Hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya, NCC ta ci kamfanin MTN tarar sama da Naira Tiriliyan daya.
An ci tarar kamfanin ne saboda gazawarsa wajen rufe layukan masu hulda da shi, wadanda ba su yi rijista ba har wa'adin yin rijistar ya wuce.
Wannan shi ne karon farko da aka ci tarar wani kamfanin sadarwa makudan kudade saboda rashin bin umarnin hukumar.
Kamfanin na MTN dai ya yi kaurin-suna wajen rashin biyan bukatun masu hulda da shi.
Bbchausa
Title :
NCC ta ci tarar MTN naira tiriliyan daya
Description : Hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya, NCC ta ci kamfanin MTN tarar sama da Naira Tiriliyan daya. An ci tarar kamfanin ne sa...
Rating :
5