Babbar kotun Majaristare ta biyu da ke cikin garin Katsina ta ingiza keyar dattijo mai shekaru 60, Dikko Sanin a garin ’Yar Taura zuwa gidan maza bisa zargin yi wa jikarsa ciki.
Alkalin kotun mai shari’a Abdu Ladan bayar da umurnin ne, bayan sauraren karar da Sufeto Abas Hamza ya gabatar inda ake zargin tsohon da yi wa jikarsa ’yar shekara 14 ciki. Laifin, wanda ya ce ya saba wa kashi na 283 na kundin laifuffuka da hukunce-hukuncensu na finalkod.
Kamar yadda mai gabatar da karar ya shaida wa kotu, Dikko na amfani da dabarar aiken matarsa ne yadda zai samu kadaicewa da jikar, wanda asirinsu ya tonu ne ta samun ciki da jikar ta yi.
Alkaki ya dage sauraren wannan kara har zuwa 11 ga watan Nuwanban bana, bayan ya bayar da umarnin a tasa keyar dattijon zuwa gidan yari.
Ita ma babbar kotun Majestare ta 6, a ranar Labarar makon da ya gabata ta bayar da umarnin iza keyar wani matashin mai shekaru 29 zuwa gidan maza, bisa tuhumarsa da ake yi na yi wa ’yar uwarsa mai shekaru 11 fyade.
dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Hashimu Musa ya shaida wa mai shari’a Nafisa Lawal Bagiwa cewa, a wani lokaci ne ’yan sanda da ka Malumfashi suka kawo Mudassiru Abdullahi Malumfashi mai shekaru 29 a hedkwatar ’yansanda da ke Katsina, bisa tuhumarsa da ake yi na yi wa yarinyar fyade; laifin da ya saba wa sashe na 283 na dokar finalkod.
Mai shari’ar ta bayar da umarnin kai Mudassiru gidan maza har sai ranar 17 ga watan Nuwamban bana, domin ci gaba da sauraren wannan kara.
Kazalika, shi ma dattijo dan shekara 65 mai suna Ibrahim Salisu Runjin Baushe da ke cikin karamar Hukumar Bindawa, mai Shari’a Nafisa Lawal Bagiwa ta bayar da umarnin kai shi gidan maza har zuwa 12 ga Nuwamban bana, bayan sauraren karar da dan sanda Sufeto Hashimu Musa ya gabatar na tuhumar dattijon da yi wa wata yarinya mai shekaru 12 fyade.
Shi kuwa daya matashin mai suna Babangida Ya’u da ke unguwar Rahamawa a cikin garin na Katsina, babbar kotun ta dage sauraren karar da aka shigar a gabanta na tuhumarsa da yi wa wata yarinya mai shekaru uku da rabi fyade har zuwa 24/11/2015. karar wadda aka sake ambata ta a wannan kotu, mai shari’ar ta tura ta zuwa ma’aikatar shari’a ta jiha domin bayar da shawara, yayin da ta bar Babangida da ya ci gaba da zama a karkashin belin da aka zo mata da shi yana ciki har zuwa ranar da aka tsaida don ci gaba da sauraren karar.
Title :
Wani Tsohon Da Shekara 60 Yayi wa Jikarsa Ciki
Description : Babbar kotun Majaristare ta biyu da ke cikin garin Katsina ta ingiza keyar dattijo mai shekaru 60, Dikko Sanin a garin ’Yar Taura zuwa gidan...
Rating :
5