Mutuwar dan takarar gwamna na jihar Kogi ya jaza maganganu akan yadda za’a gudanar da zaben. Dan takarar APC ya samu kuri’u 240, 867 inda yake kokarin zama gwamnan jihar karo ba 3 bayan da yayi kokari sau 6. Abokin hamayyar sa Idris Wada ya samu 199,514. Amma ba’a bayyana shi a matsayin Gwamna ba Saboda akwai Inda ba’ayi zabe ba Inda keda kuri’u 49,000.
Kundun tsarin mulkin Najeriya bai fayyace Akan mutuwar dan takarar zabe ba. Kundun tsarin dokokin zabe Na 36 yace: “Idan an maida takardun neman tsayawa takara amma ba’a fara zabe ba dan takara ya mutu, kwamishina zabe ko kuma shugaban zabe idan ya gamsu da mutuwar dan takarar da kuma hukumar zabe Sai ya bada wani lokaci ayi zabe cikin kwanaki 14.
“Jerin sunayen masu zabe wanda za’ayi amfani dashi domin ayi zaben da aka daga shi zaya zama rajista Wanda aka amince da Ita Wanda ada za’ayi amfani da Ita kafin a daga zaben.”
Wanna dai ita kadai ce maganar da kundun tsarin dokokin zabe yayi. Lauyoyi da yawa sun maganta akan cewa akwai gibi da yawa a dokokin zaben Najeriya Wadanda lokaci yayi Yanzu da ya kamata ace an gyara su domin kaucema rudani.
Title :
Abunda Dokar Zabe Tace Akan Mutuwar Audu
Description : Mutuwar dan takarar gwamna na jihar Kogi ya jaza maganganu akan yadda za’a gudanar da zaben. Dan takarar APC ya samu kuri’u 240, 867 inda y...
Rating :
5