Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 30 suka samu raunuka, bayan da wata roka ta fado akan gungun mutane masu zanga-zanga a birnin Benghazi da ke gabashin Libya a wannan juma’a.
Mutanen dai na gudanar da tarzoma ne domin nuna adawa da tattaunawar samar da zaman lafiya a kasar wadda MDD ke jagoranta.
Daruruwan mutane ne suka taru a tsakiyar birnin na Benghazi da ke gabashin Libya inda suke nuna adawa da yadda aka tsara raba mukamai a tsakanin kungiyoyin ‘yan tawaye na kasar kamar dai yadda MDD ta bukaci a yi domin samar da zaman lafiya a kasar.
Majiyoyin kiwon lafiya sun tabbatar da mutuwar mutanen biyar, yayin da suka ce wasu akalla 30 sun samu raunuka, yayin da jami’ai a wani asibi mai zaman kansa da ke birnin ke cewa an shigar da wasu gawarwaki da dama a asibitin.
Kawo yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, to sai dai akwai bangarori da dama na ‘yan tawaye da ke hamayya da juna a birnin na Benghazi.
Title :
Makami mai linzame ya kashe mutane 5 a Benghazi
Description : Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 30 suka samu raunuka, bayan da wata roka ta fado akan gungun mutane masu zanga-zang...
Rating :
5