SHINKAFA DA KWAKWA
• Shinkafa.
• Nama.
• koren wake.
• kayan miya amma banda tumatir.
• kwa-kwa.
• karas.
• maggi,gishiri da sauran su.
Da farko zaki tafasa shinkafan ki,ki wanke ki aje a gefe.sai ki zuba mai a tukunya ki zuba namanki a ciki da maggi da gishiri da kayan kamshi ki rufe yadan dahu,sai ki dauko kwakwanki ki kankare bayan ki markada ki tace sai ki zuba ruwan a kan naman nan dake kan wuta ki kara su maggi da su albasa da tattasai da koren waken ki da lawashi,ki rufe ya tafasa waken ya dahu,saiki zuba shinkafan da karas din da kika yayyan ka harya tsotse.ki gwada dan jiyama naci Hmmm akwai dadi.
admin Sadia tafida