A kasar Kamaru, mayakan Boko Haram sun kama garin Kerewa da ke kusa da iyakar kasar da Najeriya, bayan da suka yi nasarar fatattakar jami’an tsaron kasar.
Wannan ne dai karo na farko a cikin ‘yan watannin baya-bayan nan da mayakan na Boko Haram suka yi nasarar kwace wani yanki a cikin Kamaru, kasar da ke taimaka wa Najeriya a yakin da take da magoya bayan wannan kungiya.
Kerewa dai gari ne mai kunshe da mutane sama da dubu 50, kuma wasu majiyoyi sun ce an samu asarar rayukan fararen hula da jami’an tsaron kasar da dama a lokacin da ‘yan bindigar ke kokarin kama garin.
Title :
Yan Boko Haram sun kama garin Kerewa na arewacin Kamaru
Description : A kasar Kamaru, mayakan Boko Haram sun kama garin Kerewa da ke kusa da iyakar kasar da Najeriya, bayan da suka yi nasarar fatattakar jami’an...
Rating :
5