Ya kai dan uwana ka sani dabi.ar ýa mace kamar iska ce da take kalawa a hankali idan ka furtawa ýa mace kalma mai kyau to zaka tashi a tutocin soyayyarta,
Idan kuma kai mata rauni ko da kalma daya zasu rusa soyayyarka,
Lallai ne ana son namiji ka siffantu da wadannan siffofin domin ka sami cikakkiyar soyayya da kauna a wurin matarka,
1] KA MUTUNTA MATARKA:
Ka nuna mata kai da ita duk abu daya ne ba bambanci kana da buri itama tana da shi, kana da sha.awa itama haka,
Lallai ne ka mutunta ta, kamar yanda kai ma kake son ta girmamaka.
Manzon Allah S.A.W yana cewa.
Duk wanda ya sami mace to ya girmamata,
don haka kuskure ne da jahilci a hanawa mace ýancin fadar ra.ayinta ko neman shawararta, ko tattaunawa da ita a cikin wasu al.amura. Kar a maida ita kamar kayan wasan yara, ba a nemanta sai za a bukaceta, duk wanda yake wa mace irin wannan dabi.ar tabbas zai rasa soyayyarsa a cikin zuciyar matarsa,
2]KA ZAMA ABOKIN MATARKA: ma.ana kayi mu.amala da ita ta kowane bangare kada ka bar wata kafa a bude ta yanda zata fahimci baka damu da ita a wannan bangarenba, lallai ne ka zama mai debe mata kewa ta kowane bangare, mai saka ta farin ciki da nutsuwa,
3] KARKA ZAMO MAI CIN DUNDUNIYAR TA,
ma.ana kai a kullum burinka so kake kaga tayi laifi kai kuma ka bude mata wuta A.A! Ka zama tamkar mai koya mata yanda zatayi rayuwa, inda ta kauce sai ka saitata. Domin a kullum ita mai raunin tunanice in har ta aikata marar kyau, to kada ka saka mata da marar kyau, A.A! Sai ka sai tata da mafi kyau, tabbas zaka dace da soyayyarta.
4] LALLAI NE KA ZAMA MAI JURE WOWTAR ÝA MACE: ka zama mai kyautata zamantakewarka gareta ka saki fuskarka gareta, ta yanda ba zata rainaka ba, ma.ana kada kayi sakacin da zata iya raina ka.
5] KA ZAMA MAI TAI MAKONTA. Yayin data shiga tsanani, kada kayi banza da ita,
6] Ka zama mai dece mata kewa yayinda take ita kadai.
7] Ka zama shimfidar kwanciyarta yayin da ta bukaci barci,
8] kar ka nuna mata kosawa ko ka fara gajiya da ita,
9] In ta kamu da cuta karka shareta, kayi iya kokari wajen nema mata waraka.
10] In zaka shigo mata gida to kashigo da murmushi kuma in zaka ita ka fita da murmushi hmmmmm.
11] Karka tozartata yayin data nemi wata bukata a gareka, kuma in har zakayi mata alhairi, to kada ayi mata mafi karanci.
12] Idan tayi abu mai kyau ka yabeta ka gode mata.
13] Idan tayi kuskure ka yafe mata.
14] Kar ka yabi wata mata agabanta.
15] Ka zama mai tsafta da kwalliya.
16] Karka zama mai yawan mita da dawo da kuskuren da ya wuce.
17] Ka zama mai kishin iyalinka kar ka zama DAYYUS"
18] ka zama mai girmama yan uwanta musamman iyayenta.
19] Ka zamo mai kiyaye sirrinta kada ka zama mai yada kuskurenta a cikin daidaikun jama.a
20] Kar ka zama mai son kai ka girmama kanka ita kuma ka wulakantata......
Title :
Abu Ashirin Da Mata Ke So
Description : Ya kai dan uwana ka sani dabi.ar ýa mace kamar iska ce da take kalawa a hankali idan ka furtawa ýa mace kalma mai kyau to zaka tashi a tutoc...
Rating :
5