Isata gida keda wuya na ketawa ma‘aikatan gdnmu rashin mu2ncin dana saba harma sai dana mari me baiwa fulawowi ruwa sbd yayi sakacin watsa min ruwa duk kuwa da cewa ba yana sane bane, kai tsaye dakina na wuce nayi wanka naci abinci na jawo laptop dina hau aikin dana saba.
Bayan kwanaki biyu da haduwa da saurayinnan da ko sunansa ban sani ba ina zaune a bakin harabar makarantar tamu a wannan karon wayata ce kawai a hannuna sakamakôn laptop dina tana hannun mufida, zuwa da wurin da nayi ne yasa a gabana dai-daikun dalibai ke isowa suna wucewa ba ruwana dasu sai dai su wuce.
wasu lktn zakaga daliban na zuwa ne a group-group kamar yadda al‘adar rayuwar makaranta take.
Ana cikin haka ne group din da suka fi kowanne shahara a makarantar suka zo wucewa ai kuwa caraf idon saurayinnan a kaina ya dakata tare da duban na kusa dashi yace “nazir“.
Wanda aka kira da sunan nazir din yace “na‘am leader.“
wuce min da jakar nan na hango mu2niyar, nazir din ya amshi jakar ya kallo inda nake tare da cewa “wlh leader kabi a hankali yarinyar nan big class ce zaka sha mari fa inkai wasa.“
ya rike kugu tare da cewa “Ta mareni?? haba dallah sai kace a zamanin jahiliyya?? kudai ku tsaya kusha kallo.
Ya juyo ya doso inda nake, dirar daddadar muryarsa kawai naji a kunnena da fadin “Amincin Allah ya tbbta a gareki ma‘abociyar son kadaici da hutawa“.
Har ga Allah wani sanyi naji a raina amma da yake ni din ce kawai sai kauda kai kamar bansan me yace ba.
ya sake yin murmushi yace “kauda kanki lfy tauraruwa me haske“, na sake hade rai na kalli kasa.
woww!! gsky ke daban ce ban taba ganin wanda fushi keyiwa kyau ba sai ke.
Ya fada yana kallona. Na cije lebena na dubeshi zanyi magana yayi saurin cewa “ina ma kiyi magana a ckn fushi daba karamin kwarjini zaki kara ba.“
Na dan rufe idona a raina nace “BALA‘I“ na kara hade rai nace “kaga nifa ba shashasha bace da za‘a zo har inda nake a cikani da suru2 idan ina son zama a wuri me hayaniya mezai kawoni nan?
murmushinsa wanda adon fuskarsa ne ya karu yace “gani nayi zaman kadaici bashi da dadi shine nazo na debe miki kewa gashi kuma nayi nasara 2nda a baya bakinki a rufe yake yanzu kuma gashi yana motsi, na girgiza kai nace “to bana so idan wurin ne yayi maka zan iya tashi nabar maka“.
Ya mike tare da cewa “ kinfi karfin kina waje ace wani ya tasheki amma ki sani babu wata halitta dake iya rayuwa ita kadai dole tana bukatar mataimaki Allah ne kawai yake guda daya baya bukatar abokin tarayya amma bamu y‘an adam masu rauni ba, yaja da baya tare da dago min hannu yace “sai anjima“.
Na bishi da kallo ba karya fa gayen ya hadu wlh, tun daga zubinsa har ya zuwa kalamansa da halayensa ababan birgewa ne.
Ban jima a zaune ba na tashi na shiga class ko break ban fito ba sai da aka tashi, abinda ya kara bata min rai sai dana shafe min2na 15 da tashi direba na bai iso ba bare mu tafi na zauna bisa dandamalin dana saba zama na zaro wayata na kira direban yana dagawa na balbaleshi da fada duk da hakurin da yake bani sai da nayi na gaji sannan na kashe wayar hade da doka tsaki, Allah ya wuci zuciyarki yake tauraruwa me kyalkyali, na dago kaina muka hada ido da saurayinnan na bata rai naja tsaki na kauda kai.
Yace “ina bbr aminiyar taki ne na ganki ke kadai??“
sakanni talatin na dauka sannan nace “ Ta tafi koyo sallama “
Ya saki murmushi yace “sorry i took the correction“
Amma me yasa duk ranar da ake kwallawa baki nemi inuwa kin zauna ba kika zabi zama a ckn rana??“
Cikin fusata nace “ina ruwanka? wai kai wanne irin mu2m ne?“
Yace “bakar fata, musulmi kuma bahaushe, bana fatan kice na takura miki don haka kinga tafiyata, sai anjima.“
MAYE!!!!!! na fada a raina, dai-dai lkcnne direbana ya karaso mufida ma ta fito kai tsaye muka nufo gida, inata zabgawa direban ruwan bala‘i ta inda na shiga ba tanan nake fita ba.
******* Kwanaki uku da faruwar haka misalin 11:30am mun fito break da yake ban karya ba naja mufida muka shiga restaurant aka kawo mana abinci muka fara ci, bamu dauki tsawon lkc ba muka gama.
Na kira dan matashin bakin saurayin daya kawo mana abincin nace “yauwa nawa ne kudinku??“ yayi yar gajeriyar dariya yace “No ai basai kun biya ba“.
Na zabga masa harara nace “kai nifa bana wasa da yaro nawa ne kudinku aka ce??“ nakai karshen maganar cikin tsawa.
ya girgiza kai yace “An riga an biya muku fa“, na bishi da kallo nace “kai kada ka raina min hankali kaga nayi kama da matsiyaciyar da za‘a siya wa abinci?? To ai ni ko gaba daya restaurant din naku nagadama ina iya siya bare abincin mu2m biyu kada ka batamin rai ka batawa kanka, nawa ne kudinku??“
fuskar saurayin ta canja yace “haramun ne a aikina na karbi kudin mtm biyu akan abu daya amma idan kina musu ga wanda ya biya muku can, nabi hannunsa izuwa inda yayi min nuni caraf idanuna suka dira akan saurayinnan me lakabin leader na dauke kai tare da runtse idanuna ckn takaici, shit!!! wai wannan wane irin mtm ne?? Na tambayi kaina naja jakata dake ajiye akan tebirin dake gabana na doshi inda yake. Ko sanin nazo inda yake baiyi ba na tsaya a kansa nace “mallam abin naka kuma yana neman yayi yawa fa, daga ina dan saurararka kuma sai raini ya shiga??
cikin rashin fahimta ya ajiye kofin juice dake hannunsa ya dago kai yace “ raini kuma?? me ya faru??“ Na dan harareshi nace “idan ba haka ba meye na biya min kudin abu mafi sauki da kowa ke iya siya irin abinci??“
Fuskarsa tayi saurin canjawa zuwa murmushi yace “ wlh na zaci wani gingimemen laifi na aikatawa sarauniyar matan wannan karnin, ashe ma ba wani abu bane “ Na bishi da kallo nace “ba wani abu ba?? kayi min wulakanci irin wannan kace ba komai bane??“, ya juyar da p-cap din dake kansa izuwa baya yace “Ni banyi miki wulakanci ba a wajena kyautatawa nayi miki sbd kin cncnci fin haka a wurina bawai nayi hakan bane don kankantar dake domin kin wuce haka, kuma ni a wurina kyauta ai itace mafi girman karramawa!!
Ni kuma a wurina itace mafi girman kankantarwa, nawa ka basu na biyaka??
Na fada dai-dai sanda na zaro wata yar karamar jaka daga bbr jakata.
Ya dago da sauri tare da bina da wani irin kallo tamkar bai fahimci abinda na fada ba yayi saurin girgiza kai yace “baki yi kama da wadda zata maida hannun kyauta baya ba sbd nasan kinsan hakan bai dace ba, abinda nake so ki gane shine don an baki abu kin amsa ba yana nufin baki fi karfin abin bane.“
Na tabe baki nace “well!! naji 2nda kai kagadama kaga zaka iya amma ka sani idan wai kayimin haka ne don naji dadi to banji ba, kuma bazan gode maka ba sbd bani na saka ba.“
yayi saurin sakin murmushi yace “dama badon ki gode min nayi miki sbd ba nema kikai ba martabarki ce kawai takai ayi miki abinda yafi haka.“
Na juya tare da cewa “kai dai ka jiyo“.
Sai dai a zuciyata ba karamin dadin kalamansa naji ba sbd ni mtm ce me son a zigani.
Na nufi inda mufida take wacce har yanzu ke zaune kawai tana kllnmu ta mike kai tsaye muka nufi class muka cgb da lacca.
*** Wato 2nda nake a duniya ban taba ganin mu2m irin saurayinnan ba, ya hadu ta ko‘ina kuma ba shakka yasan abinda yake yi kalamansa kawai ke tbbr da haka, abinda nayi iya kokarina na gano na kasa shine me yasa yake burgeni? me yasa yake da kwarjini a idona? me yasa bana iya wulakantashi kamar sauran mutane??? tambayoyin dana kasa bawa kaina amsarsu kenan ***.
Bayan kwanaki uku da faruwar haka, na shiga inda ban taba shiga ba library don duba wani littafi me danake ma2kar bukatarsa da wuri, al‘adata ban damu na duba littafi a library ba domin waya kawai zanyi a kawo min shima wannan din don ina bukatarsa da gaggawa ne.
Ni kadai ce a cikin wajen hakan yasa nake neman nawa ckn kwanciyar hankali, motsin shigowar da naji yasa nayi saurin dago kai muka hada ido dashi nayi saurin dauke kai daga kllnsa, yadan tsaya yana kllna lkc guda ya tako tare da cewa “Amincin Allah a gareki ya tauraruwar da haskenta baya disashewa“, ko kllnsa banyi ba naci gaba da abinda nakeyi, ya tako a hankali izuwa nesa kadan dani yace “nayi sa‘a kenan yau zan taya sarauniyar mata bincike me kike nema ne??“
ko kllnsa banyi ba nace “ Idon matambayi “.
Hmmmm lemme stop here kar mucika cikawa kuce yayi yawa..!
SABAHUL KHAIR..