Masana harkar lafiya a Najeriya sun nuna damuwa game
da yawan karuwar cutar yoyon fitsari a tsakanin matan
kasar.
Masana sun ce a duk shekara ana samun mata wadanda
suke kamuwa da cutar dubu 12, amma dubu biyar ne
kawai ake iya yi wa magani.
Kwararrun sun bayyana haka ne a wajen wani taro da
shirin Fistula Care da ke karkashin hukumar tallafawa
kasashen duniya ta Amurka wato USAID ta shirya a Kano
kan matsalar ta yoyon fitsari.
Wani kwararren likitan mata a Kano Dr. Habibu Sadauki
ya shaidawa BBC cewa a Nigeria mata dubu 150 zuwa
dubu 200 ne wadanda ke fama da wannan cutar.
Likitan ya kuma ba da shawarar zuwa asibiti a lokacin
haihuwa.
Title :
Yoyon fitsari na karuwa a Nigeria
Description : Masana harkar lafiya a Najeriya sun nuna damuwa game da yawan karuwar cutar yoyon fitsari a tsakanin matan kasar. Masana sun ce a duk she...
Rating :
5