Ina nan zaune ni kadai bisa tsakiyar makeken gadon da nake kai, jikina na sanye da kaya na alfarma kaina na kasa kirjina na dukan uku-uku na rashin sabo.
Sallamarsa da naji tasa naji wata nutsuwa tazo min sautin muryar tasa ya daki kunnuwana kai tsaye ya fara zagaye a kwakwalwata, ban dago kai ba shi kuma baiyi magana ba ya zauna ta salo na fuskantar juna ya kura min ido kawai.
Na dan dago kai a hankali na dubeshi nayi saurin mayar da kaina, yayi murmushi tare da cewa “yes dago mana ya kika fasa my AMARYA!!
kodai tsorona kike ji??
Na girgiza kai nace “Koda ace za‘a wayi gari kowa ya zama abin tsoro a gareni na tbbt banda kai.“
To ki dago kanki.
Na yace mayafin dake kaina tare da dago kai fuskata wadda hawaye ya gama jikata sharkaf ta bayyana.
FARUK yadan yi baya da kansa kmr yaga abin tsoro yace “Kuka kuma?? Maimakon murna da farin ciki??“
Na girgiza kai ckn sheshsheka nace “ni nafi cncnta nayi kuka fiye da kowa, mafi yawan amare nayin kuka amma na munafunci ne ni kuwa nawa kukan na dolene sbd rayuwa bata zo mana a yadda yakamata ba, laifin me mukaiwa duniya da tayi mana wannan horon FARUK...??
ya kauda kansa tare da cewa “ki daina fadan haka HUMAIRA ba muka iya da yadda Allah ya kaddara, Ai dai gamu a tare matsayin MA‘AURATA wannan shine bbn abu mafi jin dadi daya kamata ki rinka 2nawa. Na kara kasa da murya nace “ma‘auratane mu amma ba kmr saura ba 2nda mu muna da nakasu ta bangarori da yawa kowacce amarya takan zauna ne a tankwashe amma ni kafuna kaga a mike suke daga sama har kasa ba wani motsi da zasu iya yi, kaga kenan ni nakasashshiya ba wani amfani da zanyi a garek......“
Yadan zaro min ido tare da katseni yace “HUMAIRA!!“. yabini da kallo ya dora da fadin “don Allah ki daina fadar haka, idan baki manta ba a baya na taba sanar dake cewa ba ina sonki ne don bukatuwar samun wani abu daga gareki ba, ina sonki ne a mtsynki na humaira gnnki a kusa dani kawai ya wadatar dani.
Kuma ai larurarki ta iya wani lkc ce ba‘a ce ta har abada ba don haka zaki warke kuma muyi rywa kmr sauran MA‘AURATA.
Tarayyarmu bata wani dan lkc kankani bace ta har abada ce, babu wani dalili dazai rabamu har abada.
Ki rinka 2na wannan a koda yaushe.“
Ckn sheshsheka nace “a baya na dade ina hango yadda rayuwar aurenmu zata kasance ckn farin ciki walwala da jin dadi sai gashi tazo mana akasin haka, tazo da babban nakasu.“
faruk yace “ki daina kawowa zamanmu babu farin ciki sbd kawai kina da larura, duk inda HUMAIRA da FARUK suka kasance tare akwai tbbcin farin ciki a wajen a kowanne irin yanayi ne.“
nadan bishi da kallo nace “Me yasa ka hana a bamu y‘ar aiki da zata taimaka mana, alhalin sanin kanka ne ba abnd zan iya yi.
Yayi saurin girgiza kai yace “babu bukatar wani ya shigo ckn rayuwarmu ya taimaka mana mu zamu taimaki rayuwarmu da kanmu kuma mu tafiyar da ita yadda muke so, zamuyi zama irin wanda ba‘a taba yin irinsa ba.
Na tbbt Allah daya haliccemu zai taimakemu.“ “girki, goge-goge, share-share, wanke-wanke duk waye zaiyi wadannan ayyukan??
Na tambaya ina dubansa.
ya mayar min da amsa da cewa “duk nine.“
Idanuna sukayi saurin tafiya yawo sbd AL‘AJABI!!!!!
kai kuma??
Naka aikin kuma fa ko shikenan a gida zakayita zama??
“A‘A! aikina yana nan amma bazai shafi wannan ba.“ Wasu sababbin hawaye FIL suka sulalo min.
Lallai bana jin za‘a samu mu2m irinka duk duniya!! ka sarayar da hakkinka da duk wani ango ke buri idan yayi aure sannan ka dauki alhakin aiki mafi girma akanka duk sbd ni.
Ina rokon Allah ya kawo sababin da nima zan nuna maka HALACCIN da kayimin duk da nasan zaiyi wuya nayi maka irin abnd kayi min sai dai na kwatanta.“ Na kwantar da kaina bisa cinyoyinsa na fashe da kuka.
Mun dau tsawon lkc a haka dakyar faruk ya rarrashe ni na iya yin shiru, da kansa ya tashi ya zubo min abnc ya tilasta min sai da naci sosai.
Ya dauke plask din da sauran kayan ya mayar dasu wajensu ya tako a hankali yace “To kinga yanzu lkcn kuka ya wuce ki kwanta kiyi barci isashshe kada kiji komai a gdn masoyinki FARUK kike..
yakai karshen maganar dai-dai sanda ya zauna a dan karamin tebirin dake gefen gadon, nabishi da kallo har yanzu hawayen idona basu kafe ba saima kara gudu da sukeyi.
Na dubeshi nace “amma wannan rana tazo mana ba yadda yakamata tazo ba, me yasa ma haka zata faru??...“
Faruk ya dan kauda kai ya dawo ya dubeni yace “ki bari!! zakiyi sabo fa! idan kika ce me yasa, kai tsaye Allah kenan fa kike tambaya.
Haka Allah ya kadarta mana koda a haka zamu tafi har mu2wa ni bani da kaico, kada ki karya zuciyarki da yawa duk wanda yasanki yasanki akan dakakkiyar zuciya me zai hana ki dawo ki cgb da zama a haka??“
Na girgiza kaina nace “zaiyi wuya koda zai yiwu badai a ynz ba.“
Ya bini da dogon kll yadan zunburo baki yace “Zamu bata idan baki daina kuka ba.“
Na goge hawayen idanuna.
Yace “yauwa ko kefa??
Sai ki kwanta kiyi barci ki samu isashshen hutu kinji??
Na gyada kai kawai nabi gadon na kwanta nace “kai kuma ina zaka??“
Zanyo alwala nazo nayita sallah na godiya ga ubangijina daya bani ke.
Zan bika muyi tare.
Na fada ina dubansa.
Ya girgiza kai yace “A‘A my amarya aike kina da lalura barci shine mafi dacewa a gareki a yanzu.“
Ka daina kirana da amarya sbd lalura ta hana na amsa wannan sunan, ban kuma san sanda zata barni na warke harna amsa sunan ba.
Na fada.
Yayi saurin cewa “manta da wannan“ ya jawo bargo ya lullubeni har zuwa wuyana yace “kiyi nutsatstsen barci da safe zaki fada min kalar mafarkin da kikai.“
Yakai maganar murmushi na tashi daga fskrsa, fuskata ta fadada da murmushi nima na gyada kai kawai.
Ya juya ya dauro alwala akan idona ya fara sallah sautin kara2n da yake yi yana ratsa kunnuwana har barci ya kwashe ni.
*WASHE GARI da asuba faruk ya tasheni nayi sallah a zaune kmr yadda na saba yi barci na koma sbd akwai shi a idona sosai.
Misalin 8:15 na safe faruk ya tasheni a karo na biyu, cak ya daukeni ya dôrani bisa kekena ya seta kafafuna a matokarar keken dake kasa ya 2rani a hankali muna hira kai tsaye muka fito falo ya wuce dani gefe falon inda aka tanadi wani faffadan tebirin cin abinci zagaye kujeru ya 2rani har izuwa gbn kayataccen tebirin ina zaune bisa keken da aka halitta sbd irinmu.
faruk yace “yauwa kinga ke y‘ar baiwa ce ba ruwanki da kujera, ni kuwa bin tebirin kawai nake da kll zagaye yake da abinci kala-kala irinna breakfast kuma dafawar yanzu sai tiriri suke kana gani kasan yanzu aka hada su.
ckn AL‘AJABI nace “waye ya dafa duk wannan abubuwan??“
Yayi murmushi yace “Nine!! kina mamakine??“
Ya fada dai-dai sanda ya ajiye kofin tea a gefena tare da cewa “bismillah! sai ki fara da duk wanda kike so.“
A ido kawai nasan duk abinda ya dafa zasuyi dadi ma2ka sanda nakai bakina dazan hadiye har wani lumshe ido nayi, na bishi da kll nace “a jami‘o‘in koyon girki wacce kayi??“
Yayi dariya yace “A jami‘ar ummina mana, 2n ina yaro tare muke yin komai gashi kuma yanzu hakan ya fara amfani.“
Haka dai muka cgb da cin abincin ckn nishadi muna hira har muka gama, faruk ya fara shiga dani loko da sakon na gidan.
*Haka dai muka cgb da rayuwa har hu2n faruk ya kare ya koma wajen aiki sai ya zamana kafin ya tafi duk abinda zan bukata ya aje minshi bisa faffadan tebirin dake gaf da makeken gadona.
Abinci, ruwa, magungunana da komai suna kusa dani sai kuma uwa-uba wayata wadda da ita muke tare a ko yaushe.
kllm sai ya dawo ya koma, da la‘asar tayi kuma ya dawo gida ya shiga kitchen da kansa ya dafa mana abinci.
A wasu lktn tare muke shiga ina zaune bisa dan kekena muna hira har mu gama hada abnd muke so, rayuwarmu abin sha‘awa ckn sauki muke gudanar da ita cike da walwala da aminci wanda hakan ya samu ne ta silar tsantsar SOYAYYA ta gsky.
Anya kuwa...za daure..
Barka da rana..!