Tambayar dana fara yiwa kaina kenan tambayoyin suka cgb da yawo a zuciyata.
wai me yasa daddy ke yimin haka ne??
Sai yanzu a lkcn da yakamata ya samar min farin ciki fiye dana ko yaushe yake kokarin dakile hakan??
Na dade a haka zan2kan na karo da juna a ckn kwakwalwata, dakyar na rarrafa izuwa kan gadona na kwanta kawai idona a bude karrr amma 2nanin dana tafi yana kama da ace barci nake yi, ni kaina bansan yadda zan kwatanta ynyin da na shiga a wannan lkcn ba.
Allah sarki faruk kawai nake 2nawa wanda ban taba ganin mu2m irinsa ba, hakurinsa kawai ya isa yasa na kara kaunarsa dubi yadda daddy ke fada masa bakaken maganganu amma ko kadan ba saima ya zamana kmr kara masa karfin gwiwa yake yi.
Ni dai duk ranar ban ma koda yi sha‘awar fitowa daga dakina ba. washe gari kuwa da wani azababben ciwon kai na tashi wanda ina tsammanin ban taba yin kmrsa ba, sai duk da wuyar da yake bani ban damu ba don ba shine a raina ba abinda ya dame ni daban, momi cema ta rude ta takura min akan lallai mu tafi asibiti amma naki don ni nasan meye dalilin ciwon. Can misalin karfe uku na rana ina kwance abin duniya ya isheni ina son na kira faruk amma na kasa, ringing da wayata ta dauka yasa na dago kaina na mika hannu na jawota ina me runtse ido sbd yadda kaina ke sarawa.
hmm.. DAN HALAK na fada a zcyt sanda nabi secreen din wayar da kll a hankali na daga tare da kaita kunnana sautin muryarsa ya ratsa jikina na kwantar da kaina bisa gadon na amsa sllmr da fadin “W salam farin wata sha kallo.“ Nayi saurin zarcewa da fadin “Don Allah ya kuka karke da daddyna jiya??“
Ya danyi dariya yace “kina so kiji na jiraki 30minutes koki dan rakoni, na kira wayarki har sau uku baki daga ba?? sannan baki kokarin kirana ba a tsawon awannin da aka shafe da faruwar abin??
Na dan kauda wayar daga kunnena dama a jiyan ya kirani?? Lallai na shiga wani yanayi da yawa. Na mayar da ita tare da cewa “uhm! faruk kayi hakuri da wannan, amma dai don Allah ka fada min ya akai??“ Yayi murmushi tare da cewa to kin shirya??
Da sauri harda gyada kai nace “EH“.
Ya fara zano min hirar 2n daga farko duk yadda na jita haka yake fada sai da yazo kan gabar da nake so nayi saurin mikewa zaune duk da karuwar da sarawar da kaina keyi amma na jure duk don naji abnd banji ba, ya karasa daga dai-dai inda na tsaya da ji da fadin:
“.....don haka bawai zan yarda ka auri humaira don kun dace bane ta bangaren dukiya ko alfarma ba sai dai don kun dace da son junanku, dôn haka lallai ka 2romin magabatanka ckn kwanaki uku rak!! domin muyi magana.“
Idona yayi saurin budewa kaina dake mummunar sarawa ya daina, bugawar da zuciyata keyi na fargabar abnd zanji ya daina, Nayi saurin gyara zamana nace “Faruk da gaske??“
“Kwarai“ ya amsa tare da fadin “kina mamakin daddy ya bani ke ko da kina tsammanin zai hanaki wanda kike so??“
Wani yalwataccen murmushi ya fadada a fuskata farin ciki sabo ya ziyarci zucita na koma kan gadon na kwanta tare da cewa “Baka san yadda akai bane!!“
Sai dai idan kin fada min, yace.
Na kada kai nace “To ai ni jiya labewa nayi ina sauraron hirarku farkonta kawai naji hankalina ya tashi 2n jiya ba‘a dai-dai nake ba wlh.
Faruk yayi dariya yace “To banda ke wa yake hukunci da farkon abu ba tare da yaji karshensa ba?? Ashe ni ban sani bama tauraruwata bata ckn walwala?? Nifa duk nayi 2nanin farin ciki ne yayi miki yawa.“
Na gyara kwanciya nace “INA!! ban taba yin barci harda mafarki alhalin idona yana a bude ba sai jiya, Ga wani ciwon kai da nayi me taba kwakwalwa.“
Ya sake yin gajeriyar dariya yace “TO!! amma ina fatan kin warke??“
Na gyada kai nace “Eh mana kana fada min lbrnnan naji na warke.“
Dukkanmu mukai dariya.
Kina sona da yawa fa!!
Ya fada.
Na dan zunburo baki nace “kai kuma fa??“
Yace “Ni? hm.. bawai SO kawai ba akwai KAUNA da SHAKUWA da BEGE gareki a koda yaushe gami da ALKAWARI wanda bazai canja ba duk rintsi duk wuya ba wani dalili na rabuwa har mu2wa.
Na lumshe idona kawai muka cgb da hira ckn frn ciki da walwala na tsawon lkc sannan mukai sllma.
Sai sannan naji wata YUNWA ta taso min domin duk yinin yau dama banci komai ba.
lallai na dawo hyycn na fada sanda na mike na wuce izuwa kitchen.
*duk da cewa ina da shakka akan daddy amma lkc guda duk wani bakin ciki ya fita daga zuciyata naci gaba da harkokina ckn walwala, 2nanin zan iya rabuwa da faruk kawai na sawa in kwanta rashin lfy ina kuma ga an rabamu din?? Shine kawai abnd na tbbtr bazan iya jurewa ba.
** Kamar yadda daddy ya nemi faruk ya 2ro haka kuwa akai bayan kwanaki uku da daddare suka zo, ina dakina na kishingida bisa tafkeken gadona fuskata fresh ba kyalkyali kawai take tana walkiya, zuciyata tayi fari, wayata nakan WHATSAPP messenger muna hira da faruk.
Ina jin alamun hirarsu sama-sama sai bana iya fahimtar abinda suke cewa, har sanda suka gama tattaunawarsu suka tafi.
Farin ciki kmr ya kasheni idan na 2no gaf muke da fara sabuwar rayuwa wadda nake hangowa 2n daga yanzu, farin ckn nawa bai yanke ba sai washe gari da naji abinda ya wakana tsakanin daddy da iyayen faruk.
Faruk ne ke fada min ta waya, 2n da naji yana cewa in nutsu kada hankalina ya tashi nasan da matsala, ashe daddy rufe ido yayi ya zabgawa iyayen faruk rashin mu2nci hade da bakaken maganganu tare da yin alkawarin yarsa tafi karfin tozarcin auren talaka kamar dansu (FARUK).
Tunda ya fara fada min maganar na mike tsaye, sanda yakai karshen lbrn kuwa zcyt ta gama harzuka, kwakwalwata ta dimauce, idanuna suka kada sukai jajir duk a ckn kasa da sakanni 30.
Wayar ta subuce daga hannuna izuwa kasa ta tarwatse komai nata ya rabu da jikinta amma ban kula ba.
Abin kuma harda yaudara??
Wato daddy na ganin idan ya biyo ta haka iyayen faruk su zasu fara tilastawa ya rabu dani.
Nayi dawurwura a guri daya na juya da karfi na bangaji kofar dakin ta bude na fito da gudu na izuwa falon momi na tarar a zaune bisa kujera tayi saurin dago kai tace “Lfyrki kuwa??“
Na tsaya a gbnta nace “wai momi me yasa daddy keyi mana haka ne??
Koda yana son rabamu ne bai kamata yaci mu2ncin iyayen FARUK ba!!
Ashe daddy na falon rufewar da idona yayi ne yasa na gaza ganinsa.
Yace “kaji shashasha talaka har yana da wani mu2nci ne???
Nayi turus kawai nabi daddy da kallo wani takaici da bakin ciki suka rufeni, wlh badon dai ubana bane a wannan lkcn Allah ne kadai yasan abnd zanyi.
Na dawo da baya a hankali izuwa tsakiyar falon duk da cewa ckn fushi nake ma2ka amma nayi kokarin sanyaya zuciyata na saita harshena ckn salo na marairaicewa nace “amma daddy bai kamata ka gyyto mutane da kanka kuma ka tozarta su ba, idan har kasan haka zakayi 2n farko gara ace FARUK din ka fadawa amma ba iyayensa ba.“
Daddy ya matso da hularsa gbn goshinsa yace “Ok! kina nufin muyi sulhu dashi kenan na bashi hakuri ko??
Ai hakan da nayi shine kawai abnd yafi a gareni domin iyayensa sunji zafin wutar maganganun dana watsa musu dole ma su tilasta masa ya rabu dake.“
RABUWA!!!
kalma mafi daci a gareni kenan har sai da takai na kauda kaina kadan lkc guda na dawo da fuskata gareshi nace “daddy talauci, arziki ko wata daukaka duk na Allah ne shike bada su ga wanda ya gadama a sanda yake so kuma ba abnd ke tbbt face kudirar ubangiji muma arzikin da muke takama dashi Allah ne ya bamu kuma badon munfi kowa bane.“
Daddy ya kwantar da kansa jikin kujerar da yake kai yace “EH!! nafi ki sanin wannan ai.“ Na dan matso gaba kadan nace “Ashe kenan ba wata hujja da za‘a ce yar me kudi ba zata zauri dan talakawa ba? tunda duk Allah ya haliccesu ya.....“
Kaji shashanci banza!!
Daddy ya katseni tare da cewa “har akwai wata alaka tsakanin mai arziki da talaka da har zata kai ga aure??
Ai a doka ma hanyar jirgi daban ta mota daban ba yadda za‘ai na siyar da akuya ta dawo tana cimin danga ba.“
Na danyi yaken takaici nace “Indai don wannan ne to karka damu domin dai-dai gwargwado FARUK nada rufin asiri zai iya sauke duk wani nauyi na dake wuyansa kuma koma ba wannan ba ni faruk ko kasa ya kawo min zan dafa mana mu ci.“
Bawai daddy ba har momi sai data dago kai a firgice, daddy yayi saurin duban momi yace “wai yarinyar nan da hankalinta kuwa??
Anya talakawan nan ba asirceta sukai ba??“ Na girgiza kai nace “bawai asiri bane hakan na nuna zunzuru2n SON da nakewa faruk.
na durkushe bisa gwiwoyina na canja izuwa ynyn da dole a tausaya min nace “Daddy don grmn Allah ka taimaki rayuwata wlh faruk nake so domin ina da tbbs akansa kayi min komai 2n daga kuruciya har izuwa girmana wannan shine abu na karshe da zaka samar min wanda zan cgb da rayuwa ckn farin ciki har abada, FARUK bashi da wani aibu na yarda kayi duk binciken da kake so akanshi indai ka samu aibu tare dashi nayi alkwrn zan hakura.“
Daddy ya gyara zaman bakin glass din dake idonsa yace “bincike??“
yayi nuni da hannunsa da cewa “Talaka har yana bukatar wata ne?? Halin talaucin da yake ciki kadai ya isheshi hujja, Bansan sanda kika lalace haka ba kika manta ko y‘ar waye ke!! to idan ke baki da hankali ni bazan biye miki ba.
Ranar auren y‘ata ina saran shugaban kasa da kansa zai halarta, gwamnoni, sanatoci, yan majalissu uwa-uba manyan y‘an kasuwa a kasarnan zasu halarta kawai sai ace ina ango aga wani talaka ya shawo kwana??
Kema kinsan bazai yiwu ba akwai masu sonki da yawa y‘ay‘an gata ki zabi wanda kike so a cknsu amma dole ki hakura da wannan FARUK din.“
Ban taba sanin daddy haka yake ba sai yanzu, a wannan lkcn ji nake duk duniya ba wanda yakaishi rashin imani, zuciyata tayi harzukar dana kasa dannewa na mike kawai nace “ni kuma bazan rabu dashi ba kuma bazan auri wani ba face shi ma2kar dai ina numfashi a dorôn kasa, hakki nane a barni na auri wanda nake so tunda bashi da wani aibu, hawayen idona ya karasa zubowa ckn sheshshekar kuka nace “wlh ko a kotu saina kwaci hakkina ba wanda ya isa yayi min auren dole!!!!“
Na juya nabar falon, daddy yabini da kll tare da mikewa, momi da bata tsoma mana baki ba tace “amma Alhaji....“
Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yace “tace ba wanda ya isa ko? ya kada kai yace To zata ga isar tawa.“
Ya gyara babbar rigarsa ya wuce dakinsa.
*Daga ranar komai ya sake sakwarkwacewa dady ya shiga amfani da damarsa da krfnsa wajen rabani da faruk.
sai da takai ya hana faruk zuwa gdnmu, kullin da yayi na cin mu2ncin iyayen faruk yasa shima suka masa lamba akan lallai sai ya rabu dani.
Soyayyarmu na karuwa kalubale na daduwa, takaicin safe daban na rana daban na dare daban.
Soyayya nada koguna da yawa nikam na ruwan zafi na fada, ga tarko ya rike min kafa hagu da dama na rasa yadda zanyi na kwance, sama da sati daya ko a waya na daina samun FARUK hakan ya gigitani ma2ka har sai da takai abinci ma ya gagareni ci duk na rame tamkar bani ba, rayuwar da ban taba zaton zata juya min ba.
Cikin bakin ciki kmr yadda na saba nake zaune a yau ma, zaune nake ni kadai a tafkeken kayataccen falon gdnmu wanda yanzu ya zame min tamkar kurkuku na zauna bisa doguwar kujera dan karamin filo na dora bisa cinyoyina tare da dafashi sbd 2nani idona ma baya kiftawa hankalina 100% baya jikina.
Dafa nin da momi tayi yasa nayi firgigit tamkar wacce ta farka daga barci nabi momi da kallo da jajayen idanuna tamkar gauta, nasan danniya kawai takeyi ita kanta amma abin ya dameta.
Ta zauna tace “Humaira me yasa kike hakane??
Kefa ba karamar yarinya bace da zaki mayar da kuka mafi tasiri akan komai naki.
wannan 2nanin da kike yawan yi baki san babbar illane a gareki ba??
Akan hakan gara kiyi addu‘ar Allah ya zaba miki abnd yafi alheri.
Momi in auri faruk kawai shine alheri.
Tabini da kll tace “FARUK!! FARUK!!! FARUK!!!!
Kllm maganarki kenan???
Uhmmm nima allah ban wadda xatasoni kaman haka..koda wata tacemin she love me morther dt bet amma bataso wai asan tana sona agidansu..its a true love..?lolxxx
GOOD MORNING...!