Yayin da gwamnatin Najeriya ke cigaba da nade-
naden jami'anta, matasa na kokawa kan rashin
sasu cikin gwamnati
Kakakin Majalisar Matasan
Najeriya Honorabul Abba Waziri y ace matasa ba
su ji dadin rashin damawa da su a gwamnatin
Shugaba Muhammadu Buhari ba. Ya ce bai
kamata gwamnati ta fara da kin tafiya da matasa
ba, ganin rawar da matasa ke takawa da kuma
wadda su ka taka a zabukan da su ka gabata cikin
nasara.
Da yak e magana da wakilinmu a Abuja Hassan
Maina Kaina, Kakakin na matasa y ace akwai
matasan da su ka goge a fannoni daban-daban ta
yadda kowane irin matsayi ka bai wa matasan
Najeriya ba za su kasa ba.
Ita ma wata ‘yar rajin kare hakkokin matasa a
Najeriya mai suna Fatima Maina Abdullahi ta ce
matasa sun dauka cewa Buhari zai bai wa matasa
kaso a gwamnatinsa sai gashi an barsu a tutar
babu. Don haka Fatima ta ce yakamata a yi
kwaskwarima ma sunayen da aka gabatar don a
bai wa matasa wasu mukamai.
To amma Honorabul Mai Mala Boni, Sakataren
jam’iyyar APC mai mulkikn Najeriya y ace akwai
matasa isassu a gwamnatin Buhari ciki har da
Ministocin da aka gabatar daga jahohin Kebbi,
Borno, Yobe Kaduna da sauran mukamai.
Title :
Matasa Sun Koka Da Rashin Tafiya Da
Su A Gwamnatin Buhari
Description : Yayin da gwamnatin Najeriya ke cigaba da nade- naden jami'anta, matasa na kokawa kan rashin sasu cikin gwamnati Kakakin Majalisar Mat...
Rating :
5