Jarumin nan na fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya sake yin aure.
Wani aminin jarumin ya shaida wa BBC cewa ya yi aure ne a asirce, kuma wacce ya aura sunanta Ummu Kulsum a birnin Ngaoudere na Jamhuriyar Kamaru.
Gabanin auren nasa dai, Adam Zango, yana da mata guda biyu.
Sai dai a baya ya saki wasu matan da ya aura, lamarin da ya sa ake yi masa kallon mai auri-saki, ko da ya ke ya sha musanta hakan.
A kwanakin baya, daya daga cikin jarumai mata, Nafisa Abdullahi, ta bayyana matukar son da take yi wa jarumin, tana mai rokon addu'ar Allah ya zaba musu abin da ya fi alheri.
Title :
[Photos] Adam A Zango Ya Kara Aure Aboye
Description : Jarumin nan na fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya sake yin aure. Wani aminin jarumin ya shaida wa BBC cewa ya yi aure ne a asirce, kuma wa...
Rating :
5