Tijjani yacigaba da cewa Ina dai jajanta maka na
abnd ya samu y‘arka amma ba2n aure babu gsky ba yadda za‘ai kamar ni ace na auri gurguwa, da harkokina zanji ko kuma da jiyyanta?
Kafin na taho munyi magana da dad dina kuma ya fadawa da duk wadanda a bangarenmu muka gayyata cewan an fasa bikin nan.
An fasa??
Daddy ya tambaya ckn kaduwa.
kwarai na hakura da ita don bazan iya zaman KADDARA ba, daddy ya kara sanyaya murya yace “haba TIJJANI abin fa ba wani me muni bane likita ya tbbtr min zata dawo normal ckn y‘an lkt kankani.“
Tijjani ya mike tare da cewa “Alhaji kaga tafiyata, na isar maka da sakon daya kawoni.“
Ya gyara zaman suite din jikinsa ya juya ya nufi hanyar ficewa duk da kiran da daddy ke masa TIJJANI!! TIJJANI!!!.
Amma ina! ko alamun waiwayowa baiyi ba dai-dai lkcnne nida momi muka fito ina zaune bisa keken guragu irin na zamani a hankali momi ke 2rani har muka karaso tsakiyar falon momi tabi kofar fitar da kll ta dawo da kllnta ga daddy tace “Tayaya kake tsammanin zai dawo??
Bayan dama ba don Allah yake sonta ba??
Koda ma ace anyi auren idan kaddara irin wannan ta sameta juya mata baya zaiyi!
Amma abin tambayar me yasa shi mahaifinsa ya ki tilasta masa ya aureta a haka??
Shi ya manta amincin dake tsakaninku??
Na tbbtr yana sane amma zai iya danne wannan ya nunawa dansa syy abnd kai ka kasa yi kuma ka kasa ganewa kenan.“
daddy ya 2nbuke hular kansa ya jefata kan kujera gaba daya ya rikice dakyar ya karasa kujerar da tafi kusa dashi ya zauna ya dago kamar ya fashe da kuka yace “kinga shugaban kasar CHAD yanzu haka ya sauka a hotel kuma don daurin auren nan yazo, banda wadanda suka 2ro wakilansu, ga sanatoci ga gwamnoni banda abokaina manyan y‘an kasuwa na duniya duk sun hallara abin kunyane na 2nkaresu da maganar an fasa bikin nan, inna-lillahi wa inna-ilaihir raji‘un....“
Yakai maganar dakyar.
Hmm... Zaune kawai nake ina binsa da kallo bama ta tawa yake ba ta yadda zaiyi ya fita kunya kawai yake, ba a wanne hali nake ciki ba.
Hankalinsa ya tashi ma2ka fîye da ko yaushe sbd abnd baiyi zaton zai faru ba ya faru, Amma ni a wurina hkn yafi yaimin don gara na tbbt a yanayin da nake ciki da na auri tijjani.
o-o-ooo!! Ina zansaka raina???
Daddy ya sake fada kamar zai rushe da kuka don takaici.
Budewar da kofar tayi da karfi yasa duk hankalinmu ya koma gareta, kamar daga sama FARUK ya fado da saurinsa caraf muka hada ido dashi duk da a yadda yake ba‘a farin ciki yake ba amma bai hana annuri tashi daga fuskarsa ba.
Yanayin tfyrsa ya canja ya fara takowa a hankali muna klln juna.
Nayi saurin cewa “FARUK meya kawoka?? me kazo yi??
Kayiwa Allah ka juya ka tafi karka yarda ka kara kusanto inda nake sbd ni yanzu bani kadai bace tafe nake da rakiyar KADDARA, yayinda BALA‘I da MASIFA ke take min baya.
Yayi saurin girgiza kai yace “Ba wata kaddara da zata iya sawa na gudu na barki, karki manta Alkawarinmu na kasancewa a tare duk tsanani duk wuya.
Da ace ba wata masifa da zata iya riskar dan adam toda har abada ba za‘a taba iya gane masoyi na hakika ba, sai kaddara ta afku ne kawai ake iya gane soyayya ta zahiri da kuma ta karya don haka yanzu ne yafi ko yaushe cncnta na nuna miki soyayya.“
Na daga kaina sama wasu sanyayan hawaye suka gangaro min, ya tako izuwa inda nake ya durkusa ya dafa keken da nake kai yace “Sannan idan zaki 2na na taba gaya miki cewa ba ina sonki don wani abu naki bane ko don moruwar wani abu daga gareki, ina sonki ne a matsayinki na humaira kuma zanci gaba da sonki har abada.“
Ya mike tare da duban daddy yace “Idan har ka amince ni zan auri HUMAIRA a haka, zan zauna da ita domin bazan taba guje mata ba har abada.
Babu bukatar duniya tasan abnd ya faru da ita bare makiyanmu su sami bakin yi mana dariya.
Fuskar daddy tayi saurîn washewa, wani sbn annuri ya saukar mata ya mike tare da cewa “Lallai faruk ba‘a banza ba humaira ta yarda da kai yau na gani da idanuna don nayi imanin ko ni ban fika son humaira ba, laifi nane da nayi yunkurin hana abnd Allah ya kadarta.
Nagode da kayi yunkurin rufa min asiri da kuma masoyiyarka.
Lallai samun masoyi kamarka za‘a dade ana tonawa.“
Faruk ya gyara tsayuwa yace “Don na rufawa HUMAIRA asiri ba wata bajinta nayi ba domin kaina nayiwa.“
Daddy ya gyara babbar rigarsa yace “idan kuwa har kayi min haka nayi Alkawarin baka dukiya me tarin yawa kuma zan dauki nauyinku kai da ita ba abnd zaku nema ku rasa.“
Faruk ya girgiza kai yace “bana bukatar komai daga gareka indai akan HUMAIRA ne sbd daga ranar da na samu humaira hakkin kula da ita da samar mata da farin ciki akaina yake kuma dole na saukeshi.“
Daddy yayi saurin cewa “uhm!! kaji masoyin gaske masoyi na hakika yanzu kai kana ganin a shirye kake??“
Faruk ya gyada kai yace “kwarai kuwa!! abinda kawai nake so a dauke daurin auren daga gobe a matsar zuwa jibi idan zai yiwu.“
Ah! kwarai kuwa sosai ma!!
Don dai kwana daya kawai??
Faruk ya kada kansa tare da juyowa muka kurawa juna ido, ni kaina ya bani mafi girman mamaki a yau, domin duk yadda nake hango HALACCIN faruk ya wuce nan.
DAN HALAK farar fuska farar zuciya.
Har yanzu hawaye ke kwararowa daga idanuna har na fara hango yadda sabuwar rayuwarmu zata kasance duk da cewa bata zo mana a yadda muke so ba.
Ya goge hawayen dake idonsa har ya taka izuwa bakin kofa sai ya juyo yace “kayi hakuri amma Sai kasa an kwashe wadancan gardawan banzan daka tara a bakin gate izuwa asibiti sbd ta karfin tsiya na bigesu na shigo nan.“
daddy yayi saurin gyada kai yace “KARKA DAMU KAYI DAI-DAI.“
Ya juya tare da yimin klln karshe ta wani irin salo kmr zaiyi magana amma sai ya fice, nabi daddy da kll na durkusar da kaina na fashe da kuka kmr raina zai fita.
Kukan na abubuwa da yawa ne da suka cunkushe zuciyata, ko yunkurin rarrashina ma ba wanda yayi zuwa jimawa MUFIDA tazo a lkcn ina daki ta zauna a falo momi ta zayyane mata duk abnd tijjani ya fada da tsananin mamaki ta dago kai tace “amma TIJJANI anyi tsinannen mu2m mara mu2nci da bashi da imani a zcyrsa, ynz momi shikenan komai ya rushe???
Ta girgiza kai tace “FARUK yazo kuma yace yaji ya gani ya amince ba abnd za‘a fasa, sai dai nifa ina jin tsoron al‘amarin nan sosai.“
MUFIDA tadan yi gun2n murmushi tare da girgiza kai tace “babu abin tsoro momi, 2nda nake ban taba ganin soyayya irin ta HUMAIRA da FARUK ba, wlh momi yadda kika san da son junansu aka haliccesu 2n fil‘azal.
A kyalesu kawai tbbs da abinda Allah yake nufi a tryyrsu.“
Momi ta kauda kanta kawai ba tare data sake cewa komai ba, mufida ta mike ta nufo dakina.
Kwance nake na kishingida akan makeken gadona na zubawa kafafuna ido hawaye na zuba daga idanuna, mufida tadan rufe min ido tare da bina da kll tace “haba HUMAIRA meye haka??
kuka bashi da wani muhimmanci a gareki sbd bai isa ya dawo miki da abnd kika rasa ba, a zatona farin ciki zan tarar kinayi Allah ya kadarta abnd kike buri.“
ckn sheshsheka nace “Dole nayi kuka sbd shi kadai ne abnd zan iya yi a yanzu, ba haka naso rywr aurenmu tazo mana ba.“ Shi kuma Allah haka yaso.
Tayi saurin fada tare da dorawa “Allah na tsara abubuwansa ne yadda yaso ba wanda ya isa ya canjasu, amma dai na tbbtr ko a yayane zakiyi dauwamammen farin ckn zama da faruk wannan kawai ya wadatar.“ Haka dai kalamai irin nata na RARRASHI tayi ta jerowa.
*Faruk kuwa isarsa gida keda wuya ya fadawa wadda take uwa da ubansa kudirinsa da kuma taimakon da yake so tayi masa, duk da cewa bata fiya fushi ba amma a wannan karon sai data canja.
Tabishi da kll tace “A zatona kana da hankali amma ka canja.
HUMAIRA ce kadai mace a duniya??
ka manta abnd suka yi maka kenan??
sai yanzu da suka shiga wani yanayi sun kada gabas da yamma basu da me rufa musu asiri shine suka taho wurinka kai sbd kafi kowa wauta ka yarda ko??
kai wannan bai zama abin kunya bama a gareka??
Mutumin nan bakai kawai ya wulakanta ba harda iyayenka wadanda su zasuyi maka wakilci su kuma dame zaka 2nkaresu da yarda su dawo su shige maka gaba??
2n wuri ka cire wannan daga ranka don bame yiwauwa bane.
Fuskarsa ta canja kmr ya fashe da kuka yace “amma ummi mahaifinta ne yayi mana laifi ba humaira ba, ni kuma yanzu humaira nace zan aura ba mahaifinta ba laifin wani yana shafar wani ne??
Ta dan zaro masa ido tace “EH yana shafa! indai ina na isa na fada ka dauka to ka rabu dasu da y‘arsu idan a jibin kake son auren ni ina da wadda zan baka gasu nan da yawa ma.“
Faruk yayi saurin girgiza kai yace “ni HUMAIRA nake so ita zan aura kota yaya ni naji na gani 2nda ni zan zauna da ita.“
Ta daga kai sama tace “TO!! tashi daga kasa ka dawo kan kujera muyi magana 2nda ka zama abokina.“
Ummi ba haka nake nufi ba amma...
Ta katseshi da fadin “wai Yaushe ka koyi musu da gardama irin wannan to bani da lkcn musayar zance akan maganar banza tashi ka tafi.“
Dole tasa ya mike ckn nuni da hannu yace “don Allah ummi ki.....“
Ka bacemin nace ko??
Ta katseshi.
Ya saki hannunsa kawai ya bita da kallo kawai.
“Allah ya wuci zcyrki.“
Ya fada sanda ya wuce izuwa sashinsa, bangarene me zaman kansa da falo guda gefe guda kuma ga dakinsa gdn nasu dai-dai gwargwado na rufin asiri ne.
Ya zauna jim kadan ya zaro wayarsa ya lalubi lambar bbn abokinsa NAZIR yana dagawa yace “kazo gida don Allah yanzu ina son ganinka,
............
Ah lfy kadai zo yanzu.
................
OK sai kazo.
Ya mike ya wuce dakinsa min2na kadan yaji motsin zuwan nazir yana fitowa nazir wanda 2ni ya dare kujera yace “HUMAIRA!! HUMAIRA!!! kllm zancenka kenan wai da gaske kai ahaka zaka aureta...?
Faruk yadan tsaya a hankali ya tako tare da bata rai yace “Eh a hkn ko zaka hana nine??“
Yayi tambayar sanda ya wuce izuwa karshen falon ya dauko lemon juice da kofi ya juyo izuwa inda nazir ke zaune yace “idan munafuncin daya kawoka kenan ka tashi ka tafi.“
Nazir ya warto kofin da faruk ya dora a dan karamin tebirin dake gbnsa ya zuke lemon cknsa yace “haka akeyi? ka gyyceni kuma ka koreni??
kawai dai nayi mamakin yadda kayi haka anya baka nuna rashinzuciya ba??“
Faruk ya grgza kai yace “Nazir ba haka bane ni HUMAIRA bata taba yimin laifi ba, bada yawunta, sonta ko yardarta abubuwan da suka faru suka faru ba hasalima jajircewa tayi sai ni sbd tana da yakini akaina, don haka idan na juya mata baya yanzu ita nayiwa ba wani ba.“
nazir ya jinjina kai yace “kazo da zance kaima, ynz dai me kake so ayi??“
Faruk ya gyara zama yace “So nake pls ka sanar da kowa jibi daurin aurena kowa ya shirya ba, nasanka da zafin nama a shirya komai ckn lkc nasan zai yiwu??“
Ah! kwarai me zai hana?? ai ko gobene bazamu kasa kintsawa ba bare jibi.
Faruk ya dago yace “Na sani, zan 2ra maka isassun kudi a account dinka yanzu so nake komai ya kintsu ckn kwana biyu kmr anyi shkr biyu ana shiri, ga mukullin nan (ya jefa masa) na gdna ne nasan kasanshi shima a gyarashi gyara bana wasa ba a shiryashi a kintsashi kada ya rasa komai da ake bukata.“
Nazir ya mike tare da sarawa yace “an gama ‘leader‘ yayi kasa da murya yace “amma dai UMMI fa dole...“
faruk yace “karka damu shawo kanta a guna bame wuya bane kai dai ka zartar da aikinka ka barni da nawa ka hanzarta kaga dare ya taho yi .“
Nazir ya taka kmr zai fita sai kuma ya juyo ya rike baki yace “um!! gskyne gaf kake da kafa record fa saurayin daya zama ango ckn kwana biyu.“
kana gaf da zama MAI GIDA.....
Faruk ya nunashi yace “kai! bana son iskanci, na.... yayi kmr zai bishi.“
Nazir ya kyalkyale da dariya ya fice da sauri.
Faruk ya koma dknsa.
*WASHE GARI da safe faruk ya fito byn ya gama duk abnd zaiyi a falo ya tarar da ita zaune a kujera ya gaisheta ta amsa sama-sama.
Faruk ya gyara zamansa yace “Ummi gameda maganar nan ne ta jiya ina so....“
Kace game da maganar banzan nan ce ta jiya, ta mike tare da juyawa zata bar falon, faruk yayi saurin mikewa ya tsaya a gbnta ya saki hawayensa data fi tsanar gani fiye da komai ya durkushe bisa gwiwoyinsa yace “Don girman Allah ummi ki taimakeni ki fahimceni, kin sani ban isa na aiwatar da komai ba sai da izininki kuma bazan taba bijirewa umarninki ba domin kece komai nawa.
Ina so nayi wani abu ne guda daya dazai gyara abubuwa da yawa kuma ya samar da alkhairai da yawa, ciki harda ladan taimakon wanda yake bukatar a taimaka masa wanda kin dade kina kwadaitar dani akan haka, kinsha fada min na zama me juriya da yafiya a koda yaushe.
Humaira batayi mana laifin komai ba hasalima keda kanki yabonta kike kuma itama bata so akai mana haka ba idan na gujeta a yanzu ba wani nayiwa ba ita nayiwa, na tbbtr idan na barta zata shiga kangi da takura fiye da ko yaushe a rywrta nasan kuma kema ba zaki so a gujeni don wata kaddara ta fada min ba!!“
Jin tayi shiru yasa ya kara tausasa lafazi yace “2n ba yanzu ba kin dade kina fada min yadda karshen rayuwar masu HALACCI, CIKA ALKAWARI da RIKE AMANA take yin kyau ki taimakeni na zama daya daga cksu don Allah.“
Ta bishi da kll da alama kalamansa sun ratsata ma2ka, da dawo da baya izuwa kan kujerar jim kadan tace “kai yanzu wane shiri kayi??
Shirina bame wuya bane umarninki kawai nake jira.
Ina ka shirya kaita to byn auren??
Ta sake tambayarsa.
Ya bata amsa da fadin “Gidan da kika fada min cewa shima nawa ne dana gada a wurin mahaifina kuma kika bani mukullinsa da komai nashi da hnnki can zan kata mu zauna idan kin amince.“
Shikenan ya zanyi da yin Allah?? Na amince Allah yasa hkn shi yafi alkhairi.
Fuskar faruk tayi gaggawar washewa yayi saurin mikewa ya dawo gbnta ya zauna tare da cewa “Abinda nake so ki fada kenan ummi nasan kuma zaki amince shi yasa nake godewa Allah daya bani ke NA GODE sosai ummina, amma kina ganin su kawu zasu amince kuwa??“
Ba dole ba??
Tayi saurin fada.
Kaifa maraya ne kowa so yake yayi maka abnd zaisa kayi farin ciki ko don ya sami lada ka bari zamuyi magana dasu kaje kawai.
ckn farin ciki faruk ya fita daga gdn.
Hakika abnd Allah ya kadarta faruwarsa babu abinda ko wanda ya isa ya dakatar dashi.
Da ana SO da ba‘a SO, Ana kuka ko ana dariya, dole aka daura aurena da faruk a ranar da lokacin a kuma inda aka shirya.
Ranar da bazan manta da ita ba a rayuwata, daga waje biki yayi armashi ma2ka sbd ba wanda yasan halin da ake ciki, kai ko a gdn wadanda ya zama dole su sani ne kawai suka sani.
A gdnmu kam naira jknta ya gaya mata, daddy masu sakin famfon kudi haka kawai ma bare da dalili.
Kowa yayi mamakin faruk da irin abubuwan da yayi a sannan ne daddy ya tbbtr faruk ba irin talakan da yake tsammani bane!!
Washe gari byn komai ya lafa dare nayi aka kaini gdn faruk, gdn sabuwar rayuwa, gdn farin ciki, gdn jin dadi da walwala.
Ba wasu mutane masu yawa bane suka rakoni hakan yasa ba jimawa kuwa kowa ya watse ya zamana daga ni sai MUFIDA, ina zaune bisa shimfideden gadon da a yanzu nake jinshi fiye dana sarauta ma daya zarce na alfarma.
Mufida na zaune sai zuba take ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, da yake uztaziyya ce a nasihar tata harda ayoyi da hadisai, maganganun nata na ckn ratsani naji tayi shiru jim kadan ta mike tare da jawo mayafinta da jakarta zata fice, nayi gaggawar dago kai na damko hannunta wasu hawaye sukayi saurin gangaro min nace “MUFIDA kema tafiya zakiyi ki barni ni kadai??“
Ta bini da kallo tausayina ya bayyana karara fuskarta, ta dawo ta zauna gaf dani tace “dole zan tafi sbd nan gdnki ne ba namu ba, gasu can a waje ni kadai suke jira mu tafi FARUK yananan tafe KIYI HAKURI.“
Ta banbare hannunta daga nawa ta fice tana waigena.
Daga nan sai naji ni a wani irin yanayi, ba wanda zai zauna??
Wace irin rayuwa na shigo kenan??
Kodai basa sona shi yasa kowa ya tafi??
Tunanin da yayi ta yawo a zcyt a wancan lokacin..!
Hmm da kina tunanin xasutayaki xamane...
Koya wannnan zaman aure zekasance..? Se ku biyoni INSHA ALLAH..!