Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC mai
mulkin Najeriya sun yi kira ga Shugaba Muhammadu
Buhari ya cire tallafin man fetur.
Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, wanda ya
bayyana wa BBC hakan a madadin takwarorinsa, ya ce
tattalin arzikin Najeriya na ci gaba da tabarbarwa, yana
mai cewa cire tallafin zai ba su damar bunkasa sauran
kafofin ci gaban tattalin arziki irin su noma da
masana'antu.
Ya ce, "Ya kamata a cire tallafin mai domin ban ga
amfaninsa ba. Mai yiwuwa idan aka cire tallafin farashin
man fetur ya sake faduwa. Idan ba a cire ba, mutanen da
ake bai wa tallafin za su ci gaba da kwashe kudin
Najeriya".
A makon jiya ne Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya
bukaci gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur baki
daya, sannan kuma ta sake duba batun rage darajar
kudin kasar watau Naira.
Amma tuni aka ambato wani babban jami'i a babban
bankin Najeriya yana mayar da martani ga matsayin
Sarkin Kano, yana mai cewa ba za su rage darajar Naira
ba.
Su ma gwamnonin sun ce ba su ga amfani rage darajar
Naira ba.
A watan jiya a lokacin wata ziyara a Faransa, an ambato
shugaba Muhammadu Buhari yana cewa ba ya goyon
bayan rage darajar Naira.
Title :
Gwamnonin APC na so a cire tallafin man fetur
Description : Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya cire tallafin man fetur...
Rating :
5