Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gwagwarwa cikin Jihar Kano, ta gurfanar da wata mata mai suna Fatima Muhamamd bisa zarginta da laifin lakada wa matar tsohon mijinta dukan kawo wuka.
Mijin matar mai suna Ahmad Lawan ya shaida wa kotu cewa tsohuwar matar tasa ta je har gidansa inda ta sami matarsa ta yi mata dukan kawo wuka ba tare da laifin tsaye ko na zaune ba.
Da take kare kanta, Fatima ta bayyana wa kotu cewa ta yi hakan ne sakamkon dukan da tsohon mijin nata ya yi mata lokacin da ta je gidan yayansa ta dauko ’ya’yansu da nufin ta rike su. “Bayan na je gidan yayansa na dauko ’ya’yanmu da suke can sai ya ji labari shi ne ya zo muka yi rigima da shi har ya doke ni. Haka ya sa ni ma na je gidansa na rama a kan matarsa. Sai dai ina neman afuwar kotu bisa abin da na aikata, wanda bacin rai ne ya sa na aikata.” Inji ta.
Sai dai Malam Ahmad Lawan ya musanta ikirarin tsohuwar matarsa tasa, inda ya bayyana cewa shi a iya saninsa babu abin da ya shiga tsakaninsa da tsohuwar matar tasa, ballantana har ya kai hannu ya doke ta.
Ita ma a nata bangaren, matar da aka doka din mai sun Maryam Ahmad ta nemi kotu ta shiga tsakaninta da tsohuwar matar mijin nata, don guje wa abin da ya faru a nan gaba.
Alkalin kotun Mai, Shari’a Muhamamd Abba ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 26 ga wata tare da sanya matar da ake zargi a hannun beli.
Title :
Ta yi wa kishiyarta dukan kawo wuka
Description : Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gwagwarwa cikin Jihar Kano, ta gurfanar da wata mata mai suna Fatima Muhamamd bisa zarginta da laifi...
Rating :
5