Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya ce zai daukaka kara kan hukunci da wata kotun shari'ar zabuka a Najeriyata ta yi na soke zabensa.
A ranar Asabar ne kotun wacce take zaman sauraron karar a Abuja, ta kuma bayar da umarnin a sake sabon zaben gwamna a jihar nan da kwanaki 90.
Kotun ta kuma yanke wannan hukunci ne sakamakon korafin da dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC Mista Dakuku Peterside, ya shigar na cewa bai yarda da sakamakon zaben ba.
Alokacin da yake ganawa da manema labarai bayan gama sauraron karar, Lauyan da yake kare Mista Wike, Chris Uche ya ce Mista Wike zai ci gaba da kasancewa gwamna har sai an kammala sauraron daukaka karar da za su yi.
Zaben da aka gudanar a jihar ta Rivers a watan Afrilu ya sha suka daga masu sa ido na kasashen waje da na cikin gida saboda tashe-tashen hankulan da aka yi ta samu tsakanin jam'iyyun APC da na PDP a lokacin gudanar da zaben.
Title :
Nyesom Wike Zai Daukaka Kara
Description : Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya ce zai daukaka kara kan hukunci da wata kotun shari'ar zabuka a Najeriyata ta yi na soke zabensa. A...
Rating :
5