Sakamon nasarar da Najeriya ta samu, inda ta lallasa kasar Australia da ci 6-0 a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shakaru 17 da ake gudanar wa a Chile, yanzu haka kungiyar Golden Eaglet ta Najeriya, za ta kara da Brazil a wasan dab da na kusan karshe a gasar.
Najeriya wadda ta dauki kokfin gasar har sau hudu, na taka rawar gani, yayin da ta yi nasara a wasanni uku cikin hudu da ta buga.
Ita ma dai Brazil ta samu nasara a wasanni uku cikin hudu da ta buga, kuma za ta kara da Najeriya ne sakamakon doke New Zealand da ta yi da ci daya mai ban haushi.
Title :
Najeriya za ta kara da Brazil a gasar cin kofin duniya
Description : Sakamon nasarar da Najeriya ta samu, inda ta lallasa kasar Australia da ci 6-0 a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shakaru 17 da...
Rating :
5