BEEF FRITTERS
********************
• Nama
• filawa
• karas
• albasa
• koran tattasai
• jan tattasai
• baking powder
• magi&gishiri kori
• mai
Dafa nama ya dahu,a dakashi a turmi a yanka albasa koran tattasai da jan tattasai a kankare bayan karas sai a goga a hadasu duka a aje agefe,a tankade fulawa a kwabata da baking powder ayishi ruwa ruwa amma yafi kwabin waina kauri,a zuba magi gishiri da sauran kayan hadin a juya a rufe zuwa minti30.
a zuba mai a kasko adinga diba ana soyawa kamar za ayi kosai ana cinsa da tea ko kunun aya ko hakansa,
admn Asma'u Garba