar ma ai da saura na mayar da kaina ga t.v din naci gaba da kallo.
$$$$$$$$$$$$
in Alhaji lfy irin wanWashe gari misalin karfe 8:00am na safe zaune muke mu uku, mum da dady na zaune a kujeru daf da juna yayinda nake zaune a kujerar dake fuskantarsu.
faffadan tebirine a gabanmu kayan abinci kala-kala jere bisa kansa wadanda suka dace da karin safe, babu wanda ke magana a cikinmu.
Humaira!!!!!!!!!!!!!
dady ya kira sunana, na dago a hankali na dubeshi.
yace " misalin 11:30 na safen nan zaku tashi, abinda nake so dake shine kibi a hankali kuma ki kula sosai sbd kasar da zaki je ba taki bace ba wadda kike ciki bace kuma ba wadda kika saba da ita bace, kiyi abinda yakai ki kawai shine karatu ki samo abinda zanyi alfahari dashi sbd ina da comfidence 100% akanki kuma ba zaki bani ba.
Insha-Allahu dady. Na fada tare da mayar da kaina ga kofin tea dake hannuna.
Daddy ya mike yace " bari inje na shirya na fita ina da meeting karfe tara hajiya ina takardun nan dana baki ajiyansu jiya??
Ta dago kai a karon farko tace " Suna nan cikin lokar sama." Ok " ya fada tare da dubana yace " yar lele na Allah ya kiyaye hanya, da zarar kun sauka zanyo miki waya."
To dady na fada ya juya nudi dakinsa.
Na mike na koma kan kujerar dake gaf da mum nace " Momina banji kince komai ba."
To me zance???
Ta fada kanta na duban abinda take ci.
Nace yakamata kice wani abu saboda kinga tafiya zanyi ta shekaru da yawa kodai bakin cikin rabuwa dani kike yi da yawa haka har ya hana ki magana??"
A'A ta fada tare da cewa " nifa haushinki kawai nake ji "
Na bita da kallo lokaci guda nayi yar gajeriyar dariya nace " da gaske??"
ta gyada kai kawai.
Na kwantar da kaina a jikinta nace " sorry my mum ai nasan da wasa kike ba zaki taba jin haushi na ba, uhmm! mum pls sarkar nan don Allah ki bani zanyi amfani da ita acan.
Ta girgiza kai tace " kefa kika nuna halin ko in kula da ita sai yanzu zaki ce kina so??"
Mum dama can ina sonta wlh zan kula da ita, Zaki bani??
nakai karshen maganar da kwantar da murya.
Mum ta dubeni kadan ta kauda kai tace " Zan baki ".
Na saki fuska hade da alamar jinjina nace " Thank you MUM bari naje na fara shiri. "
Na nufi dakina.
Misalin karfe goma 10:00am mufida tazo kawowa momi sako ta iske ina gaf da gama shirina ta tayani muka karasa na tilasta mata ta tsaya don yimin rakiya izuwa airport.
MUFIDA y'a ce a wurin haj. jameela kawar mum kuma aminiyarta, mufida ce kadai zan iya cewa kawata a duniya don da ita kawai na yarda muyi kawance sbd ta wasu bangarorin halinmu yazo daya duk da muna da banbanci da ita sosai a wasu bangarorin.
Misalin karfe 10:15am Nayi sallama da momi da sauran wadanda zan iya sallama dasu sauran yan aikin gidanmu kuwa da rashin mutunci muka rabu don ban hakura ba sai da nayi final.
A jibgegiyar mota kirar PRADO muka fito, mufida na gefena sai kuma mutum biyu har direba dake gaba.
Mukanyi hira jefi-jefi da mufida, kaina sai wani kumbura yake waini zani kasar turai.
Cikin kankanin lokaci muka isa AMINU KANO international airport, tunda naga jirgin dazai daga damu na yarda bana yara bane saboda haduwarsa, ya isa a nunashi a ko'ina.
Ban dauki lokaci ba aka gama tantanceni na juyo na karbi jakunkuna na mukai sallama da mufida...
****************************
Shigata jirgin ya tabbatar min da abinda dadyna ya fada, tsaruwarsa daga ciki yafi yadda nake ganinsa daga waje domin ya wuce duk yadda nake tsammani.
kai tsaye sit dina na wuce na zauna duk da cewa yaune karon farko dana shiga jirgi irin wannan amma ban yarda na nuna hakan ba don kada wadanda ke cikin jirgin su raina ni.
Abinda na lura dashi shine kowa naji da kansa a cikin jirgin sbd daga manyan attajirai masu tafiya kasuwanci sai yayan attajirai masu zuwa karatu irina, babu ma zaton samun dan talaka a ciki bare a samu din. Kamar yadda aka shirya 11:00am dai dai jirgin ya daga kai tsaye izuwa birnin london tafiya mafi tsawo dana fara yi a rayuwata, jami‘an cikin jirgin kuwa sai nan nan ake damu duk abinda muka bukata ba bata lkc ake bamu.
Awanni nata shudewa 2n ina sha‘awar tafiyar har sai dana gaji amma bamu iso ba, duk na kosa sbd wannan ne karon farko dana taba yin tafiya irin wannan daga karshe madai wani nannauyan barci ne ya kwashe ni ban farka ba sai AIRPORT na birnin londôn, A hankali daya bayan daya muka sakko daga cikin jirgin.
wowwww!!! Nan fa naga abin mamaki domin ba birnin ba airport din kadai abin kallo ne ban taba tsammanin akwai wuri me kyau da kawatuwa irin wannan lallai duk yadda ake bada lbrn birnin nan ya wuce nan, duk yadda nakai da ji da kai sai dana zama kamar wata yar kauye a wurin.
saukowarmu keda wuya jami‘an filin jirgin suka yo kanmu nan fa aka shiga secreening kala-kala harda wanda ban taba ji ba ko a lbr, bayan na cika duk wani sharadine aka bani damar ficewa daga airport din, ban jima ba kuwa wata jibgegiyar mota me matukar fadi da tsawo ta iso like take da banner din OXFORD UNIVERSITY bamu dauki tsawon lokaci ba ta debemu tare da mutane daban-daban da muka zo daga wurare da kasashe maban-banta, Anan ne fa naji kwalta tamkar ita ta shimfida kanta, duk inda motar tabi titine luwai-luwai ba gargada bare rami.
Shuuuuuuu!!!!! A haka motar ke tafiya tamkar jirgin sama ban-bancin kawai ita wannan a kasa take tafiya ba‘a sama ba.
Gefe guda tsarin gine-ginen birnin wanda keda matukar tsayi tamkar zasu tabo can kololuwar sama sun kawatar dani matuka.
gashi kowa irin rayuwar da nafi so yake yi ta ba ruwan kowa da wani, kowa ka gani harkar gabansa yakeyi. jim kadan muka iso katafariyar jami‘ar daya daga cikin mafi girma, daukaka da suna a duniya, bayan komai ya kammalu kuma kai tsaye aka yimin jagora izuwa masaukina.
Ni kadai ce a sashin nawa wanda ya kunshi duk abubuwan da nake bukata.
************************* Nan fa na shiga karatu gadan-gadan kasancewarsa wajene da ko baka so sai kayi karatu, da farko na dauka a nigeria ne naci gaba da jiji dakai da takama sai naga ina!! domin a banza wajene da kowa keji da duk abinda nake ji dashi shima. Dole tasa na sakko na fara maraba da kowa nan da nan kuwa na tara kawaye masu yawan gaske tamkar bani ba, na saki jiki da mutane sosai. Da yake ba karatu ne irinna na nigeria ba cikin shekaru biyu kacal na kammala degree na na farko a hakan ma don mun sami dan tsaiko ina daya daga cikin wadanda suka sami sakamako me kyan gaske hakan yasa makarantar ta bani damar yin masters degree kyauta kasancewar ina jin dadin zaman yasa na amince na zarce cikin ba tare da jinkiri ba. shekara daya kuma na kammala masters, degree biyu cikin shekaru uku kacal, wannan shine tarihin kara2na da yadda na samu masters degree a kasar birtaniya.
“hmmm..... Lallai gskyr Bahaushe da yace ‘Talaka bawan Allah‘ domin talakan nigeria ne zai kwashe shekaru hudu yana neman diplomer bai samu ba“
Ahmad ya fada sanda ya kauda kansa daga kan littafin lkc guda ya mayar da kansa ya dora. kammaluwar komai tasa na tattaro inawa-inawa nayo nigeria, ranar laraba misalin 12:00pm jirginmu yayo nigeria.
dirarmu keda wuya dady ya iso tare da wasu daga cikin yaransa aka daukeni direct mukai gida, nan fa girman kai, takama, gadara da raina mutane ya dawo sabo fil. Na fara jin nifa yanzu nafi kowa kuma samun kamar ni sai an tona kai zaiyi wuya ma a samu mace kamar ni da tattara abubuwan da nake dasu.....
Hmmm'un yanxu akapara shirin..!
BARKAN KU DA ASUBAH..!