Yayin da ake ta kiraye-kirayen a taimaka ma
jami'an tsaron Najeriya a yaki da Boko Haram,
rundunar sojin Najeriya ta ce dakura 'yan Boko
Haram da aka yi ya sa su ke ta kokarin nuna
cewa har yanzu su na da karfi, ta wajen kai hare-
hare.
Hafsan Hafsoshin Sojojin
Najeriya Manjo-Janar Tukur Yusuf Brutai ya ce
wutar da ‘yan Boko Haram ke sha ce ta sa su shiga
kai hare-haren kunar bakin wake don su nuna har
yanzu sun a nan, alhalin kuwa tasu ta kusa
karewa.
Don haka wakiliyarmu a shiyyar Filato Zainab
Babaji ta tuntubi wani mai sharhi kan al’amuran
yau da kullum mai suna Dan Manjang don jin
yadda yak e ganin al’amuran tsaro a Najeriya a
yanzu sai ya yi nuni da kudurin Janar Burutai na
cimma wa’adin da Shugaba kasa a ba sojojin
Najeriya. To amma y ace kodayake akwai fatan a
gama da Boko Haram cikin wa’adin na Shugaban
kasa, da wuya a iya cimma wannan wa’adin. Y ace
ai ba a Naijeriya kawai Boko Haram su ke ba.
Game da cigaba da kai hare-haren da ‘yan Boko
Haram ke yi, Manjang y ace ya kamata mutane su
gane cewa yaki da ta’addanci ba aikin gwamnati
ba ne kawai, na kowa da kowa ne. Y ace ba
jami’an gwamnati ‘yan ta’addar ke kashewa ba,
jama’a ne; kuma gashi babu yadda ‘yan ta’addar
za su shiga cikin jama’a ba tare da sanin kowa ba.
Ya ce da gwamnati da jama’a - kowa da rawar da
ya kamata taka.
Title :
“Yaki Da Boko Haram Ba Aikin
Gwamnati Ba Ne Kadai”
Description : Yayin da ake ta kiraye-kirayen a taimaka ma jami'an tsaron Najeriya a yaki da Boko Haram, rundunar sojin Najeriya ta ce dakura 'ya...
Rating :
5