**** BAYAN WATA BIYU DA KAMMALA MAKARANTARMU ****
Ranar wata juma‘a da bazan manta ta ba tun misalin 4:30pm dana kwanta a dakina na kishingida kaina bisa lallausar katifar gadona sanyin A-C na ratsani ta ko‘ina daga na‘urorin sanyaya dakin, fuskata fresh ba wani abu dake damuna musayar sakwannin soyayya kawai muke yi ni da faruk. Murmushi ne kawai ke tashi daga fuskata a wasu lktn ma nayi dariya har da samba2na ni kadai, FARUK nada barkwanci sosai abune mawuyaci kuyi magana ta min2na dashi bai saka dariya ba.
2nda muka fara hirar ba wanda ya gajiya a cknmu sai da aka kira sallar magariba sannan mukai sallama a hakan ma ba‘a son ranmu ba, Na tashi nayo alwala na fito falo momi na zaune har ta idar da tata sallar na jawo darduma nima, kiran sunana da tayi yasa na dago kai tace “wai lfy naji ki kina samba2 harda dariya ke kadai?? Na danyi kasa da kaina nace sambatu kuma??
Ah momi da Fa..ruk... muke hira....“
Nakai karshen maganar a kunyace.
Tadan harareni ckn murmushi tace “OK hira ce tayi dadi ko??“
Na danyi dariya kawai na tayar da sallah ta.
Bayan na idar baifi da min2na biyar ba daddy ya shigo da sallamarsa duk muka amsa masa, zamansa keda wuya muka zarce da hira ckn nishadi da walwala.
Zuwa can daddy ya kwantar da kansa bisa kujerar da yake kai ya dubeni sosai yayi murmushi yace “My daughter yanzu ne lkc yayi da yakamata ace kin samu mijin aure domin mutane sun dade suna cece-kuce akanki amma na toshe kunnuwa na, Alhamdulillahi kin samu duk kulawa daga garemu da kuma gata lkc kuma yayi da dole muma zamu aurar dake domin ke macece babu wani gata na karshe daya rage muyi miki kamar aure.
Momi tayi murmushi ta dubeni tace “gskyne musamman da yake takai munzalin da ba abnd ya rage mata sai aure.
hmm... Kwanci tashi kenan ba wuya yau daddy da kansa na zancen ya aurar dani, a raina sai naji wani dadi domin damar da nake jira kenan gata tazo burina na daf da cika.
daddy ya gyara zama yace “akwai babban abkn kuma aminina wanda tsohon shugaban kasar nan ne to yana da dansa me suna tijjani.
bansan a inda ya ganki ba to dai yasa uban ya fada min wai yana sonki kuma harma mun tsayar da rana gobe zai zo ku tattauna ko Allah zaisa ku fahimci juna.
Kirjina ya buga da karfi na dago kai na dubi daddy kawai nama kasa cewa komai har ya tashi izuwa dakinsa, na koma kan kujera na zauna na tabe baki nace “Momi me yasa ba zaki gaya masa ba??“
In gaya masa me???
Ta tambaya tana dubana.
Nace “amma kuma kinsan ni ina da wanda nake so ta yaya.....“
Ta harareni tace “rufa mana baki mara kunya da akai ki tashi kije ki fada masa mana, ko ni kin taba fada min kina son wani??
Na kara mirgina kai nace “amma dai nasan kin gane ai don Allah ki fada masa kinji“.
Momi ta mike tace “KE! nifa a wannan harkar taku ba ruwana kinji.“
Ta wuce tabar falôn, nabi ta da kallo kawai na zamar da kaina na kwanta bisa kujerar da nake kai, to ma wai meye zaisa na dami kaina?? Nasan dai daddy ba yadda za‘ai yayi min auren dole.
Na dauko tantsamemiyar wayata kirar blackberry, zuwa can na kauda wayar daga idona a abinda daddy ya fada ya dawo min, nayi y‘ar gajeriyar dariya.
hmm... tab! wai dan tsohon shugaban kasa, to ai ni ko dan shugaban kasa me ci yanzu bai isheni kll ba.
Na lalubi lambar FARUK muka dora daga inda muka tsaya.
**Washe gari 2n misalin karfe 11:30 na safe jerin gwanon motocin alfarma har kusan guda goma suka shigo harabar gdnmu kowacce na takewa y‘ar uwarta baya, a dai-dai lkcn ina can sashin saman bene sbd inda na saba hawa kenan duk sanda nake bukatar kadaici a gdn namu.
Na bude labulen tagar dakin da nake ciki na hangi fitowar wanda na tbbtr shine tijjanin sai wani shan kamshi yake yake yana hura hanci cabinets na take masa baya, bansan sanda na zabga masa harara ba 2n daga nan inda nake alamar fara jin haushi da tsanarsa 2n yanzu kenan.
Na mayar labulen na koma kan katafaren gadon dake madaidaicin dakin na kwanta Allah-Allah nake kawai barci ya daukeni.
Jim kadan wata y‘ar aikin gdnmu ta hawo izuwa inda nake ta karaso tare da cewa “Ranki ya dade momi ce tace a gaya miki bakon ki yazo.“
ji nayi kmr na bigeta don haushi.
Inda a dah ne da tasha tsawa da fada intayi wasa ma harda mari amma da yake yanzu na canja daga kwance nace “salama kyaleni kinji, je kice mata kawai barci nake.“
Ba wata gardama kuwa ta juya.
Na jawo filo tare da gyara kwanciyata a raina nace ‘indai nice ya hada kansa da wahala‘, ko 2nanin na fito ma bana yi. Sai bayan akalla min2na 30 dan ni har na fara barci ma naji momi na kiran sunana.
Na dago kai na dubeta a jikin kofar dakin ta tsaya hannunta a kugunta ta hade rai zuwa can tace “baki san tijjani yazo fiye da min2na talatin yana jiranki ba?? ko ban aiko a fada miki ba?? wato sbd wulakanci shine kinsan da zuwansa kikayi kwanciyarki ko?? To ki tashi maza ki sauka kasa yana falo ke yake jira.“
Momi nifa..... Zaki fito ko zaki fito ba??
ta katseni tare da tsareni da ido.
Dole tasa na mike na sakko daga kan gadon na wuce ta gbnta kai tsaye dakina na dosa maimakon nayi wata kwalliyar kirki saina dakko katon hijabina wanda mafi yawa sai zanyi sallah nake sashi nasa har jan kasa yake ina ma ina da nikab wlh sai nasa haka dai na fito falon fuskata ba wani annuri nayi kicin-kicin, shi kuwa yana ganina sai ya wani bude baki wai murmushi yayi yace “sannunki da fitowa uwar kyawawa, ai ance min kina shiryawa ne nace a barki ki gama a nutse.“
Na girgiza kai nace “Ba wani shiri da nake yi kawai yanzu nayi niyyar fitowa ne.“
Ya dan daga kai tare da cewa “hakan ma ya birgeni, Ah kamar yadda nasan an gaya miki sunana TIJJANI nazo ne domin na sanar dake irin son da nake miki ina fatan zaki karbi syyta hannu bibbiyu.
hmm.. soyayya! na fada tare da dubansa sosai nace “kaga mallam tijjani ba wani boye-boye ko bata lkc da zamu tsaya yi, indai don wannan ne to ba zaka taba samu ba ka ngd da zumunci a matsayinka na dan aminin mahaifina ka tashi ka tafi kawai.“
Nakai karshen maganar tare da kauda kai.
Da alama yayi ma2kar mamakin maganar ya bini da kallo kawai zuwa can yace “Ah humaira ni kuma sai nake ganin duk duniya idan ta fuskar dace ne nafi kowa dacewa dake.“
Na dan saki murmushin rainin hankali nace
“hm.. a hakan??“
of course!! ya fada tare da dorawa.
“Idan kika duba dukkanmu y‘ay‘an masu hali ne, mahaifina tsohon shugaban kasa ne kuma yanzu haka yana wakiltar kasar nan a zaman koli na majalissar dinkin duniya, ke kuma mahaifinki shahararren dan kasuwa ne aduk fadin afrika.
Kinga kuwa ko tanan mun dace da juna.
Na dan jinjina kai nace “Ok! dama sbd dukiya zamu so junanmu kenan daga ranar da dukiyar ta kare mun rabu kenan??“
Na rufawa tambayar baya da harararsa.
Abin ya kulad dashi sosai ya dago kai sosai yace “yakamata ki sani nifa babban mu2m ne a kasar nan me dimbin dukiya ya zama dole ki girmama ni.“
Dukiya?? Na tambayeshi tare da dorawa da cewa “da motoci goma ka shigo nan a matsayinka ma na dan wanda dukiyar al‘umma ya rike, idan ka fita ka tambaya ina ma‘ajin gdnnan ya baka mukullin ma‘ajiyar motoci ka debi 100 idan kana so wadanda da zunzuru2n kudin halak ma aka siye su.“
Idanunsa suka zaro waje yace “kina nufin ni mahaifina barawo ne??“
Na kara gyara zama nace “maganar mu2nci kuwa babu 2nda aka wanko kafa aka taho barar abinda ba za‘a samu ba sbd alfarma ba zata samar dashi ba gashi kuma kudi basa iya siyanshi shine SOYAYYAR HUMAIRA.“
ya danyi shiru jim kadan yace “yakamata muyi magana ta fahimta pls karki manta daga nesa nazo duk domin ke.“
Nesa?? sai ka koma ka fadawa nesa da yan nesa abnd kaje nema baka samu ba, na mike na dora da cewa “bata lkcn ya isa haka zan shiga daga ciki“.
Ya dan marairaice yace “bai kamata kiyi min haka ba yakamata ki bani dogon lkc muyi magana ko dôn kasancewar nayo doguwar tfy.
Na juya tare da cewa “yanzu ma ai ba korarka nayi ba, ga T.V nan kayi kllnka son ranka amma idan ka gama karka kashe can an jima zan kalli wani program.
Na wuce kai tsaye na doshi dakina kan ma nabar falon shima ransa a bace ya mike ya fice, na juya na kyalkyale da dariya KORA DA KALAMAI kenan na tbbr bazai taba yin marmarin dawowa ba, dama ba SON gsky ya kawoshi ba kalarshi ma tafi kama data munafukai don duk abinda yake fada babu alamun har zuciyarsa hakane.
Na wuce dakina ban kara komata takansa ba
** Misalin karfe 8:00 na dare ina zaune bisa dardumata byn na idar da sallar isha‘i, kwala min kiran da naji ana yi kuma yasa na saurara dakyau.
Bisa mamaki daddy ne abinda bai taba faruwa ba kenan sai yau na jefa dardumar kan gado na tare da nufo falon, daddy na tsaye ckn fusata ya hade hannunsa biyu ta baya.
Na zauna tare da cewa “daddy barka da dawo.....“
Tun kafin na karasa Ya katseni da cewa “Menene dalilin da mu2m zai taso 2n daga katsina domin ke, kuma na gaya miki matsayinsa da kuma ko waye shi amma maimakon ki karramashi saima ki wulakantashi??
Me kika fishi??
Anji ma bakya sonsa ki mu2ntatashi mana idan nazo sai ki fada min baiyi miki ba insan yadda zanyi na sanarwa mahaifinsa amma sai ki bishi da bakaken maganganu??
Shekararmu 40 da mahaifinsa ke baki isa ki shiga tsakaninmu ba.“
Na danja da baya a kujerar da nake zaune nace “kayi hakuri idan hakan ya bata maka rai gsky bana sonshi ne ina da wanda nake so kuma shima ai da laifinsa don me zai......“
Tsawa daddy yayi min a karona farko a rayuwata da fadin “Ki rufa mana baki, ki shirya TIJJANI ne mijinki nan bada dadewa ba za‘a saka ranar aurenku.
Sbd girgiza bansan sanda na mike tsaye ba kaina yayi wata juyawa sau daya, na maimaita abnd daddy ya fada “TIJJANI ne mijina??“
Kwarai!! daddy ya fada.
Nace “koda hakan na nufin bakin cikina da tbbt a takaici na har abada??
Daddy ya amsa da “koda hakan na nufin mutuwarki da tbbt a kabari na har abada.“
Duk da matsananciyar damuwa data bayyana a fuskata, idanuna suka fito waje kamar zasu fado.
ba AL‘AJABIN mgngnunsa kawai nake ba, amma yadda idonsa ya rufe yake zazzaga min ruwan bala‘i ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba.
Ya kara da fadin “da bakinsa yake fada min kince masa MUMMUNA, BANZA, DABBA!! kmrsa ki fada irin wadannan maganganun??
Kawai ji nayi kmr an sare min gwiwoyi, lallai TIJJANI munafuki ne lamba daya abin nasa harda kage da sharri kenan??
Wasu hawayen takaici irinsu na farko a rayuwata suka gangaro min, Na gyada kai nace “ eh na fada masa haka sbd ya cncnci fiye da haka ma kuma zan kara gaya masa haka duk inda muka hadu, ckn sheshshekar kuka nace “daddy karka manta ka bani ilmi me yawa wanda yasa nayi wayewar da nafi karfin ayi min auren dole.
Bana sonsa!! Bana sonsa!!
Ina da wanda nake so kuma shi zan aura bana jin akwai wanda zai hana ni don addini ma ya bani dama.
Kuka na ya karasa fitowa na juya izuwa dakina, ina zuwa a hankali na zauna a gefen gadona na hada kaina da gwiwa naci gaba da ku kan da nake yi. Tijjani ne mijinki....
Koda hakan na nufin mu2warki da tbbt a kabari na HAR ABADA.
Kalaman dake kara yawo a zuciyata kenan, ashe har akwai ranar da daddy zai fada min maganar da zata sani damuwa? Akwai ranar da zai aje dunbin son da yake yimin a gefe ya fada min bakaken maganganun da zasu sani kuka??
Na dade a zaune a haka har zuwa sanda naji an dafa ni, nayi saurin dagowa muka hada ido da momi. Na kwantar da kaina bisa cinyoyinta ckn kuka nace “momi daddy ya daina sona yanzu,“ Ta dago fuskata muka fuskanci juna tayi saurin grgz kai tace “ba haka bane ransa ne ya baci kuma kema da laifinki bai kamata ki yiwa TIJJANI haka ba“.
Wlh momi abnd yace na fada masa duk karya yake yi ban fada ba.
momi tabi ni da kll tace “amma me yasa kika cewa daddynki kin fada??“ na goge hawayena nace “Sbd ya tbbr bana son TIJJANI.“
momi ta jinjina kai tace “yanzu dai kiyi shiru ki share hwynki, dadynki ba wanda yake so a duniya kmr KE duk abnd ya fada nasan bazai taba aiwatar dasu ba.“
Na karasa goge dukkan hawayen dake idona nace “ba lallai ya saurareni yanzu ba momi“.
Tayi murmushi tace “nafi kowa sanin halinsa bashi da wuyar sakkowa duk irin fushin da yayi jeki kinji??“
Na bita da kallo kawai a hankali na mike na doshi dakinsa gwiwata a sanyaye, Zaune na tarar dashi a tsakyr dakin bisa dardumarsa ya idar da sallah, na karasa inda yake na zauna a gbnsa tare da sunkuyar da kaina kasa ckn sanyin murya nace “Daddy don Allah kayi hakuri nasan ban kyauta ba kuma na bata maka rai dana......“
Nayi shiru sakamakon daga min hannu da yayi yace “Ya isa haka my daughter koda baki roka ba ya zama dole na yafe miki kan KUSKURE DAYA TAK!!.“
Nagode my dad na fada dai-dai sanda nayi yunkurin mikewa.
Ya dakatar dani da cewa “wanene wanda kike so din? kuma yaushe kuka hadu?
Ya akai bansanshi ba kuma??“
Na danyi shiru kmr bazan ce komai ba zuwa can nace “sunansa FARUK, A makarantar koyon kwamfuta muka hadu dashi kuma har gdnnan yana zuwa momi ma tasanshi tfyr da kayi ce ta tsawon watanni yasa baka sanshi ba.“
Ya kada kai yace “Wajibi nane na baki wanda kike so amma ki sani mafi girman gatan da zanyi miki a yanzu shine na tbbr na zaba miki miji nagari idan har na samu wani matsala game dashi bazan amince dashi ba.“
Na gyada kai tare da cewa “Insha-Allahu zaka sameshi duk yadda kake so,“ Shikenan kice masa yazo ina nemansa“.
Na amsa da fadin “To, Sai da safe my dad.“
Kai tsaye na fice daga dakin nasa na koma nawa, har yanzu momi na zaune bata tafi ba na zauna gaf da ita na saki murmushi tare da dakko hannunta na hada ckn nata nace “Momi kinsan me?? yace in fadawa FARUK yazo yana nemansa“
Tayi murmushi tace “Humaira kina son faruk da yawa fa!! kina barci ma fa kiran sunansa kike yi.“
Na danyi dariya nace “Ah haba momi a barci kuma??“
kiyi ta fadin FARUK! FARUK!! FARUK!!!“
Na kyalkyale da dariya, momi ta mike tare da cewa “idan zaki kwanta ki rinka kashe kwan nan haskensa yayi yawa.“
Ok gud night my mum.
Na fada ta juya ta fice.
Na karasa kwanciya kan gadon sosai na zaro wayata na nemi lambar faruk.
Mun dade muna hira dashi har sai da dare ya tsala sannan mukai sllma dashi byn na sanar dashi sakon daddy.
***FARUK bai zo gdnmu ba sai byn kwanaki biyu misalin 5:00 na yamma, daddy na gd a lkcn da kaina na fita na yi masa jagora izuwa falo inda daddy ke zaune bisa kujera.
ya amsa sallamar da mukai sai dai daga shigowarmu na lura da wani kllo da naga daddy na yiwa faruk anya kuwa....
Ya zauna a kasa daga jkn kujerar dake fuskantar daddy, ni kuwa mikewa nayi nabar falon har na shiga dakina hankalina ya gaza kwanciya na dawo da baya don jin hirar da zata gudana tsakanin FARUK da DADDY.
daga inda na tsaya ina hangensu tare da jin abnd suke fada.
*dai-dai sanda na tsaya faruk ne ke cewa “...cikakken sunana Umar faruk jibrin, mahaifina mllm jibrin dalhatu da mahaifiyata hajiya Hauwa‘u sun rasu 2n ina karami hakan....
Daddy yace “sunan mahaifinka mallam sunan mahaifinta Alhaji banbanci na (1) kenan, mahaifanka sun mu2 nata nada rai banbanci na (2) kenan, ina sauraronka.“
Ba tare da wani damuwa ba faruk yace “na sami yin kara2 kurewarsa shine degree dana samu anan bayero university...
Daddy ya gyara zaman hularsa yace “Ita kuma masters gareta a OXFORD UNIVERSITY england, another deference kenan.“
Faruk dai bai kula ba ya karasa da fadin yanzu haka ina aikin banki nakai matsayin activities-director.
Daddy ya kwantar da kansa ckn kasaita bisa kujerar da yake kai yace “Akwai banbanci me yawa tsakaninka da y‘ata wanda ya wuce a misalta, kasan ko danbe ake akwai wanda kll daya zaka masa kasan yafi krfnka!! Don haka.........
Jirin da naji yana neman dibata ne yasa nayi saurin dafe kaina nabi fuskar masoyina faruk da kll kawai na juya da sauri na shige dakina domin kunnuwana ba zasu jure jin maganganun da daddy ke fada ba, don na riga na gane inda suka sa gaba.
Ina shiga kofar na mayar na rufe nabi jikin kofar daga sama har kasa hawaye suka gangaro min, wai me daddy ke nufi ne?
Nima tan bayana kenan ga masu karatu..!
Medaddy kenune..?¿ Allah sa kuna fahinta..!
SABAHUL KHAIR..!