Duk maganar da za‘ai dake sai kinyi kokarin dangantata da FARUK??
zaifi yi miki kyau ki hakura da soyayyarsa...
Fuskar momi ta canja ma2ka irin yanayin da ban taba gani ba tace “amma Alhaji rashin tausayin da rashin imanin yayi yawa wlh, a ina aka taba....“
DAKATA!!
ya fada sanda canja fuska, yace “ince dai y‘ata ce ko??
nina haifeta??“
Auren dole fa kake shirin yi mata!! Haka na gadama.
Daddy yayi saurin mayar da martani. Nabi daddy da kll wasu hawaye masu zafi tamkar tafashashshen ruwa suka gangaro bisa kuma2na, na mike muryata na rawa nace “Kayi zabinka da kake ganin yayi maka, amma hkn ba lallai ya zama zabin ubangiji ba wanda zabinsa shine mafificin zabi don haka har yanzu banji a jkna na rabu da FARUK ba.
Na taka a hnkl izuwa dakina.
Momi Ta kada kai tare da cewa “wannan matakin naka Ba komai kake sonyi ba face cutar da ita wlh, ta tashi 2n daga kuruciya bata san meye takaici ba bata san meye damuwa ba lkc guda kana kkrn tusa mata su toka sani idan humaira ta haukace karka zargi kowa face kanka,“ Ya hade rai yabita da kll kawai ya doka tsaki ya koma kan kujera ya zauna ya zaro jaridarsa ya fara karantawa.
*A kwana a tashi kwanaki sai kara matsowa suke, Abu kmr wasa yana nema ya zama gaske, ckn kankanin lkc zance ya karade ko‘ina cewar bikina saura y‘an kwanaki ai kuwa duniya ta dauka kmr guguwar yaki.
Ban kara tbbtrwa abin gaske bane sai da ya rage sati daya, wasu akwatina dana iske sunyiwa falonmu tsinke da ni kaina bansan adadinsu ba aka ce wai kayan lefe nane, hakan ya girgizani ma2ka lallai daddy da gaske yake.
Kmr a mafarki haka nake ganin abin gashi kuma yana nema ya tbbt gaske, kuka 2n hawaye na zuba har sun daina ma zuwa.
Ba komai nake hangowa ba sai rayuwar da zata zo min a gaba ta shekaru masu yawa da zanyi ckn takaici da damuwa watakila na har abada, abinda na dauka shine aure shine last distination na duniya a wurin mace walau ta dace da rayuwar farin ciki ko takaici na har abada.
Illolin mace ta auri wanda bata so sun wuce a misaltasu, a yadda nake jin tsanar TIJJANI wlh a duniya ma bana son ganinsa yana rayuwa ina kuma ga ace mu zauna har abada???
Wadanda ke waje basu san meke faruwa ba gani suke ai hadin ya dace har tayani murna akeyi ta waya, ciki harda wadanda bansansu bama abnd ke kara min takaicin kenan.
Wasu ma ganin da suke yi ni na juyawa faruk baya sbd dan uwana me kudi yazo, dadai sauran zan2ka ire-iren wadannan.
ba wanda yasan gskyr abinda ke faruwa sbd ba wanda na sanarwa, abune da nake zaton cewa nafi karfinsa yazo yafi karfina, abnd nake ganin bazai yiwu ba yake nema ya yiwu.
Lkcn daya rage saura kwanaki uku sai ya zamana duk gdn T.V ko radio daka kamo ba sai ka samu ana sanarwar DAURIN AURENMU, jaridu da mujallu duk an baza gari ya dauka auren y‘ar gata AISHA HUMAIRA ISMA‘IL yazo, harabar gdnmu har ta fara cika da mutane anata kafa runfunan alfarma na manyan baki da kanana.
a dai-dai sanda ya rage saura kwanaki biyu da safe ina kwance nayi nisa a duniyar 2nanin dana saba ban sani ba ashe mufida tazo ta shigo har dakina kuma ta zauna ban sani ba, ta dade tana kllna sannan ta tabani da cewa “KE“.
Na kakalo yake wanda yafi kuka ciwo nace “Ah mufida yaushe kika zo??“
Ta bini da kll kawai tace “HUMAIRA 2nanin me kikeyi haka??“
NayĆ® kasa da kaina kawai zuwa ca na girgiza kai tare da cewa “ba komai“.
Karyane wlh, ta fada tare da dorawa da fadin “Naji sanarwar aurenki rana tsaka, kuma abin mamakin da wani me suna tijjani ina faruk din kuma?? nidai a sanina shi kike so.“
Nayi kokarin hana hawayen da suka taho zuba amma na kasa, “bakisan abnd ya faru ba??“
na tambayeta.
Tayi saurin mayar min da amsar “Na sani amma zatona ke kika canja ra‘ayi da kanki don banyi zaton duk duniya akwai me tilastaki ba.“
Na girgiza kai nace “Daa kenan amma yanzu ta canja daddy ya daina kaunata ya tsaneni yafi son mu2 da bakin ciki akan na rayu.....“
Tayi saurin rufemin baki tare da rike hannuna ckn nata tana me grgz kai tace “karki ce haka, may be a ganinsa gata yake sonyi miki, addu‘a yakamata kiyita yi kawai a yanzu amma ba kuka ba sbd ba maganin dazaiyi miki a ynzu.“
taci gaba da tsara kalamanta wasu na gane inda ta dosa wasu ma na kasa ganewa har dai mukaĆ® sallama.
y‘an min2na wayata tadau ringing
Na jawota a hankali nayi arba da sunan TIJJANI!! me kuma ya bugo ya fada min??
kmr bazan daga ba amma Na daga tare da kaita kunnena, dariyar da yayi ce ta fara dukan kunnuwa na, yanzu fa kin hakura ko har yanzu kina da ja??
abnd ya rage dai bai fi awanni 48hrs ki tbbt amaryata“.
Duk yadda naso na danne kuka na sai daya fito, tijjani yayi dariya yace “irin dan kukan nan na al‘ada a gurin amare ba sbn abu bane“.
Amma kai mugu ne wlh ba tausayi ko imani a zcyrka ko kadan, Ya kara fashewa da dariya na saki wayar ta fado bisa katifar makeken gadon da nake kai, nayi ruf da ciki kawai na rufe idona sautin kukan ma baya fitowa.
Tsawon lkc na kwashe a haka har sai da wayar dake kusa dani ta sake daukan sabuwar kara, Nayi wata irin dagowa a fusace na warto wayar a zatona tijjani ne sai kuma fuskata ta canja.
Faruk ne nayi saurin dagawa tare da kaita kunnena sautin sheshshekane kawai ke kaiwa da komowa, dakyar nace “faruk shikenan mun rabu ko??
ki jirani zanzo har gdnku yanzu.“
A firgice na dago kirjina ya buga da karfi, gdn suwa?? karka zo zasu cutar dakai fa!!
FARUK!!
sai dai ina! tuni ya kashe wayar.
Ina ckn frgbr ne kasa da min2na ashrn naji hayaniya na tashi a hrbr gdnmu, na tbbtr shine bansan sanda na zabura da gudu na fita daga dakin ba maimakon na nufi wajen rikicin amma ba dama kai tsaye saman bene na nufa na tsaya gaf da farfajiyar saman ina hangen abnd ke faruwa.
Turewa, hantara harma da dukan da daka-dakan samari majiya karfin suka farmasa ne yasa na dafe bangon dake kusa dani ina me miko hannu hawaye na kwarara daga idona, Tausayinsa yai bala‘in kamani.
Faruk me yasa kazo?? Nayi tambayar badon a bani amsa ba.
Da yake umarnin da aka basu kenan a knknn lkc sukayi masa lilis!!
Wani layi da naga yana yi ne ya kara rikitani karfa su kasheshi, zuciyata ta fada min.
nayi wata irin juyawa da gudu na biyo hanyar da zata sadani izuwa inda abin ke faruwa sai dai bisa tsautsayi dora kafata bisa matattalar benen keda wuya na zame tare da rikitowa 2n daga kololuwar saman benen zuwa kasa......Zamewar ce tasa ba shiri na rikito gadan-gadan izuwa kasa, a maimakon na mirgino ta matattakalar sai jikina ya zamo nayo kasa kacokan. Tazarar dake tsakanin kasa da sama nada yawa na kwarara uban ihu wanda shine iya abinda na sani ban kara bude ido ba sai a gadon asibiti.
Awanni masu yawa ne suka shude ina ckn yny na suma, lktci sunyi nasarar ceto rayuwata daga halaka bayan tsawon lkcne kuma na farfado.
A hankali idanuna suka bude tamkar wadda ta farka daga barci ni kaina abinda ya fara fado min kenan barci nayi, nayi saurin karasa bude idanun nawa a sanda na tbbtr nan ba inda na sani bane a ina nake meya faru dani??
Nayi yunkurin tashi naji an danneni a sannan ne nabi inda nake da yanayin da nake lkc guda duk abinda ya faru ya fado min, Na dubi kafafuna dake mike a dai-dai gwuwoyina ansa wani kurunbon roba daban san ko meye ba.
Sai fuskata dake kunshe da ciwuka na kujewa dama sauran sassan jikina, Na daga kaina mukai ido hudu da momi sai kuma MUFIDA dake zaune a gefena.
bana jin bakina zai iya furta komai hakan yasa banma yi yunkurin cewa komai ba, naci gaba da jujjuya idanuna ina kallon faffadan dakin asibitin.
A wane hali faruk ke ciki kada dai ace sun kasheshi?? Abinda yayi saurin fado min kenan, Wasu hawaye suka gangaro min.
budewar da kofar dakin tayi da saurine yasa muka kalli hanyar shigowar daddy ya fado a firgice, nayi saurin dauke kaina daga kllnsa.
Ya karaso inda nake yana ganin yanayin da nake ciki ya dafe kai tare da doka salati ya juya ga momi a rude yace “wane hali ake ciki??
me likitan yace muku??
momi ta girgiza kai tace “Ba abinda ya fada mana yadai ce kawai idan kazo yana son ganinka.“ Inna-lillahi wa inna ilaihir-raji‘un. Daddy ya sake nanatawa ya gyara zaman babbar rigarsa tare da juyawa ya wuce izuwa ofis din babban likitan dake kula da sashen.
Zaune lukutin bakin mu2min yake yasa faffadan tebirin dake gabansa a gaba sai rubuce-rubuce yake, shigowar da yaji tasa ya dago kai.
Sannu da zuwa Alhaji ya fada tare da mikewa don girmamawa.
Doctor wane hali yata ke ciki?? meya sameta??
fuskar likitan tayi saurin canjawa ckn nuni yace “bismillah Alhaji zauna“
Ya fada dai-dai sanda shima ya zauna.
Koda daddy baiso ba dole tasa ya zauna a kujerar dake fuskantar likitan ckn tsananin zakuwa da son jin abinda zai fada masa.
Likitan ya gyara zama yace “Alhaji kasan ita fadowa daga sama irin wannan na zuwa da abubuwa daban-daban wani lkcn a sami karaya, rauni koma a rasa rai dungurungum.
Anyi sa‘a bata rasa ranta ba ba kuma a samu karaya ko daya ba, hakan ya farune sbd sanda tazo kasa da gwiwa tazo shine yasa....“
Shine yasa me.....
Daddy yayi saurin tambaya a firgice.
Likitan ya gyara zaman farin gilas din dake idonsa yace “ Kasan a yadda gwiwa take ita ke daukar dawainiyar iya taka kafa gaba daya ko kuma iya karyata a zauna daidai sauransu.
Magana da gsky kokon gwiwarta dukkansu sun sami matsala munyi kokari mun dai-daitasu daga gocewar da sukai amma sunyi sanyi ma2ka sbd buguwar ba y‘ar kadan bace hakan yasa zata dau dogon lkc bata iya taka kafarta kamar yadda kowa yake yi ba.
Doc..tor me kake...nufi ne??
Daddy yayi saurin tambayar.
Abinda nake nufi shine a yanzu kafafunta basu da maraba dana karamin yaro don haka za‘a dau lkc bata iya taka su ba.“
Ckn kallo me kama da harara daddy yace “kada dai kace min ta zama gurguwa??“
Kayi hakuri alhaji amma ta zama, sai dai kawai na wani dan lkcne zata dawo taci gaba da tafiya kmr kowa.
Daddy baisan sanda ya cire hular dake kansa ba ya sake doka salati tare da goge gumin dake kwaranyo masa ya matso gbn kujerar tare da dafa tebirin dake tsknnsa da likitan yace “doctor yanzu ba yadda za‘ai?? kasan kudi ba matsalata bane ko nawa ne zan iya biya kada ta zama nakasashshiya doctor.“
Wannan ba magana bace ta kudi 2nda kokai nasan baka taba jin inda akai dashen gwiwa ba, dole sai dai ayi hakuri ba abnd za‘a iya yi kuma duk inda kaje ina da tbbcin haka abin yake.
Kuma da yake ynyn larurar tata ba wadda dole jinyarta sai a asibiti bane nan da wasu y‘an awanni idan komai ya dai-daita muna iya sllmrku.
ku koma gida aci gaba da kula da ita a kula kada ku sake tayi yunkuri na taka kafar sbd a yanzu kafarta tamkar ta jariri take.
Daddy ya dago tare da dafe kai yace “ynz shikenan ckn y‘an awanni y‘ata ta zama gurguwa???“
Sai dai hakuri.
Likitan ya fada.
A sanyaye daddy ya dawo dakin da muke, ina kwance nabi fuskarsa da kll har izuwa sanda ya zauna yaune karon farko da naga hawaye a idonsa.
Kmr yadda likitan ya fada haka kuwa akai domin a ranar aka sllmemu, abnd yafi bani mamaki shine nidai bana jin wani ciwo a kafata sai dai kawai ji da nake tamkar kafafuwan ba ajikina suke ba.
Ko kadan bazan iya motsa su ba, KADDARA kenan idan tazo babu me iya canjata kasa da awa 12 na zama gurguwa.
Rayuwa ta kara juye min bangare mafi baki da muni, na shiga kangi na bala‘i da masifa da ko a mafarki ban taba 2nanin zan shigesu ba.
WASHE GARI tijjani yazo har gdnmu ko dakina inda nake bai karaso ba a falo ya zauna anan daddy yazo ya tarar dashi ya zauna tare da cewa “TIJJANI kaga abnd ya faru ko??“
Wlh naji Alhaji.
Ya fada fuskarsa a daure, babu alamun walwala tare dashi.
Daddy ya gyara zama yace “amma KADDARA baki iya zuwa ba, um-u-um!! yanzu ya za‘ai tijjani??“.
Game da me fa??
Ah game da harkokin bikin nan mana kasan duniya ta gama sanin gobe ne ga manyan baki sun hallara an gama shirya komai bai kamata ace anji kunya ba.“
Ban gane ba Alhaji.
Tijjani ya fada.
Daddy ya gyara zama tare da matsowa gab da kujerar ckn kasa da murya yace “a bari a daura auren nan idan yaso koda tarewar ne sai a daga ya zama dai an fita kunya...“
Allah ya kiyaye!!
Tijjani ya fada tare da dorawa da fadin “wani zancen aure gsky a barshi Alhaji me za‘ai da HUMAIRA bayan ta zama NAKASASHSHIYA?????“
hmmm ALLAH YASA KUNA KARANTA SHIRINMU NA "BANBANCIN SHA'AWA DA SOYAYYA"wata kila kugane meyasa tijjani keson humaira
uhmm allah hadamu damasoyanmu nagaskiya badon wani abu namuba..!