Ibnu Aqeel ya fada acikin Littafinsa mai suna ALFUNOON cewa a Unguwar Zufriyyah agarin Baghdad akwai wani gida wanda duk lokacin da aka sauki wasu mutane acikinsa sai an wayi gari agansu gaba dayansu sun mutu!!
Rannan sai wani mutum Mahaddacin Alqur'ani yazo ya karbi hayar gidan. (Bayan an gaya masa yanayin gidan amma bai damu ba, ya karba duk da haka). Sai muka ga ya shiga gidan lafiya kalau, kuma har wayewar gari babu abinda ya sameshi.
Yaci gaba da Zamansa har zuwa wasu kwanaku masu yawa, sai ranar da zai tafi muka tambayeshi shin babu wani abinda ya faru ne?
Sai yace mana : "Ranar da na fara kwana agidan nan, nayi sallar Isha'i sannan na zauna na karanta wani abu daga cikin Alqur'ani.
Ina cikin karatun sai naga wani Yaro saurayi ya fito daga cikin rijiyar gidan. Yazo yayi mun sallama, na amsa masa cikin tsoro. Sai yace mun "Ba zanyi maka komai ba. Amma ina so ka koyar dani karatun Alqur'ani".
Don haka na fara koya masa sannan na tambayeshi Shi. labarin da ake fada game da gidan nan gaskiya ne? Sai yace "Mu Musulman Aljanu ne. Muna sallah, muna karatun Alqur'ani. Amma duk lokacin da za'a sauki mutane agidan nan sai mu gansu duk fasikai ne. Zasu hadu suna kade-kade suna Shan giya. Don haka sai mu taso cikin dare mu Shakesu har sai sun mutu".
Sai nace masa "To ni dai ina jin tsoron zuwanka cikin dare. Don haka ka rika zuwa da rana". Daga nan sai kullum yake haurowa daga cikin rijiyar nan, ni kuma ina karantar dashi".
Wannan labarin yana nan acikin littafin AAKAMUL MARJAAN (babi na 47).
Tabbas ko anan Nigeria akwai gidajen da irin hakan take faruwa ta sandiyyar Makobtaka da Aljanu. Wani lokacin kuma gobara tana afkuwa.
Don haka ya kamata duk wanda yayi sabon gida ya tabbatar an karanta Alqur'ani da zikirin Allah da sauran addu'o'in neman tsari kafin ya tare agidan.
An sha kawo mana marassa lafiya wadanda ta sanadiyyar tarewa a sabobbin gidaje suka tarar ds matsalar.
Ya Allah ka kiyayemu, ka tsare mana dukkan iyalanmu da 'yan uwa musulmai baki daya.
ZAUREN FIQHU WHATSAPP.
Title :
Labarin Wani Aljanni Musulmi
Description : Ibnu Aqeel ya fada acikin Littafinsa mai suna ALFUNOON cewa a Unguwar Zufriyyah agarin Baghdad akwai wani gida wanda duk lokacin da aka sauk...
Rating :
5