Aikin daukar fim din nan na barkwanci 'Malam Zalimu sabon yanka' ya yi nisa a Kano.
Marigayi Rabilu Musa wanda aka fi sani da Ibro shi ya fito a matsayin takadarin Malami Zalimu, Limamin wani gari.
A sakamakon rasuwar shararren dan wasan ne da kuma bukatar ci gaba da fim din yanzu, Suleman Yahaya, wanda aka fi sani da Bosho ya canji Ibro a matsayin kanen Zalimu.
A ci gaban labarin fim din dai Bosho kanen marigayi Liman ya samu labarin mutuwar dan uwansa ya kuma dawo garin ya rike gadon gidansu na Limanci, lamarin da ya samu tirjiya daga Liman mai ci Abba Al Mustapha.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Ahmad Ado Gidan Dabino MON a hirarsa da BBC.
Malam Zalimu littafi ne da Ado ya rubuta kuma littafin ya ci gasar adabi ta tunawa da Injiniya Bashir a shekara ta 2009.
Bosho gwanin wasan barkwanci ya fito fina finai da yawa ciki har da 'Sarki Jatau' da 'Hanyar Kano' da sauransu.
Abba Al Mutapha ya yi fice fina finan Kanywood a in da ya ke fitowa a matsayin kasurgumin attajiri amma a wannan karon ya fito a matsayin limanin kauye.
Title :
Bosho ya gaji Ibro a fim din "Zalimu"
Description : Aikin daukar fim din nan na barkwanci 'Malam Zalimu sabon yanka' ya yi nisa a Kano. Marigayi Rabilu Musa wanda aka fi sani da Ibro ...
Rating :
5