TAMBAYA TA 1755
********************
Don girman Allah a taimaka a amsa man tambayata. Allah yaima sakayya da gidan Aljanna mlm. na kasance daya daga cikin daliban wannan zauren kuma ina bibiyar fatawoyinka. mlm ina fama da matsalar sanyi (gonorrhoea), wato wani farin ruwa ke fitowa daga azzakarina shine nake so mlm ya taimaka man da magani don naji ance wannan matsalar na hana mutum haihuwa kuma gashi saura wata ukku bikina, sannan kuma ina gudun kar in gogama matar da xan aura. na jarraba wani daga cikin magugunan da kai bayani ga irin wannan mtslar a baya na garin tafarnuwa, citta da kustilhindi a cikin zuma duk inna sha sai zuciyata ta rika yin ciwo. kuma na jarraba wanda ka bada ga tambaya ta 1458 shima ban dace ba. mlm a taimaka a amsa man don na dade ina fama da wannan matsalar kuma abin na damuna. mlm a boye sunana. na gode.
AMSA
*******
Shi wannan sanyin gaskiya yana da wahalar jin magani. Domin kuwa wadancan abubuwan da ka ambata a baya, mutane da yawa sun jarraba kuma sun samu waraka da yardar Allah.
Amma ga wasu nan ga jarraba:
1. Ka nemi Man Habbatus sauda dan Misra ko Algeria ko Hemani. Ka gaurayashi da man Tafarnuwa Original tare da Man Albabunaj. Sannan ka rika dafa 'danyar chitta (Ginger) da ruwa kofi guda. idan ya dafu sai ka sanya wancan Man chokali guda aciki, sannan ka sanya zuma daidai gwargwado, sannan kasha.
In dai sanyi ne, kowanne iri ne in sha Allahu zaka samu waraka.
Ka samu Furen Albabunaj (chamomile flower) ka rika dafa cokali guda kana sha kullum da safe. In sha Allah Wannan zai wanke maka Qodarka da mafitsararka, Kuma zai magance maka Matsalolin ciwon sanyi.
WALLAHU A'ALAM.