An horar da kimanin mutane 128, dubarun mu’amala da zamantakewa a cikin al’umma a harabar Rundunar Bataliyar Soja da ke Maiduguri.
Mutanen dai, wadanda kimanin wata guda ke nan da Rundunar Soja Bataliya ta 7 da ke garin Maiduguri ta saki daga gidajen yari, bayan wanke su daga zargin kasancewa ’ya’yan kungiyar Boko Haram, sun samu horon ne na tsawon kwanaki biyar.
Laftanar Kanar Sulaiman Bawa Salisu, shi ne limamin da ya jagoranci koyar da mutanen al’amuran da suka shafi zamantakewa da mu’amala da jama’a yadda ya kamata da nufin canja dabi’unsu da rage musu akidar zafafa al’amuran addini, musamman yadda za su iya gudanar da rayuwarsu cikin zaman lumana da sauran al’umma tare da dogaro da kansu.
Malamin ya ce: “Mun yi masu bayani a kan yadda addinin Musulunci yake da kuma yadda addinin ya tsara yadda ake mu’amala da wadanda ba Musulmi ba, domin akwai rashin fahimta da dama, wadda kuma ita ce ta sabbaba wadannan fitintinun da muka tsinci kanmu a ciki a halin yanzu. To, wannan ya sanya Rundunar Soja ta ga ya kamata ta kara masu haske, ta kuma jawo hankalinsu. Kuma alhamdu lillahi, mun yi gwargwadon kokarinmu, mun fadakar da su yadda zamantakewa take a Musulunce da kuma kyautata dabi’a da zamantakewa da wadanda ba Musulmi ba, da kuma saukin fahimta da saukin zama da jama’a wadanda ba akidarku daya ba ko kuma ba addininku daya ba. Sun kuma nuna gamsuwa tare da fahimtar abin da muke nufi. saboda haka wannan shi ne abin da muka sa a gaba.”
Malam Musa Ali, daya daga cikin wadanda suka amfana da wannan horo, ya bayyana cewa: “A gaskiya na karu da ilimi mai yawa, domin an koya mana yadda addinin Musulunci yake koyar da mu zamantakewa da mutane, har da ma wadanda ba Musulmi ba. Mun kuma fahimci hanyoyin da addini ya shimfida na yadda za a samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Mun kuma fahimci abin da ake nufi na gyara dabi’u da halayenmu. Ko da ko mutum dan kasuwane ko ma’aikacin gwamnati, akwai yadda za ka bayar da gudunmuwarka ga ci gaban addini da kuma zamantakewa a tsakanin al’umma. To, mun karu kwarai da gaske kuma in Allah Ya yarda za mu yi amfani da abin da muka koya.”
Ita ma Fatima Usman, tana daya daga cikin wadanda suka amfana da horarwar, ta kuma ce: “A gaskiya mun karu da ilimin zamantakewa da kuma yadda dabi’u da halayenmu za su kasance bayan mun fita. Kodayake dai ni ba ’yar Boko Haram ba ce amma na gamu da matsalar Boko Haram din ne, yadda suka kama ni har suka kai ni wajensu a dajin Sanbisa har na tsawon shekara daya; inda na zama matarsu ta wucin-gadi, bayan sun ba ni sadaki har na Naira dubu biyu, na kuma yi masu wasu aikace-aikace, kafin Allah Ya ba ni sa’a na tsere daga wajensu. To kuma na gudu ke nan sai na fada hannun sojoji, suka kuma kai ni barikinsu, suka hadani da wadannan mutane; tunaninsu cewa ni matar ’yan Boko Haram ce.”
Title :
Halin da na samu kaina tare da ’yan Boko Haram a Sambisa
Description : An horar da kimanin mutane 128, dubarun mu’amala da zamantakewa a cikin al’umma a harabar Rundunar Bataliyar Soja da ke Maiduguri. Mutanen ...
Rating :
5