Mufida na isowa direban wanda har ya fara barci na daka masa tsawa ya farka ya juyar da motar muka nufi hanyar da zata sadamu da gida, Mufida ta dubeni tace “amma fa nayi mamakin yadda naga kuna hira da faruk harda dariya sai kace ba ke ba??“
Na kwantar da kaina kadan nace “manta da wancan faruk din lamarinsa sai shi.“
mufida tayi dariya tace “Ah kidai fadi gsky tbbs akwai wani abu“.
Ganin yadda take kokarin kureni yasa na kautar da zancen ban bari yayi nisa ba, har na isa gida.
*Abinda na kasa ganewa game dani shine: Nidai faruk na birgeni ma2ka, komai nasa naban sha‘awa, shine kawai a duniya da bana iya tozartawa ko in wulakantashi koda nayi niyya sai hakan ya gagara yiwuwa a wajena.
Ga yawan 2naninsa da nake yi a koda yaushe banda son kasancewa dashi a kowanne lkc da nake yi!! Shin wannan shine SO?? tambayar dani bansan amsarta ba kenan.*
Washe gari misalin karfe tara na safe tsaye nake a jikin wata faffadar bishiya dake harabar makarantarmu nesa kadan da inda dalibai ke zama, kasancewar yau an tashi da lullumi ga iska me dadi na kadawa yasa nake jin dadin wurin.
Gefe guda dalibai ne group-group masu hira nayi masu kara2 nayi, Ni kuwa littafine a hannuna ina karantawa hankalina gaba daya tafi ga kara2n, jin sallamarsa yasa dole na tsagaita daga kara2n da nakeyi duk da cewa ban dago na kalleshi ba.
Amincin Allah a gareki ya ma‘abociyar son kadaici da hutawa, Ya fada 2n yana nesa kadan dani. Dan kwalisan saurayi kllm kara kyau yake ya karaso inda nake tsaye yace “ina fatan dai kin shirya tambayar dazan bige a karo na karshe??? Nayi banza kmr banji abinda yace ba. Yayi murmushi yace “ Kinyi shiru kodai kin karaya ne??
Nayi yaken karfin hali nace “baka isa kasa na karaya ba, yau so nake ka fada min ranar da aka haifeni da watan da shekarar kayi jumulla ka fada min shekaruna nawa??
da wata nawa??
kuma da kwana nawa??
Nayi karatu a kasar waje ka fada min wace kasa ce kuma wacce university??
Na kumbura baki sanda nakai karshen maganar ckn gadara da takamar cewa na gama dashi.
Ya kura min ido kamar baisanni ba.
na kalleshi nace “yadai ka kasa cewa komai kodai ka karaya ne??“
Yayi murmushi yace “gskyrki da kika ce ko aljani yayi kadan ya amsa tambayarki tayau sbd shima baisan gaibu ba amma ina so ki sani SOYAYYA ba karya bace don haka duk abinda naji a jikina game dake to gskyne, zuciyata bata taba gaya min karya akanki ba don haka zan jaraba idan har son gsky nake miki na tbbt Allah zai bani nasara.
Ya taka kadan gaba da inda yake yace:
Irinku rayuwarku na tfy ne ckn tsari ba a hargitse ba don haka ina da tbbs idan nace, an saki a primary shekara shida sannan kika samu shekaru shida a ita primary din, kin secondary da shekaru 12.
kika gama secondary da shekaru 18 kika wuce university kika yi shekaru 3, jumulla shekarunki ashirin da aya (21) yanzu.
Tofa!! 2n daga nan idanuna suka zaro waje sbd AL‘AJABI.
Ya kara gyara tsayuwa yace “idan har jikina dai-dai yake bani an haifeki 1/6/1994 kuma kinyi kara2 a OXFORD UNIVERSITY ta kasar england domin itace burin duk wani dan gata irinki.“
Hmm... Nifa tun kafin ma yakai karshen zancen nasa bansan sanda duk abinda yake hannuna ya subuce ba naja da baya a dan tsorace, idan har faruk ba aljani bane to yana harka da aljanu.
Kallo daya yayi min ya tbbr ya amsa dai-dai ya tako inda nake tare da durkusawa ya tattaro kayana da suka zube kasa ya mike muka fuskanci juna yace “karki AL‘AJABI ko mamakin abinda ya faru a maimakon haka ki yarda Allah keson tarayyarmu, nasan kina sona tun tuni don na dade da gani a idanunki amma kina dannewa abnd kika manta shine zuciya ba‘a yaudararta akan soyayya yau dai wasa ya kare zamuyi soyayya abar kwatance indai da tsawon rai.
na karbi laptop dina da littafina harma da wayata daya miko min yaja da baya yace “Yes ki shirya daga yau an fara, I LOVE YOU.“
ya juya izuwa ga abokansa dake can gefe nesa sosai da inda nake, nabishi da kallo kawai na kwantar da kaina a jikin bishiyar da nake, wani murmushi ya kwace min Allah ya sani ina so kauce-kauce ne kawai irin nawa yau kuma karya ta kure.
Nadan dade ina cgb da tsayuwa a wurin har zuwa sanda lkcn shiga class, ko break yau ban fito ba yau sai da aka tashi na samu naja mufida bamu bata lkc ba muka tafi, kai tsaye gd muka nufa bayan da muka sauke mufida a gdnsu.
Isowata keda wuya da yake da yunwa na dawo kai tsaye kitchen na wuce na zubo abinci naci nayi sallar azahar sannan na jawo laptop dina na shîga aikina. Zaune nake bisa luntsumemiyar kujerar falon namu na tankwashe kafafuna laptop din na ajiye bisa cinyoyina gaba daya hankalina ya tafi ga laptop din sai shiga da fita nake, television dake yi ma kasheta nayi sbd karar ta dameni.
Tunda na fara ba kakkautawa sai naji an kira sallar la‘asar sannan na rufe na sakko tare da shimfida darduma na jawo katon hijab dina dana tanada musamman don yin sallah nasa.
Idarwa ta keda wuya momi ta fito falon ta zarce izuwa kujera ta zauna ta danna remote din dake rike a hannunta tafkekiyar T.V din dake manne a jkn bango ta dawo taci gaba dayi. Gamawata keda wuya na mike na koma kan kujera na zauna na jawo laptop dina na budeta, momi tace “aikin kenan bakya gajiya bakya daga kafa.“ Na danyi dariya nace “momi ai computer tayi, uhm don Allah momi dan rage karar t.v dinnan tana takura min, momi tace “don kina wannan shiriritar sai nabar jin abu me muhimmanci irin wanda nake kll yanzu??“
Nadan kumbura baki nace “ momi shiririta kuma??“
Eh an fada shiririta ai ni wannan makarantar taki da ita da shirme duk dayane a wurina.“
Na dan hade rai nace “ai kuwa momi ba shirme bace don kara2n computer na daya daga ckn mafiya tsada a duniya, kuma wlh yadda nake jin dadin makarantar nan ko OXFORD banji dadinta haka ba.“
Momi ta kauda kai tace “karyar banza!! yanzu dai ki tashi kije banki ki ciro min kudi zanyi baki gobe ba kudi a hannuna kinsan dadynki sai jibi zai dawo,“ Na dan cilla hannu nace “kayyyy!! momi kina gani aiki nake yi kuma.....“
Ta katseni tana kallona da cewa “OK ba zaki je ba kenan???“
Na mayar da kaina ga laptop din dake gabana nace “Zanje“
to ki tashi maza ki tafi kinga yamma nayi, na rufe laptop dina na nufi dakina kai tsaye bathroom na shiga nayi sabon wanka na wuce ma‘ajiyar kayana na saka wadanda suka dace dani a yanzu na dawo ga tafkeken madubina na zauna kujerar dake fuskantarsa zagaye dani kayan kwalliya ne bila-adadin kala-kala.
Bayan dana gama shiryawa na kalli kaîna bansan sanda wani murmushi ya subuce min ba, hmmm... wato ba karya ne ba ni nakai mafi kololuwa fagen kyau bama kyau kawai ba komai nawa daban ne domin abinda kesa wasu muni ni kuma kyau yake kara min bare kuma nasa abu me kyau, Na zama kwatankwacin zarah a ckn taurari gasu da yawa amma daka daga kai ni zaka fara gani.
Na fito izuwa harabar kasaitaccen ygdn namu ina takun isa, takama da gadara.
Direba ya taso da gudu tare da cewa “ranki ya dade ina zuwa haka??“
Na harareshi nace “Ba ruwanka da yinda zanje bani mukullin waccan motar,“ nayi nuni da CR-V din dake nesa kadan dani.
A tsorace ya miko min tare da cewa “amma.......“ Nayi saurin katseshi da tsawa nace “Yau nizan tuka kaina inda nake son zuwa ka koma kuci gaba da zaman munafuncinku, na warci mukullin daga hannunsa na shige motar na juyar da ita na fice nabi titin dazai sadani da inda zanje.
Tafiyar min2na 15 nayi na iso katafaren bankin nayi parking motata a inda aka tanada na wuce ckn bankin, Al‘adata duk sanda nazo kai tsaye wajen manager nake wucewa ya 2ra a ciro min abinda nake so in juyo na fito sbd asalinsa yaron dadyna ne.
Zuwana ofis din nasa dai-dai inda ya saba zama nayi turus don yau wanda nake tsammani bane ba abinda yafi kenan ba wanda ke zaunen 2n daga zamansa dress dinsa da komai nasa ma nasan ko waye.
Na tsaya akansa nace “ Ah!! Ya haka kuma?? Dalibi a wani wuri ma‘aikaci a wani wuri??
Faruk ya dago kai koda ganin nice sai ya saki murmushi ya gyara zama yace “ kina mamaki ne??
Na gyada kai dai-dai sanda na zauna a kujerar dake fuskantarsa nace “yes!! dole da mamaki mana kodai faruk din biyu ne bayan wanda na sani??“
Yayi dariya yace “Nine dai wanda kika sani don ba sunana husaini ba bare kice hassan dina kika gani, dama kina zuwa nan ne?? Ba tare dana dubeshi ba nace “shi yasa ma nake mamakin ganinka don ban taba ganinka anan ba sai yau.“
Eh gsky ba zaki ganni ba sbd ba anan bangaren nake ba yau ne kawai na dawo nan as temporary time kafin me kujerar ya dawo ya karbi wurinsa, ya dago idonsa yace “cire kudi, turawa ko kuwa kawai yawon shakatawa???“
Na dan yi dariya nace “Ah haba yawon shakatawa a banki kuma?? Bama dai zaka ji abinda ya kawoni ba......
Me yasa?????
Ya tambaya yana dubana.
Nace “sbd ba wajen ka aka turoni ba wanda aka 2roni wajensa baya nan kaga kuwa a matsayina na y‘ar aike dole na koma na fada idan ance na dawo wajenka na dawo!!“
Yayi murmushi yace “Nima zanyi farin ciki ki koma din 2nda na tbbr idan aka tambayeki wa kika tarar zaki ce masoyinki FARUK kika gane a wajen, kinga ko tanan na fara samun shiga a wajen momi da dadynki.“
Na zaro cak a jakata da biro na dora a tebirin dake gabana na fara rubutawa nace “Tayaya kake tsammanin zan fadi haka???“
Sbd nasan ba zaki taba yin karya ba.
Na tura masa cak din bayan dana gama rubutawa ya kira wani jami‘in banki ya umarceshi daya je ya ciro min kudin muka cgb da hira ckn nishadi, Na dubeshi nace “Lallai bayan kokari ma harda daukan dala ba gammo kake yi, AIKI irinna banki + KARATU irinna computer ba hu2 kenan???“
Ya kwantar da kansa jikin kujerar da yake kai yace “Aikin ne ya jawo kara2n kuma duk tare suke tafiya basu shiga lokacin hutu ba, Muna da rauni ta bangaren masu ilmin computer shine dalilin da yasa aka 2rani na karo sani akanta don cgbn wannan bankin, kinji dalili.“
Na bishi da kll nace “yanzu na gano dalilin da yasa bana ganinka in nazo, wato dan lele ne kai a bankin.“ ya daga kai yace “of course kamar yadda na zama dan lelen zuciyar humaira.
Nayi saurin girgiza kai nace “Waye ya gaya maka? Baka samu wannan damar ba ba kuma zaka taba samu ba har abada sbd ni zuciyata FARUK ne kawai a cknta kuma daga shi na rufe ba wanda zan sake bawa dama ya shiga bare ma har yayi tasiri.“
Ya dan lumshe ido ya dago kai yace “ faruk na godiya hade da alkawarin rike amana bata shekaru kawai ba ta HAR ABADA.“
Na jinjina kai nace “A wasu lktn alkawari nada saukin dauka amma saukewa nada ma2kar wahala“.
Ya gyara zama yace “Ina da tbbcn duk nauyin alkawari ma2kar ke na daukowa shi to zan sauke sbd ni akan SOYAYYA..... ni kaina mamakin kaina nake yi.“
Na bishi da kallo kawai, nima na dade da yarda yana da zafin soyayya, jim kadan jami‘in nan ya dawo ya dora leda bisa tebirin dake gbnmu tare da cewa “Sir, gasu an ciro.“
Ok thank you, koma bakin aikinka.
Ya 2ro minsu yace “An cika aiki.“
Na kauda kai nace “OK a takaice dai kora ta kake ko??“
Ya girgiza kai yace “Mezai sa na koreki?? Alhalin kece fitilar dake haskawa zuciyata hanyar daya kamata tabi?? Gani dai nayi kawai kin samu abinda ya kawo ki.“
Na juyar da kujerar da nake kai izuwa gefe nace “Amma ban gaji da klln faruk ba“.
Yayi murmushi yace “Shima bai gaji da ganinki ba sai dai idan kuka kwantar da hankalinku wannan rabuwar ta wucin gadi ce domin zaku hadu a rayuwa ta har abada.“
Na saki murmushi kawai.
Yayi saurin matsowa gaban kujerarsa yace “yauwa ni kuwa na manta ban karbi lambar sarauniyar tawa ba, na dago wayar dake hannuna kaina na kanta nace “ Ai da farko na zaci itama zaka canka ne 2nda shi yafi komai sauki a wajenka.“
Yace “Eh don dai kawai idan kika bani da kanki zata fi martaba ne a idona, amma da sai dai kawai kiji kira.
Na 2ra wayata izuwa gabansa nace “ai ko ifritu ba yadda zaiyi ya canki lambarnan dai~dai.“ Yayi dariya kawai ya 2ro min wayoyi biyu na dauki tashi lambar na mike tare da rakiyarsa na fito daga bankin.
Na dubeshi nace “kaga me girma manager nifa bance kayi min rakiya ba.
Yayi murmushi yace “bai dace ba ace sarauniya kamarki tana tafiya babu dogari ko daya a gefenta.“
Na girgiza kai nace “A yanzu ai ba sarauniya da dogari bane ke tafiya, SARKI da SARAUNIYA ne.“
murmushi ya fadada a fuskarmu har zuwa sanda muka karasa jikin motata, ya bude kofar gaba tare da dora hannunsa a goshinsa ckn salo na sarawa tamkar wani soja yace “shiga da lfy tauraruwar taurari.“
nayi murmushi kawai na shiga na zauna ya mayar da kofar ya rufe da yake glass din a sauke ya dafa kofar da hannunsa biyu yace “murmushinki ya dace da fuskarki kwatankwacin yadda ni dake muka dace da juna, sai mun hadu next time farin ganina.“
Ya juya ya koma ckn bankin nabishi da kallo murmushi na tashi a fuskata har sanda na daina ganinshi a hankali na daga glass din motar tare da takata na nufi gd.
Wannan shine tarihin asalin fara soyayyata da FARUK.
************ ************ ****
Daga ranar ne kwanci tashi alakarmu na kara karfi har takai soyayya me karfi ta shiga tsakanina da FARUK wadda tafi gaban a kwatanta, har takai mun zama ababan misali domin bawai tsakaninmu kawai ba kowa yasan alakarmu da kuma karfin syyrmu.“
Musamman a makarantarmu wanda kowa yayi mamakin ganinmu tare rana tsaka muna soyayya tamkar bani ba, daga nan ne kuma na zama ta mutane muka fara kulla abota da mutane daban-daban ta silar faruk.
Ban taba jin son wani bil‘adama a duniya kmr FARUK ba kuma ban zaci zan tsinci kaina a hakan ba, takai ga bana iya yi masa musu a duk abinda ya fada, bana ganin rashin dai-dainsa a duk abinda yayi, Sa‘a daya da nayi da shima yana ma2kar sona domin idan son da yake min baifi nawa ba to nawa bazai fi nasa ba.
Kasantuwar kusanci da karfin syyrmu yasa har aka fara kiranmu da sunaye daban-daban wasu suce LAILA da MAJNUN, wasu suce ANGELICA da MACIOLA dadai sauransu.****
FARUK ya kasance haifaffen garin kano kmr ni, ckkken sunansa UMAR FARUK MUHAMMAD yayi primary, secondary da university duk a garin kano, ya karanci irin abnd na karanta mathematic economics a BUK. Lbrn rayuwarsa daya bani wanda nafi tausaya masa shine kasancewarsa maraya.
Ya rasa mahaifansa 2n yana karami ta silar hatsarin mota, ya taso ne a hannun kishiyar mahaifiyarsa me suna hajiya amina, yana yawan ambaton sunanta a koda yaushe domin a cewarsa itace gatansa a duniya ita zame masa uwa da uba ta rikeshi tamkar dan data haifa a cknta har izuwa yanzu.
Ni kaina na yaba da halayenta da kirkinta ranar farko da faruk ya kaini gdnsu muka gaisa da ita, ba shakka yayi sa‘ar samunta matsayin wacce ta rikeshi har izuwa grmnsa.
A duk ma‘aikatan gdnmu ba wanda baisan FARUK ba domin sai da takai idan direba yakai ni makaranta FARUK ne ke dawowa dani a motarsa sannan ya wuce, kai harta da momi ma tasanshi kuma tayi farin ciki da ganinsa ta yaba dashi sosai duk da ban fada mata ba amma ta fahimci abinda ke tsakaninmu.
Kwanci tashi har lokacin gama makarantarmu yayi bayan tsawon lkc da muka shafe, ranar karshe ta rufe laccarmu bayan mun fito na nemi faruk banganshi ba mufida kuwa na can ckn kawaye suna irin sallamar nan tasu ta kawaye, nima nayi sallama da iya wadanda na sani da yake yunwa nake ji kai tsaye restaurant na dosa domin gani nake kmr bazan iya kaiwa gd ba, zamana keda wuya na umarci dan matashin saurayin dake jigilar kawo abinci na gaya masa abinda nake so ya kawo min.
A hankali FARUK ya karaso tare da zama a kujerar dake fuskantata ya dubi me kawo abincin tare da cewa “kai kawo min abinci da sauri.“
Na dubeshi nace “wane irin a kawo maka abinci baka ga na riga ka bane??“
Ya dubeni ya tabe baki yace “ina ruwana ni??“ ya juya gareshi yace “ kai aje a kawo min ka taho da juice me sanyi.“
Na kara hade rai nace “baya yiwuwa wlh na riga ka don haka dole ni za‘a fara kawowa.“
Me kawo abincin ya tsaya kawai ya kasa tfy ya dubemu yace “to ai ni na rasa yadda zanyi daku ai duk kun rudani, pls daya ya hakura a fara kawowa daya mana.“
Faruk yace “kai manta da ita dallah jeka kawo mana.“
na kauda kai nace “a manta dani ko a manta dakai.“
Ya kalleni ya bata rai yace “karki ce zaki raina ni fa don bana wasa da yarinya ranki zai baci yanzu.“
Na zabga masa harara nace “sai dai naka ya baci wlh.“
Ya hade rai tare da mikewa ya nuna ni yace “KE!!“
Na mike nima na nunashi nace “KAI!!“
Muka dan dubi juna na tsawon lkc jimawa kadan muka kyalkyale da dariya yace “gsky kin iya fa sai kace gaske??“
Na zarce da dariya nace “Na iya koka iya gsky dakai actor ne zaka kwashi yan kllo“.
Kai! dama ba fadan gaske kuke ba???
Me kawo abincin ya fada ckn AL‘AJABI.
Faruk yace “kai dai je ka kawo mana abinci don sarauniyar tawa yunwa take ji.
Har aka kawo mana abincin hira muke kafin mu gama mu tashi.
Daga ranar mukai sallama da makarantar domin mun kammalata sai dai koda NI da FARUK kllm sai munyi waya ta tsawon lkc, ko mu kasance muna hira ta WHATSAPP wataran kuma har gdnmu yake zuwa.
Haka muka cgb da rayuwa ckn jin dadi kafin KALUBALE ya biyo bayan soyayyarmu wanda yayi sanadin zubar hawaye na HAR ABADA.
Wannan wani QALU BALENE..?
Bari in barku haka kar kuce nacika surutu..
SABAHUL KHAIR...!