CUS-CUS DA MIYAN KODA.
• Cus-cus
• koren wake
• kala.
Ki zuba ruwa ya tafasa idan ya tafasa sai ki zuba mangyada kadan da gishiri da kala ana sayar dashi a kasuwa,sai ki zuba koren waken ki yadan nuna,sai ki zuba cus-cus din ki juya ki bashi minti 2.karki ki cika ruwa inba haka ba ya kwabe.
MIYAN KODA
• Karas
• koda
• albasa
• tumatir
• tattasai
• mangyada
• maggi gishiri da curry.
Da farko zaki zuba mangyadan ki a wuta karki bari yai zafi sosai, sai ki zuba kodan ki da kika riga kika wanke a ciki, ki zuba albasa da maggi da gishiri da curry sai ki juya ki rufe,ki barshi idan yayi mintina ki bude ki dunga juyawa zakiga ruwa ya tsatstsafo kinsan koda nada ruwa a jikin shi ba sai kinsa ruwa ba, kita juyawa har ya dahu, sai ki kawo albasan ki mai lawashi da kika yayyanka ki zuba da kayan miyanki da kika jajjaga ki zuba, saiki kara rufewa nasu lokutan saiki dauko karas dinki da kika kankare kika yayyan ka ki zuba ki kara rufewa har karas din ya dahu tukunna sai ki sauke aci.
Admn Sadia tafida