KOSAN SEMOVITA
________________
~Semovita
~Kwai
~Nama ko kifi
~Albasa
~Attaruhu
~Man gyada
~Maggi & gishiri
~Yeast
~Curry
zaki kwaba semovitanki da yeas kamar zakiyi fanke kibarshi ya tashi,saiki jajjaga albasa attaru ki aje gefe,san nan ki daka dafaffan namanki ko kifi ki hada dasu attaruhu ki ajiye,ki dafa kwai ki yayyanka sannan ki fasa wani ki ajiye,ki dauko kullun nan ki duba ko ya ttashi idan ya tashi sai ki zuba wadannan kayan duka a ciki tare da curry maggi da gishiri ki juya sosai,
sai ki dora mai a kan wuta kamar zakiyi kosai ki dinga diba kina zubawa idan da wutama zakiga yana juyawa dakansa ba sai kin juyaba,sai a kwashe za a iyaci da kunun shinkafa ko na shi semovita din ko kuma wanda kike so,anjima in Allah yaso zamu kawo daya daga ciki.
• yar uwarku Asma'u Garba