Yan sanda a jihar Kano da ke arewacin Nigeria sun ce sun soma gudanar da bincike dangane da zargin yi wa wasu yara maza fyade a wata makarantar kwana mai zaman kanta da ke birnin Kano.
Daya daga cikin daliban makarantar Hassan Gwarzo, wanda ya yi zargin an yi kokarin yi masa fyade ya ce "Sau biyu aka kai min hari. Da farko sun yaye min gidan sauro (net) na, sai suka rufe min baki, suka cire min wando, da na yi ihu sai suka gudu."
Sai dai hukumomin makarantar da ake zargin lamarin ya afku sun ce, an yi yunkuri ne na yin lalata da yaran, amma ba a kai ga yi musu fyaden ba, kuma sun dauki matakai na kawo karshen irin wannan al’amari.
Iyayen yaran da al’amarin ya shafa sun bukaci a dauki mataki domin hukunta wadanda suka ce, "suna lalata musu yara".
Mai makarantar, Farfesa Ibrahim Ayagi ya ce "Wannan abu bai afku ba. Abin da muka sani shi ne cewar yara uku sun kai kara wajen shugaban makarantar cewa wasu sun taba wandonsu. Daya daga cikinsu ya ce an shafa wandonsa, sannan aka rufe masa baki. A kokarin yin motsi kuma sai ya gurde bayansa."
Farfesa Ayagi ya kara da cewa "Ba a kyale 'yan wasu ajin su shiga wurin kwanan 'yan wasu ajin.Sannan da dare akwai jami'in tsaro a kowanne daki,"
Wasu dalibai a makarantar sun yi zargin cewa an dade irin wannan al’amarin ya na afkuwa, amma BBC ba ta da wata hanyar tabbatar da wannan zargin.
Bbchausa
Title :
'Zargin yi wa yara maza fyade a Kano'
Description : Yan sanda a jihar Kano da ke arewacin Nigeria sun ce sun soma gudanar da bincike dangane da zargin yi wa wasu yara maza fyade a wata makaran...
Rating :
5