Gwamnan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya ce akwai man fetur mai yawan gaske a shimfide a yankin arewacin kasar.
A wata hira da ya yi da BBC, Barista Muhammad ya ce idan dai har za a samu mai a makwabtan Najeriya kamar Jamhuriyar Nijar da Chadi, to bai ga dalilin da zai sa a ce babu man a arewacin kasar ba.
Ya kara da cewa yanzu haka yana tattaunawa da katafaren kamfanin nan na man fetur na kasar Rasha watau Gasprom domin duba yadda za a fara aikin man fetur a yankin.
Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin arewa maso gabashin Nijeriya da ake kyautata zaton suna da arzikin man fetur a karkashin kasa.
A halin yanzu dai tattalin arzikin Nijeriya ya dogara ne kusan kacokan a kan albarkatun man fetur.
Sai dai wannan yunkurin na gwamnonin arewacin Najeriya na zuwa ne a dai-dai lokacin da farashin man yake ci gaba da faduwa warwas a kasuwar duniya.
Title :
Akwai man fetur dankam a arewacin Nigeria
Description : Gwamnan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya ce akwai man fetur mai yawan gaske a shimfide a yankin...
Rating :
5