Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce Jose Mourinho zai
iya zama mutumin kirki, tunda shi ba alkalin wasa ko
dan jarida ba ne.
Kungiyoyi biyu za su hadu a ranar Asabar, a yayin da
Klopp ya ke neman samun nasara a gasar Premier.
An tuhumi Kocin Chelsea, Mourinho har sau biyu a kakar
gasar bana saboda kalubalantar alkalan wasa da kuma
nuna rashin da a, sai dai kuma Klopp ya ce a zahiri ba
halayyar Mourinho ba ne rashin da'a.
"Ina girmama ayyukan sa. Ina ga idan kai ba dan jarida
ko alkalin wasa bane, Mourinho mutumin kirki ne," in ji
Klopp.
Ya kara da cewa "Ni ba daya daga cikin wadanda na
lissafa ba ne, saboda haka mun tattauna da shi sosai shi
ya sa na gano haka".
Title :
Klopp ya ce Mourinho mutumin 'kirki ne'
Description : Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce Jose Mourinho zai iya zama mutumin kirki, tunda shi ba alkalin wasa ko dan jarida ba ne. Kungiyoyi bi...
Rating :
5