Fitaccen lauyan nan, Femi Falana yayi sha alwashin kai Shugaba Muhammadu Buhari kotu. Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Falana yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba muduwar wasu mutane wanda ake zargin cewa masu kiwon shanu ne suka kashe su. Falana ya bayyana cewa dole gwamnati tayi wani abu akan haka.
Falana yace: “Manoma kamar sauran yan kasa, ya zama dole gwamnati ta kula da hakkin su. Yawon da masu kiwon shanu sukeyi daga Arewa zuwa kudu, ya zama dole a dakata da shi ba tare da wani bata lokaci ba.
“Kamataye gwamnati ta sayi filaye domin ta maida su wajen kiwon dabbobi. Ya zama dole kuma a sanya matasan tsaro domin hana aukuwar fitina.”
Title :
Falana Zaya Kai Buhari Kotu
Description : Fitaccen lauyan nan, Femi Falana yayi sha alwashin kai Shugaba Muhammadu Buhari kotu. Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Falana yayi kira ga...
Rating :
5