Shugaba Muhamadu Buhari ya ce idan har ana so a ga sauyin da ake hankoro ya tabbata, to dole ne 'yan Najeriya su sauya yadda suke su zama 'yan kasa masu kiyaye doka.
A jawabin sa da ya yiwa 'yan Najeriya a ranar alhamis a wani bangare na bikin cikar Najeriya shekaru 55,ya yi kira ga 'yan Najeriya da su bashi hadin kai domin gina kyakyar kasa.
Shugaba Buhari ya yi bayani a kan dalilan da suka sa bai tura sunayen mutanen da yake son ya nada a matsayin ministoci ga Majalisar datawan Najeriya da wuri ba.
Shugaba Buhari ya dai dora alhaki jinkirin da aka samu wajen samun sunayen ministocin ne kan yanayin yadda tsohuwar gwamnati ta Goodluck Jonathan ta mika musu harkokin mulki.
Ya kuma kara da cewa har yanzu bai gama mika sunayen wadanda ya ke son ya nada a matsayin ministoci gabadaya ga majalisar dokoki ta tarayya ba amma ya ce zai kamala yin haka nan gaba.
Game da tarin matsalolin da gwamnatinsa ta gada kuwa shugaba Buhari ya ce sun ga yadda aka yi tabargaza da almubazzaranci da tarin dukiyar kasa a 'yan shekarun da suka gabata kuma gwamnatinsa ta APC tana kokarin bulo da tsare tsare na magance irin illolin da wannan tabargaza ta haifar.
A cewar sa a matakin farko gwamtin tarayya ta shawo kan matsalar tarin albashi ma'aikata da ke kan wasu jihohi wanda ba don haka ba da lamarin zai iya tayar da hatsaniya.
Sai dai shugaba Buhari ya kara da cewar, ba haka kawai canji ya ke samuwa ba, ya ce "da kai da ni da kowa da kowa na da rawar da zai taka domin tabbatar da sauyin da muke fatan gani."
Shugaba Buhari ya ce indai har muna so mu ga sauyin da muke hankoro ya tabbata, to dole ne mu sauya yadda mukanmu muke mu zama 'yan kasa masu kiyaye doka.
Title :
Mu hada hannu mu gina kasar mu- Buhari
Description : Shugaba Muhamadu Buhari ya ce idan har ana so a ga sauyin da ake hankoro ya tabbata, to dole ne 'yan Najeriya su sauya yadda suke su zam...
Rating :
5