A Jamhuriyar Nijar mayakan Boko Haram sun hallaka mutane goma sha hudu tare da kona garin Ala da ke yankin Diffa a harin da suka kai a daren talata zuwa wayewar garin laraba.
Shaidu sun ce a lokacin wannan hari, mayakan Boko Haram sun kwashi kayayyaki da dukiyoyin al’umma kafin daga bisani sun cinna wa gidajen jama’a wuta.
Jahar Diffa da ke kan iyaka da Najeriya na fuskantar barazanar tsaro sakamakon hare-haren wannan kungiya wadda ta samo asali daga Najeriya, al’amarin da yanzu haka ya janyo asarar rayuka da dukiya.
Title :
Yan Boko Haram sun kashe mutane 14 a Diffa
Description : A Jamhuriyar Nijar mayakan Boko Haram sun hallaka mutane goma sha hudu tare da kona garin Ala da ke yankin Diffa a harin da suka kai a daren...
Rating :
5