Sojin Najeriya sunce sun ceta mutane 338 daga sansanin yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno a Talata 27, ga watan Oktoba. A takada daga jami’i mai hudda da jama’a na sojin Najeriya ta 28 Task Force Brigade, Sani Usman yace, sojojin a Bitta da Pridang sunyi nasara da kai hari wasu sansanin yan ta’addan Boko Haram a kauyukan Bulajilin da Manawashe a hanyan Bita da Damboa a jihar Borno.
Usman yace wani hari ta auku a gafen dajin Sambisa inda yan ta’addan Boko Haram 30 sun rasu a ranar Talata 27, ga watan Oktoba.
Usman yace: “Wani sojin Najeriya sun ceta mutane 338 wadanda yan ta’addan sun kama a sansanin su. Wani masu ceta, akwai maza guda 8, mata guda 138 da yara guda 192. An dauki su zuwa Mubi.”
Yace kuma, sojojin sun karbo makamai da bindigogi. Acikin abubuwa wanda sun karbo, akwai babban bindiga da karamin bindiga da iri-irin makamai.
Ga sauran hotuna a kasa:
source naij Hausa
Title :
[Photos] Sojin Najeriya Sunyi Mamaye Sambisa, Sun Kashe Yan Boko Haram 30
Description : Sojin Najeriya sunce sun ceta mutane 338 daga sansanin yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno a Talata 27, ga watan Oktoba. A takada daga jam...
Rating :
5