Biyo bayan hare-haren kunar bakin wake da ake
kaiwa masallatai da wuraren ibada limaman
masallatan Adamawa da jami'an tsaro sun hada
kai domin inganta matakan tsaro
Daga watan Yuli zuwa yanzu
an samu hare-haren kunar bakin wake 22 a jihar
Borno wadanda suka yi sanadiyar mutane 292. A
jihar Adamawa kuma an samu hare-hare hudu da
suma suka lakume mutane da dama.
Hukumomin tsaron jihar Adamawa sun gana da
shugabannin masallatai da mijami'u domin
cimma matsaya akan tunkarar ta'adanci.
Malam Yusuf Usama na kungiyar agaji ta IZALA
yace dole zasu dauki matakai a masallatai kana ya
kira jama'a da su bada hadin kai domin a shawo
kan ta'adanci. Yace daya cikin matakan da zasi
dauka shi ne fitowar 'yan agaji da wuri har ma
idan ta kama suna iya kwana a masallatan.
Ya kira jama'a da su daina taruwa a tsaye suna
surutu maimakon su samu wuri su zauna su
saurari hudubar limami.
Shi ma limamin sabon masallacin Juma'a da aka
kaiwa harin kunar bakin waken ya roki jama'a
kada a karaya amma a jajirce a hada kai da
jami'an tsaro. Yace duka masallatai za'a kara
matakan tsaro saboda kawar da bala'in ta'adanci.
Ya kira jama'a su jajirce su bautawa Mahalicinsu.
Idan lokacin mutuwa ya yi Alla na iya karban ran
mutum koina yake.
Title :
Masallatai Sun Karfafa Matakan Tsaro
a Adamawa
Description : Biyo bayan hare-haren kunar bakin wake da ake kaiwa masallatai da wuraren ibada limaman masallatan Adamawa da jami'an tsaro sun hada ...
Rating :
5