TAMBAYA TA 1759
********************
Assalamu alaikum, Allah ya karawa Malam sani mai amfani tare da rayuwa mai albarka. Don Allah malam inaso a taimka a karba min wadannan tambayoyin nawa kamar haka:
1. Idan mutum zai yi aure a musulunci ya halatta yayi bincike akan matar da zai aura, to a nan wadanne irin mutane ne ya kamata ya yiwa tambayoyin sa akanta? Kuma menene abu mafi muhimmanci da ya kamata ya bincika game da ita?
2. Mutum ne dan makaranta aka sanya sunansa a cikin voucher ta local gov't duk wata yake karbar wani ihsani domin ya taimaki kansa dashi, amma fa baya fita aiki....to menene matsayin wadannan kudaden a addinin musulunci?
Allah ya sakawa malam da mafificin alkhairinsa, ameen
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. Eh lallai ya halatta mutum yayi bincike kafin aure. Kuma Mafificin abinda mutum zai bincika shine Tarbiyyar Matar da zai aura, da kuma yanayin halayyar Iyayenta.
Daga cikin Magabata na kwarai, Sayyiduna Anas bn Malik (rta) ya kasance yakan tura mahaifiyarsa Ummu Sulaym taje tayi masa bincike akan matar da zai aura.
Don haka zaka iya sanya wata 'yar uwarka tayi maka bincike, ko kuma abokinka ya bincika maka. Ko kuma Ka tambayi Limamin Unguwarsu akan halayyar mutanen gidan.
Kuma shi binciken nan ana yinsa ne tun kafin a fara tuntubar ita wacce ake so din.
2. Shi kuwa wannan Dan Makaranta din, in dai ya riga ya nemi izinin Ma'aikatar da yake aiki, kuma ya tafi neman Qarin ilimi ne, to shikenan wannan babu laifi.
Amma idan an shirya abun ne ta fuskar ha'inci da almundahana, to wannan bai halatta ba. Misali kamar yadda wasu Jami'an Gwamnati suke yi awannan zamanin, Sukan dauki takardun daukar aiki (Offer) su rubuta da sunan yaransu Qanana.
Zasu ci gaba da cirewa kudin albashin ba tare da ana yin aikin ba. To kaga wannan duk haramun ne. Ya kamata masu yinsa su tuba.
WALLAHU A'ALAM.