Wata kungiya ta duniya dake karrama mutanen da suka yi fice a duniya ta girmama Farfasa Attahiru Jega tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya tare da wasu 'yan majalisun dokokin Amurka.
WASHINGTON DC —
Farfasa Jega yace babu abun da zai ce sa idai godiya ga Allah wanda ya sa ya yi shugabancin hukumar zaben Najeriya na tsawon shekaru biyar kuma ya gama da nasara har zaben 2015 ya zama abun yabo a duk fadin duniya.
Yace karramawar abun alfahari ce saboda kungiyar sananniya ce a duniya. Kungiyar ta yi suna wurin fafutikar da take yi wurin inganta harkokin zabe a duniya. Tana kuma bada karfin gwiwa na gina dimokradiya.
A kowace shekara kungiyar ta kan ba mutane uku lambobin yabo. Suna daukan biyu daga cikin majalisun Amurka daya kuma daga kowace kasa a duniya.
Nancy Polosi na cikin wadanda aka karrama. Farfasa Jega yace ya ji dadi da aka hadashi da su domin ya nuna an girmamashi sosai.
Abubuwan da suka taimaka aka samu nasarar zaben 2015 a Najeriya suna da yawa. Amma Farfasa Jega yace bayan an gama zaben 2011 sun yi nazari da bincike akan kurakurai da abubuwan da suka yi da kyau. Sun yi shekaru biyar suna gyara.
Abubuwa da suka taimaka sun hada da bukatar mutane na son a kawo gyara a sha'anin zabe. Abu na biyu shi ne yin anfani da naurar dake karanta katin zabe. Abu na uku shi ne katin zaben wanda ya kunshi hoto da yatsu da dai sauransu. Wadannan sun taimaka wurin rage magudi.
Title :
Wata Kungiyar Duniya Ta Karrama Farfasa Attahiru Jega
Description : Wata kungiya ta duniya dake karrama mutanen da suka yi fice a duniya ta girmama Farfasa Attahiru Jega tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya...
Rating :
5