Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, watau Custom ta
yi wa manyan jami'anta 34 ritaya daga aiki.
Hukumar, wacce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta
fitar, ta ce ta dauki matakin ne domin yin sauye-sauye a
cikinta, kamar yadda sabon shugabanta, Kanar Hameed
Ali (mai Ritaya), ya sha alwashin yi.
Sai dai gabanin sallamar manyan jami'an nata, biyar daga
cikin su sun mika takardunsu na yin murabus daga kan
mukamansu.
Mutanen su ne: John Atte, Ibrahim Mera, Musa Tahir,
Austin Nwosu da Akinade Adewuyi.
Yawancin jami'an da suka yi murabus suna da mukaman
mataimakan shugaban hukumar.
Hukumar ta yi kaurin-suna wajen karbar hanci da
rashawa.
Bayanai sun ce gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin
jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta sha alwashin
kawar da cuwa-cuwa a hukumar kwastam ta kasar.
Title :
Kwastam ta yi wa jami'anta 34 ritaya
Description : Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, watau Custom ta yi wa manyan jami'anta 34 ritaya daga aiki. Hukumar, wacce ta bayyana hakan a wa...
Rating :
5