Hukumar zaben kasar Cote d'Ivoire ta bayyana Alassane Draman Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar wanda aka gudanar a karshen mako.
Hukumar ta CENI ta bayyana cewa Alassane Ouattara ya lashe zaben da kusan kashi 84 daga cikin dari na yawan kuri'un da aka kada. Ko wanne irin tasiri sake zaben nasa zai yi ga tattalin arzikin kasar dama na Afrika baki daya? An dai haifi Alassane Dramane Ouattara wanda ake yiwa lakabi da ADO a shekara ta 1942 a garin Dimbokro na tsakiyar kasar ta Cote d'Ivoire. Iyayensa Musulmi ne. Ouattara ya yi dogon karatu inda a shekara ta 1972 ya samu digiri a fannin ilimin tattalin arziki a jami'ar Pensilvaniya ta Amirka daga nan ne kuma ya soma aiki da Asusun Ba da Lamuni na Duniya wato IMF.
Fara shiga harkokin mulki
A cikin watan Nuwambar shekara ta 1990 Ouattara ya zamo Firaminista a gwamnatin Shugaba Felix Houphouet-Boigny na tsawon shekaru uku. Duk da wannan matsayi da ya rike, a shekara ta 1995 an haramta wa Alassane Ouattara tsayawa takarar neman shugabancin kasar a bisa hujjar cewa shi ba cikakken dan kasa ba ne kasancewar iyayensa sun fito ne daga Burkina Faso.
Ouattara Ya sake fuskantar wannan kalubale na batun dan kasa a zaben shekara ta 2000 tare da Laurent Gbagbo, batun da Ouattara ya bayyana cewa shi ne ya haddasa yakin basasar da kasar ta fuskanta a shekara ta 2002:
" Wannan batu na dan kasa ne ya jefa Cote d'Ivoire cikin wani yanayi na rikici, abubuwan da suka biyo baya kuma ba abin da hankali zai dauka ba ne, an yi kashe-kashe, kuma duk saboda wannan akida ta kishin kisa. Wanna batu shi ya janyo kafuwar 'yan tawaye a yankin Arewacin kasar, ya kum hambarar da gwamnati. Ya kamata wannan ya zamo mana darasi, mu kawo karshen kin jinin juna da banbance-banbancen da suka kawo wannan rikici."
Jajircewa da rashin karaya
Shekaru bakwai bayan wannan Shugaba Gbagbo ya canza ra'ayinsa kan Ouattara inda ya bayyana halaccin takarar Ouattara a zaben shugaban kasa. A zaben shekara ta 2010, Ouattara ya sha kaye a zagayen farko na zaben shugaban kasar da suka fafata tare da Laurent Gbagbo amma ya yi nasarar lashe zaben a zagaye na biyu.
Sai dai kotun tsarin mulkin kasar wacce ke goyan bayan Gbagbo ta juya sakamakon zaben tare da bayyana Gbagbo a matssayin wanda ya lashe shi. Kasashen duniya a nasu bangaren sun yi fatali da hukuncin kotun tare da bayyana Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben, amma Gbagbo ya yi kememe a kan karagar mulki abin da ya haddasa rikici wanda aka share watannin biyar ana yi a kasar wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 3000, kafin sojojin da ke yin biyayya ga Ouattara masu samun goyan bayan sojojin Fransa su cafke Gbagbo tare da mika mulki ga Ouattara. Bayan tsawon shekaru biyar na mulki Ouattara ya sake lashe sakamakon zaben kasar a wani sabon wa'adi na shekaru biyar a nan gaba, kuma tuni wasu kasashe irinsu Nijar suka fara nuna gamsuwarsu da dai-daituwar al'amurra a kasar ta Cote d'Ivoir wacce ke a mtsayin kashin bayan tattalin arzikin kasashen yankin. Yanzu dai jama'a sun zura ido su ga yadda Shugaba Ouattara da ke da shekaru 72 a duniya zai ci gaba da aikin farfado da tattalin arzikin kasar tasa dama hada kan al'ummar kasar bisa alkibla guda.
Title :
Ouattara ya yi tazarce a Cote d'Ivoire
Description : Hukumar zaben kasar Cote d'Ivoire ta bayyana Alassane Draman Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar wanda aka gudanar a...
Rating :
5