Dan wasan kwallon kafa Samuel Eto’o ya shirya wani taro domin taimakawa wadanda suka gudu suka bar gidajensu saboda hare-haren Boko Haram suka kai musu.
Tauraron kungiyar kwallon kafan Antalyspor na kasar Turkiyya Samuel Eto'o ya shirya wani taron manema labaran kasashen duniya domin kira ga mutane da a taimakawa ‘yan kasar Najeriya da Kamaru wadanda suka gudu suka bar gidajesu saboda hare-haren da kungiyar ta’addanci Boko Haram ke kai musu.
A cikin bayanin da dan wasan kwallon kafa na kasar Kamaru Eto’o yayi wa kamfanin watsa labarai na CNN, ya ce ‘yan jarida ba sa magana akan hare-haren da Boko Haram ke kai wa a Najeriya kamar yadda ya kamata.
Samuel Eto'o ya ce, a lokacin da aka kai wa Charlie Hebdo hari a Paris babban birnin kasar Faransa, shugabanin duniya baki daya sun la’anci wannan hari, “shi yasa kamata ne a yi magana game da ‘yan Boko Haram kuma. Domin idan bamu yi magana game da su ba, shi waye zai yi?”
Dan wasa Eto’o ya bayyana cewa ya kafa wani asusun yakan Boko Haram mai suna “Yellow Whistleblower” inda ya zuba kudi dalar Amirka dubu 75 domin taimakawa mutane, ya kuma kara da cewa “Boko Haram sun dami rayuwar ni da sauran ‘yan uwana da dama a Afirka. Shi ya sa lokaci ta yi da zamu kawo karshen wannan damuwa wannan hare-haren da Boko Haram ke kaiwa. Ko da yake sojoji na ci gaba da yakan ‘yan ta’addan amma mu ma zamu iya taimaka musu.”
Title :
Samuel Eto’o ya taimaka da dala 75,000 wurin yakan Boko Haram
Description : Dan wasan kwallon kafa Samuel Eto’o ya shirya wani taro domin taimakawa wadanda suka gudu suka bar gidajensu saboda hare-haren Boko Haram su...
Rating :
5