Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta ce mutane
bakwai ne ke tarakar kujerar shugabancinta.
'Yan takarar su ne: shugaban hukumar kwallon nahiyar
Asiya, Sheikh Salman bin Ebrahim al-Khalifa da Yarima Ali
bin al-Hussein na Jordan da kuma shugaban hukumar
kwallon Liberia Musa Bility.
Sauran su ne Jerome Champagne da Gianni Infantino da
shugaban Uefa da aka dakatar Michel Platini, da kuma
dan kasar Afrika ta Kudu Tokyo Sexwale.
Shugaban Fifa na yanzu, Sepp Blatter an dakatar da shi
na tsawon kwanaki 90 bisa zargin cin hanci da rashawa.
Shi ma Platini an dakatar da shi amma kuma Fifa ta ce za
a barshi ya yi takara idan har wa'adin dakatarwar ta kare.
Blatter da Platini sun musanta zargin cin hanci da
rashawa da ake musu.
Title :
Mutane bakwai na takarar shugabancin Fifa
Description : Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta ce mutane bakwai ne ke tarakar kujerar shugabancinta. 'Yan takarar su ne: shugaban hukumar kwa...
Rating :
5