Kasar Rasha ta bayyana aniyarta na aiki tare da ‘Yan tawayen Syria da kuma Amurka domin farwa mayakan ISIL da hare hare ta sama a Syria.
Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov ne ya bayyana haka tare da yin kiran a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a kasar ta Syria.
Wata majiya a Rasha kuma ta tabbatar da cewa shugaban kasar Syria Bashar al Assad ya amince ya shiga takarar zaben shugaban kasa a sabon zaben da Rasha ta bukaci a gudanar.
Sai dai ana hasashen yana da wahala bangaren adawa a Syria su amince da kudirin Bashar Al Assad na tsayawa takara a sabon zaben.
rfi hausa
Title :
Rasha ta amince ta hada hannu da Amurka domin yakar ISIL
Description : Kasar Rasha ta bayyana aniyarta na aiki tare da ‘Yan tawayen Syria da kuma Amurka domin farwa mayakan ISIL da hare hare ta sama a Syria. Mi...
Rating :
5